Connect with us

LABARAI

Yaki Da Rashawa: Ya Dace A Samu Alaka Tsakanin Gwamnati Da Shugabanin Addini –Malaman Addini

Published

on

Imam Fuad Adeyemi, Babban Limami na kasa, kuma Daraktan gudanarwa na Gidauniyar ‘The Just’ ya yi kira ga shuwagabannin addini da su hada hannu da gwamnati a yakin da take yi dangane da cin hanci da rashawa a kasarnan.

Adeyemi wanda ya bayyana hakan a wani taron kwana biyu domin horas da Limamai da Malaman Islamiyyu da ya gudana a Lokoja dake jihar Kogi a jiya Lahadi.

Malamin ya ce; fiye da kashi 99 na ‘yan Nijeriya, sun yarda da samuwar Allah ta’ala, sannan sun yi imani da wani addini. Ya ce; wannan taron horaswa wanda Cibiyar Al-Habibiyyah Islamic Society tare da hadin guiwar ‘the Just Foundation’, suka shirya, sun shirya ne domin ilmantar da Malaman addinin Musuluncin dangane da mene ne cin hanci da rashawa? Ya ci gaba da cewa; wannan horaswa zai ba su damar sun fahimci illar cin hanci da rashawa, wanda za su yi amfani da wannan ilimin wajen sauya halayyar mabiyansu dangane da cin hanci da rashawa.

Limamin ya ce; kungiyar ta su, wanda Gidauniyar MacArthur ta tallafa musu, sun fara wani shiri wanda suka yiwa suna da  “Encouraging Accountability and Transparency through Faith-based Interventions (EAT-FIN).” Ya ce; manufar wannan shiri shi ne; bunkasa yadda ake bincike da tantance abu, tare da rage matsalolin cin hanci da rashawa a tsarin shugabanci ta hanyar karantar da Malaman addini. Adeyemi ya jaddada bukatar samun hadin kan juna domin yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar kulla alaka da Malaman addini.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!