Connect with us

LABARAI

Osinbajo Ya Jinjinawa Sojojin Da Suka Sadaukar Da Rayuwarsu Don Kare Kasarnan

Published

on

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a jiya Lahadi, ya jinjinawa sojojin Nijeriya, musamman wadanda suka rasa rayukansu wajen ganin sun kare kasarnan daga matsalolin rashin tsaro.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a Cocin interdenominational  a lokacin da ake taron addu’a a matsayin daya daga cikin tarukan da aka shirya domin tunawa da Sojojin a wannan shekarar a birnin tarayya Abuja.

Ya ce; abin godiya ne ga Allah da ya baiwa Nijeriya maza da mata wadanda suke a shirye su amsa kira a lokacin da ake bukata wajen kare kasarsu.

Ya ci gaba da cewa; “Muna godewa Allah da ya zama suna da imani akan abin da suke yi. Ba su yaudare miliyoyin al’ummaba, sun sadaukar da dukkanin jindadinsu da rayuwarsu da soyayyar da suke yiwa iyalansu, domin mu samu wannan jindadin.”

Har wala yau, Osinbajo ya mika godiyarsa ga mamatan Sojojin, da kuma Iyalansu wadanda suka jurewa kasancewarsu a fagen yaki da ma rasa su da suka yi ta hanyar samun labaran mutuwarsu.

Osinbajo ya ce; tunawa da wannan Sojojin a wannan shekarar ya zama na musamman ganin abubuwan da suka faru a kwanakin nan a yakin da ake yi a Borno, wanda Sojojin suka rasa dimbin rayukan jami’anta. Ya ce; a makonnin da suka gabata, Sojojin sun bizne gawarwakin Sojoji 13, da kuma Sojojin matukan jiragen Sojojin sama 5, wadanda dukkaninsu sun rasa rayuwarsu a yakin da Sojojin ke yi da Boko Haram da ISIS bangaren Afrika ta Arewa.

Ya ci gaba da cewa; a makonnin da suka gabata, an ga jajircewa da kishin kasa a wurin maza da mata na Sojojin nan, wadanda suka tarwatsa mafakan ‘yan Boko Haram.

Osinbajo ya nemi hadin kan ‘yan Nijeriya, domin a cewarsa da hadin kai da wanzuwar zaman lafiya ne shi ne mafi girman abin da zamu iya girmama Sojojinmu da shi. Ya ce; sauran ‘yan Nijeriya suna ci gaba da nuna hadin kai da nuna damuwarsu dangane da abin da yake faruwa.

 Babban Mai jawabi a taron, Kadinal John Onaiyekan ya ce; 15 ga watan Janairu zata ci gaba da kasancewa ranar da ‘yan Nijeriya za su rika tuna cewa; abu mai kyau ya kamata ya kare da kyau. Ya ce; ya kamata ‘yan Nijeriya su kasance masu rungumar zaman lafiya, domin da dorewar zaman lafiya ne kawai za a samu ci gaba. Ya shawarci mutane da su guji neman mulki da karfin tsiya, domin a cewarsa duk wanda ya samu mulki da karfin tsiya, ba zai yi nasara a cikin mulkinsa.

Shugaban Majalisa, Yakubu Dogara, Sakataren Gwamnati, Boss Mustapha, Babban Joji na kasa, Walter Onnoghen da kuma Babban Hafsan Tsaron kasa, Janaral Gabriel Olonisakin da dai sauran su duk suna daga cikin mutanen da suka halarci wannan taron addu’a. 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!