Connect with us

LABARAI

Mutum 15 Sun Rasu A Iran Bayan Jirgin Soji Ya Tarwatse

Published

on

Wani babban jirgin sama na Sojoji a kasar Iran, ya tarwatse a sama bayan ya hadu da tangardar yanayi a yammacin birnin kasar Iran din. Rahotannin sun bayyana cewa; akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu cikin mutane 16 da suke cikin jirgin.

Sojojin kasar sun bayyana cewa; wani matukin jirgin wanda ya tsira a wannan hatsari yana nan asibiti ana ceto rayuwarsa. Jirgin ya fado ne a daidai filin jirgin Fath dake kusa da Karaj kusa a daidai lardin Alborz.

Jirgin mai lamba 707 yana dauke da nama ne daga Bishkek dake cikin garin Kyrgyzstan, inda ya samu tangarda a dai filin jirgin Fath a yau Litinin. A halin yanzu matukin jirgin tuni aka kai shi asibiti.

Sojojin sun kara da cewa; “A yayin sauka ne, jirgin ya yi karo, nan take ya kama da wuta.” Wannan sanarwar ta biyo baya ne bayan ana tunanin ko wane ne mai jirgin.

Sai dai duk a yau Litinin, mai magana da yawun hukumar tasoshin jirgin ya fadawa gidan Talabijin na kasar cewa jirgin mallakin Kyrgyzstan.

Hakazalika mai magana da yawun filin jirgin Kyrgyzstan’s Manas ya bayyana jirgin mallakin Iran Payam Air ne.

Gidan Talabijin na kasar ya ce; an tura jami’an tallafi wurin da abin ya faru, a tsakanin filin jirgin Fath da kuma Payam.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!