Connect with us

SIYASA

Za Mu Tabbatar Kano Na Samun Kyakkyawan Wakilci A Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya –Gwamna Ganduje

Published

on

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada aniyarsa ta ganin Jihar Kano na samun cikakken wakilci a ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, muna fatan bada kaykkyawar kulawa domin samun wakilcin al’ummar Jihar Kano a kunshi ma’aikatun Gwamnatin Tarayya a kowane mataki, musamman bangarorin da suka shafi harkokin tsaro domin tabbacin da muke dashi na cewa harkar tsaro itace ya kamata ta fara zuwa a farko kafin komai domin tabbatar da tsaron al’ummar mu.
Gwamna Ganduje na wannan bayani ne alokacin da ya karbi bakunci sabbin daukar jami’an ‘yan sanda 280 wadanda suka kammala samun horo daga makarantun horar da jami’an ‘yan sanda dake Botno da Kaduna lokacin da suka ziyarci Gwamna Ganduje a fadar Gwamnatin Kano.
Wannan jawabi na kumshe cikin bayanin da kakakin gwamnatin Kano Malam Abba Anwar ya rabawa manema labarai a Kano, ya ce Gwamna Ganduje ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyarar zumunci wadda ke nuna girma da mutuntawa tare da niyyar sadaukar da kai bisa aikin da aka dauke su a kansa.
Gwamna Ganduje ya ce kun cancanci kowace irin girmawa bisa wannan muhimmin abu da kuka aiwatar wanda ke tabbatar da cewar ku nagartattun ‘yan Kasa ne.
Gwamna Ganduje ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da ganin ‘yan asalin jihar Kano na cike dukkan gurabun da aka warewa Jihar Kano, yin hakan zai bayar da dama ga al’ummar Jihar Kano su ci gaba amfana da duk wata garabasa ta Gwamnatain Tarayya. Da yake tsokaci kan jami’an ‘yan sandan guda 280 wadanda aka dauka aiki, Ganduje ya tabbatar da baiwa kowanne Naira dubu talatin wanda jimalar kudin ya kama Naira Miliyon takwas da dubu dari hudu.
Don haka sai Gwamna Ganduje ya bukaci wadanna Jami’an ‘yan sanda da su kara himma wajen tsare aikin da aka damka amanarsa a hannunsu, ya ce Allah kadai yasan irin mukamin da zaku zaman anan gaba musamman idan kuka mayar da hankali kan ayyukan ku. Ya ce zuwan wannan Gwamnati mun samu nasarar samarwa ‘yan asalin Jihar Kano 832 ayyukanyi a bangaren aikin dan Sanda, kamar yadda yanzu haka ga guda 280 da aka dauka sabbi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!