Connect with us

LABARAI

Tirela Dauke Da Shinkafar Kamfen Ta Kashe Mutum 45 A Ekiti

Published

on

Jama’ar garin Iworoko ta jihar Ekiti sun tashi a cikin hankali a ranar Asabar yayin da tirelar kamfanin Dangote dauke da shinkafa ta mukushe mutum 45.
Ya zuwa yanzu ba a bayar da cikakken yawan mutanen da suka mutu ba sakamakon hatsarin a hukumance, amma shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, akalla mutum 45 ne suka rasa rayukansu a hatsarin.
Shinkafar da tilelar ke dauke da shi na manne ne da hoton Mista Tayo Alasoadura dan takarar kujerar Sanata a jihar Ondo.
A halin yanzu Mista Alasoadura Sanata ne mai wakiltar mazabar Ondo ta tsakiya a majalisar dattija, yana kuma neman sake komawa majalisar ne a wannan zaben dake tafe a karo na biyu a 2019. An shirya gudanar da yakin neman zabe ne da buhunan shinkafar, a inda ake raba wa magoya bayan dan takara da kuma wadanda ake fatan su jefa wa mai takarar kuri’a.
Wanda aka yi hatarin a gabansa ya bayyana wa manema labarai cewa, cikin mutum 45 da suka mutu a kwai ‘yan makaranta, inda tirelar ta markada wata mota dauke da mutane daga nan kuma ta zarce cikin kasuwar, ana kuma zaton birkin motar ne ya lalace.
Haka kuma har zuwa yanzu bamu iya tantance yawan daliban da suka mutu ba a cikin hatsarin don kuwa jami’in watsa labarai na jami’ar, Ajibade Olubunmi, bai dauki wayar da aka yi masa don jin ta bakinsa ba har zuwa hada wannnan rahoton.
Bayani ya kuma nuna cewa, da yawa daga cikin daliban sun koma gidajensu sakamakon yajin aikin da kungiyar ASUU ke gudanarwa a halin yanzu.
Wani kuma wanda aka yi hatsarin a gabansa, mai suna Segun Ajayi, ya bayyana cewa, motar dauka marasa lafiya ta yi sawu da dama wajen daukar marasa lafiya da wadanda suka rasu daga wurin da hatsarih ya auku zuwa asubiti.
“Lamarin ya munana, motar daukar marasa lafiya ta yi sawu kamar biyar a kokarin ceto marasa lafiya da kuma kai wadanda suka rasu dakin ajiye gawa,” inji shi.
Wani shi ma da aka yi hatsarin a gabansa masi suna Kunle ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misalign karfe 8 na dare a ranar Asabar.
“Tirelar da dauke ne da shinkafar da aka shirya rabawa masu jefa kuri’a ya kuma dauke da hotunan Sanata Tayo Alasoadura. Birkin motar ne ya lalace, mutane fiye 45 suka mutu kuma har yanzu a na ci gaba da samu wadanda suke kara mutuwa,” inji shi.
Majiyarmu ta mu ta bayyana cewa, a da sanyin safiyar Lahadi ne mataimakin gwamnan jihar Ekiti, Bisi Egbeyemi, ya kai ziyara yankin na garin Iworoko don ganin hanyoyin da suka lalace da kuma yankin kasuwar da ke bukatar daukin gaggawa ya kuma ziyarci wadanbda suke karbar magani a asibiti sakamakom hatsarin.
Har zuwa yanzu hukumar kiyaye hatsari na FRSC bata fitar da sanarwa a kan hatsarin ba, amma jammi’in watsa labarai na hukumar a jihar Ekiti, Caleb Ikechukwu, ya bayyanawa wakilinmu cewa, za iya tantance yawan wadanda suka mutu ba a halin yanzu.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!