Connect with us

LABARAI

Zaben 2019: Kwamishiniya Ta Nemi Iyaye Da Su Kula Da ‘Ya’yansu

Published

on

A bisa yadda a dalilin siyasa ake ta da hargitsi a jihar Kwara, Kwamishiniyar kula da harkokin mata, Hajiya Taibat Ahmed, ta shawarci Iyaye da su kula da ‘ya’yansu domin kaucewa fadawa Harkar dabba a lokacin kakar kamfen din siyasa.

Kwamishiniyar ta bayyana hakan ne a wata zantawa da ta yi da kamfanin dillacin labaran Nijeriya a yau Litinin a garin Ilorin. Ta ci gaba da cewa; yanayin yadda ake ta da rigima da sunan siyasa a jihar, tabbas abin damuwa ne.

Ta ce; yanzu lokaci ne da ya kamata a daina hakan. Inda ta kara da cewa; “An san jihar Kwara da zaman lafiya da walwala, kuma mun kasance muna zaune cikin zaman lafiya, bai kamata lokacin kamfen din zabe mu rika kaiwa junanmu hare-hare ba.” Inji ta.

Har wala yau a wani bangare na jawabinta, ta ce; da yawan mutane suna fakewa a karkashin siyasa suna yada kiyayya da rashin jituwa, wanda ta ce; sam wannan bai kamata ba.

Ta bayyana hargitsin da ya faru a Lahadin da ya gabata wanda ya yi sanadiyyar lalata dukiyoyi da raunata jama’a a matsayin abin da bai dace ba kwata-kwata. Ta ce; ya kamata Iyaye su yiwa ‘ya’yansu magana su daina yadda ana amfani da su ana hargitsa zaman lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!