Connect with us

SIYASA

Wata Kungiya Ta Yiwa Buhari Alkawarin Kuri’u Miliyan 10

Published

on

Wata kungiyar mai suna ‘Coalition of Buhari/Osinbajo Movement (COBOM)’, a yau Alhamis ta bayyana manufarta na kawo wa shugaban kasa Buhari kuri’un ‘yan Nijeriya miliyan 10 a karkashin kungiyarsu a zaben 2019 da za a yi.

Daya daga cikin masu kula da kungiyar  Manjo Janar Garba Audu mai ritaya, shi ne ya yi wannan alkawarin a yayin kaddamar da kungiyar ta COBOM a yau Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Audu ya ce; kungiyarsu na aiki tukuru da magoya bayan shugaban kasar a dukkanin kananan hukumomi 774 da ake da su a kasarnan domin ganin sun samarwa da Buhari wadannan kuri’u. Ya ce; cikin sauki za su cimma wannan manufar ganin irin ayyukan da Buharin ya shimfidawa ‘yan Nijeriya a karkashin gwamnatinsa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!