Connect with us

SIYASA

Matan Nijeriya Sun Samu Kulawar Gwamnatin Shugaba Buhari –Hajiya Hannatu Akilu

Published

on

Mataimakin Edititanmu Bello Hamza ya yi tattaki zuwa babban hedikwatar kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, ‘Buhari Sopport Organization’ dake yankin Utako a babban birnin tarayya kasar nan Abuja, don jin yadda suke gudanar da ayyukansu da kuma irin hujjojin da suke tallatawa wa al’ummar Nijeriya na nasarorin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta damu da ya kamata ‘yan Nijeriya su sake zabar ta a karo na biyu, Hajiya Hannatu Akilu ita ce Darakta Kula da Gudanarwar Kungiyar da kuma kula da yadda kungiyar ke kashe kudadenta, ta kuma samu tattaunawa da Editanmu a kan haka, ga dai yadda hirar ta mu ta kasance.Za mu so ki bayyana mana sunnanki
Sunana Hannatu Akilu nice Daraktar gudanarwa da kula da kudaden kungiyar ‘Buhari Support Organization’
Menene anihin aikin wannan kungiya taku?
Aikinmu shi ne na ganin mun tabbatar da shi Shugaban Muhammadu Buhari ya sake dawowa a matsayin shugaban kasa a karo na biyu, a wannan tafiyar, mu muka yi tsaye tare da jam’iyyar APC muke kokarin mu tattabar da ya dawo a wannan karon saboda a tabbatar a abubuwan da y a kaddamar na ci gaban kasa da kuma suka shafi yaruwar dukkan ‘yan Nijeriya, muna fatan wannna ya kafu a zuciyar ‘yan Nijeriya don a samu bukasar kasar nan gaba daya.
Ya yanayin karbbuwar wannan tafiya ta ku a wajen jama’a?
To lallai an ce gani ya kori ji, kamar misali fitowar da wata ‘yar takara ta yi, tafito gashi mutane na dauke da hotonta an tafi rali din ta amma mutane nacewa sai Baba sai Baba , su jama’a wadanda masu kada’a kuri’a sune babbar ginshikin wannan tafiya ta Muhammadu Buhari, baa bin day a dame su, su dai tunda sun tabhatarda gaskiya shugaba Buhari, ko mai ka zo musu das hi Buhari suka sani, su kuma wadanan takalawan sune mafiya a cikin al’umma, in kuma ka duba masu kudi su kaso nawa ne a cikin al’umma? sai kuma karbar Baba shi ne mutane suna da aminci da shi kuma suna kallo ne shiya fitone ya tsaya masu bawai shi yana tsaya wa masu kudi bane bai damu ba, kuma shi ba mutum bane wanda ya damu da kudi ko wani abin duniya, kuma ba mutum ne dogon buri bane , toh kuma ma in ka duba shekarusa sabain da wani abu ,toh me zai tara yanzu da zai yi masa tasiri wanda ba shi da shi, shi babban abin dake sa gabansaa shi ne kawai yadda yaruwar jama’a zai inganta, hakan kuma ya say a yi matukar karbua a tsakin jama’a Nijeriya daga dukkan bangarorin kasar nan, don haka kuma muke fadakar da jama’ar a kan bukatar su fito tare da tabbatar da sun kada masa kuri’a a zaben dake tafe na 2019.
Wani kira za ki yi wa ‘yan siyasa musamman ganin yadda ra’ayin talawan Nijeriya ya koma a kan shugaba Buhari?
Shawarar da zan ba ‘yan siyasa shi ne mu ilmantu mude na siyasar zamanin jahiliya mu fito murin ga siyasa na tsafta na na akida bawai kawai mutum ya fito ya yi ta hayaniya akawo yara matasa ana basu kwayoyi ana basu kudi suna zuwa suna kashe mutane ana bata al’umma wannan ba shi ne siyasa ba siyasa shi ku fito kuyi magana kan akida, ka tallata akidar ka, me ka tsaya wa in jama’a sun ga akidarka ta yi musu daidai su fito su bika in kuma bata yi musu ba sai su fito su bi wani wanda suka natsu da shi. Ya kamata mu fahimci cewa, siyasa maganar ra’ayi ne ba yaki bane mu daina mai da siyasa yaki kuma adaina zagezagen juna a cikin siyasa saboda siyasa dattijai ne ke shiga siyasa ba ‘yan iska kuma ba wadanda basu san abinda akeyi ba mudaina irin wannan siyasa da ake zagezage ana bata wa mutane suna wannan ba shi ne siyasa ba
Ranki ya dade wani irin kalubale kika fuskanta a dangane da harkan siyasa ganin cewa siyasa wani gwagwarmaya ne da maza suka yi wa katutu?
To ni dai a gaskiya bana ganin siyasa a matsayin gwagwarmaya na maza kadai ina kallon siyasa a matsayin harka ne da ya shafi kowa da kowa, yana cikin siyasa idan ka duba ko daga cikin gida ana siyasa da kai da yaran da ka haifa kana siyasa in kana son wani abu ya faru dole sai kayi amfani da siyasa saboda haka ni ban dauki siyasa ta maza ko ta mata su kadai ba, kuma wani abin sha’awa da ke tattare da gwambatin Shugaban Mugammadu Buhari shi ne ya ba mata cikakken mahimnaci a ta fiyar da gwamtanisa, in sa lura da yadda a ba mata mukamai daban daban a wannan tafiyar, lallai zaka fahincu haka.
To wani kira zaki yi ga mata wajen ganin suma sun fito an dama da su?
Abin da nake kira ga mata shi ne su daina kallon cewa siyasa ta maza ne su kadai, su dinga kallon cewa rayuwarsu tana ciki ne idan baki fita ba kika tsaya, to ya kike so a kare hakkinki, ba wanda ya san ciwonki kamar ke da kanki saboda haka mu mata idan bamu fito ba baza a kare hakkin mu ba haka nan zamu ga ana tafiya ta ilimin maza ba ta ilimin mace ba kamar yadda ake cewa wa rayuwa madubi ne abin da yake gaban madubin shi zaka gani saboda haka shi namiji in zai yi, zai yi ne ta fuskan daya karanta da ta shafeshi, to amma mu mata in muka shigo zamu tsaya muga mun dage a kan namu fuskan bai zama yaki ba, ni ban dauki siyasa matsayi ne wanda za’a yi yaki tsakanin maza da mata ba, Magana ne na kowa ya fito ya kare nasa hakkin, mace da namiji abinda ake ce ma dan adam ne (human being) saboda haka in kazo kare hakki yadda zaka kare hakkin namiji haka zaka kare hakkin mace dukkanmu ‘yan adam ne bai zama fada ba kuma ina kallon cewa mata kada mu fito muna siyasa saboda ace wai mace tafi namiji kotayaya bayadda zamu yi mu zama daya kowa da gurbin shi bai kamata ba ace kowa yana so ya dauki gurbin kowa a rayuwar nan kowa rabonsa zai ci .
Ranki ya dade mun gode.
Ni ma na gode
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!