Connect with us

LABARAI

Za Mu Yi Wa Atiku Abubakar Tarba Ta Musamman A Kano –Maryam Gawuna

Published

on

Kamar yadda kungiyoyin dake kasar nan ke yi wa dan takarar shugaban kasar nan a tutar jam’iyyar PDP Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar tarba a duk jihohin da yan je yakin neman zabe.
Mu ma magoya bayan jam’iyyar PDP musamman masu kaunar ganin Atiku ya zama shugaban kasa 2019 mun shirya tarbar shi a jihar Kano musamman ranar da zai shigo jihar yakin neman zaben shugaban kasa da yardar Allah. Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugabar mata ga kungiyar ‘Bata Global Phone Assoceries Sellers for Mobement Associations 2019’ dake Kano, Hajiya Maryam Musa Gawuna, a lokacin da take zantawa da manema labarai a Kano.
Hajiya Maryam Musa Gawuna ta ce an kafa kungiyar ne domin taimakawa Atiku ya samu nasaran lashe shugabancin kasar nan 2019, domin tsohon mataimakin shugaban kasar yake da tsare tsare masu kyau domin ci gaban ‘yan kasuwa da kuma kungiyoyi, wannan ya sa wannan kungiya da suka kafa ta dukufa wajen tallata manufofin ta a wasu kasuwannin dake jihar domin taimakawa dan takarar na su na PDP.
Haka ma a matsayin na shugaban mata hatta a cikin unguwannin Kano za ta yada manufofin na Wazirin na Adamawa da yardar Allah. Sai ta yi kira ga al’ummar jihar ta Kano cewa ranar da Dan takarar zai shigo cikin Kano su ba su hadin kai da kuma goyon baya ya zo lafiya ya koma lafiya ta yadda sauran jam’iyyun adawa za su yi koyi da su wajen aika ta abu masu kyau.
Za kuma ta jajirce domin ganin ya samu nasara tare da wayar da mata ranar zabe su zabi jam’iyyar PDP musamman a zaben shugaban kasa tun da Atiku yana da dinbin masoya da magoya baya masu tarin yawa a fadin jihar Kano. Da take tokaci game da har yanzu da wasu ba su amshi katin zabe ba da cewa su gaggauta zuwa afishin hukumar zabe domin su amsa, idan kuma sun amsa su adana a wuri mai kyau idan sun je runfunar zabe kuma su zabi PDP.
Ta nuna damuwarta game da yadda harkokin kasuwanci a kasar nan suka zama wani iri ba kamar shekarun baya ba saboda haka idan suka zabi Atiku idan Allah ya so zai gyara harkokin kasuwanci tare da tallafa wa manya da kana nan yan kasuwar kasar nan musamman na jihar Kano da sauran jihohin baki daya. Idan Allah ya so zai kuma kawo karshen rigingimun da ake samu tsakani manona da makiyaya da sauran matsalar tsaro da yake addabar al’ummar kasa baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!