Connect with us

FILIN FATAWA

Na Nemi Mijina A Kwanciyar Aure Bai Amsa Min Ba, Ko Yana Da Zunubi?

Published

on

Malam ina roko a taimaka min da amsar tambayata, malam na san idan miji ya nemi matar sa don saduwa ita kuma ta ki, ta aikata babban zunubi, to idan mace ta nemi mijinta shi kuma yaki, shi ma ya aikata zunubi ne ko ko?

To dan’uwa hadisi ya tabbata daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa “Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfidarsa ba ta amsa masa ba, to mala’iku za su tsine mata har ta wayi gari” kamar yadda Muslim ya rawito a hadisi mai lamba ta : 1436.
Saidai abin da malamai suke cewa shi ne : namiji ba shi da laifi,idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba mutukar ba da nufin cutar da ita ya yi hakan ba, domin namiji da mace sun bambanta, saboda mace za’a iya saduwa da ita ko da ba ta da sha’awa, namiji kuwa sai yana da sha’awa, zai iya saduwa, don haka akwai bukatar ace yana da nishadi kafin ya iya jima’i, idan haka ne kuwa ba zai yiwu ya sadu da mace ba duk sanda take so ba, Allah kuma ba ya dorawa rai sai abin da za ta iya, sannan sha’awar maza ta fi ta mata karfi, saboda haka yawanci namiji ne yake neman matarsa ba akasin haka ba.
Allah ne ma fi sani……

Fatawar Nan Akwai Gyara !

Malam fatawarka da ka yi akan mijin da matarsa ta neme shi da jima’i, bai amsa mata ba, ba shi da laifi, mun watsa ta a group da yawa, kuma ta hadu da kalubale, ga abin da wata take cewa:
Nake ganin idan har aka ce namiji kawai ne zai iya kusantar matarsa duk lokacin da ya so ko tana so ko ba ta so, ita mace idan ta nemi hakan ko bai biya ma ta bukatarta ba sai lokacin da ya so,Anya akwai adalci a hakan? Idan akwai istidlali nakli a taimakamin da su ba akali ba. Na ga istidlal din na akali aka kawo a rubutun.Ya za a yi mace ta nemi mijinta ya ki amince ma ta, duk da kasancewar mace tana da kunya. Amma har ta iya nemansa ka ga kuwa akwai dalilin da ya sa ta neme shi. Ai shi ma namiji ko da bai da sha’awa da an taba shi sha’awarshi za ta motsa.Kenan hakan ba zai zamo dalili da zai sa don mace ta nemi mijinta ba ya ki amincewa da dalilin wai baya da sha’awa.
Amsa:
To abin da zan iya cewa shi ne: saduwar da muke magana akanta ibada ce, ibada kuma tana bukatar dalili kafin a tabbatar da ita, babu wani dalili Wanda ya wajabtawa miji amsa kiran matarsa duk lokacin da ta neme shi, sannan yanayi da al’ada ya tabbatar da cewa namiji ba zai iya saduwa da mace ba duk lokacin da ta name shi, saboda Namiji yana bukatar nashadi kafin saduwa, sabanin mace, wacce take a matsayin katifa, wannan yasa malamai da yawa na sharia suka tafi akan cewa ba’a yiwa namiji fyade, tun da in azzakarinsa bai motsa ba, ba zai sadu da mace ba, mace kuwa an cimma daidaito za’a iya mata fyade saboda kamar tirmi take, in har an samu tabarya shike nan, wannan yasa za’a iya saduwa da mace tana bacci sabanin namiji.
Kasancewar an ce babu la’anta akansa idan matarsa ta neme shi bai amsa mata ba, ba ya nuna ya halatta ya cutar da ita, yaki saduwa da ita a lokacin da yake da nishadi.
Allah ne mafi sani.

Zan Iya Auren Ma’aikacin Banki, Alhali Ina Tsoron Cin Haram?
Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani ma’aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu’amalarsa za mu ce Alhamdulillah, to shi ne take neman menene halarcin auransa a shari’a? Saboda tana tsoron kar ya rika ciyar da ita da dukiyar haramun.

To dan’uwa Annabi s.a.w. yana cewa : “Allah ya la’anci mai cin riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka” Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598.
Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke mu’amala da riba, saboda ma’aikacin banki zai rubuta ko kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan aike . .
Duba fatawaa Allajanah adda’imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401.
Idan ya zama abin da ma’aikacin banki yake amsa haramun ne, kuma ba shi da wata sana’a sai wannan, akwai hadari a auransa, saboda zai ciyar da matarsa da haramun
Malamai suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin halal da haram, idan ya maka kyauta za ka iya amsa, saboda Annabi s.a.w. ya yi mu’amala da yahudawa, kuma a dukiyarsu akwai halal da haram, amma in ba shi da wata sana’a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin dukiyarsa ba.
Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.
Allah ne mafi sani.

Mijina Ba Ya Sallah, Ko Zan Iya Neman Ya Sake Ni?
Assalamu alaikum malam ya karatu, Allah ya kara basira, malam wata mata ce take son a fada mata hukuncin zama da mijinta da bai damu da sallah ba, ko da kuwa lokacin Ramdahana ne, sannan kuma yana tilasta mata ya sadu da ita a lokacin watan Ramdhana da rana, bayan haka yana saduwa da ita tana jinin haila, kuma ta fada masa haramun ne amma ya ki ya daina, shin malam za ta iya neman saki tun da ba ya bin dokokin Allah ko ta cigaba da zama da shi? , na gode Allah ya karawa malam basira da hazaka.

Wa’alaikum assalam To ‘yar’uwa mutukar an yi masa nasiha bai bari ba, to za ki iya neman saki, saboda duk wanda ba ya sallah kafiri ne a zance mafi inganci, kamar yadda Annabi ya fada a hadisin da Muslim ya rawaito mai lamba ta: 81.
Ga shi kuma aya: 10 a suratul Mumtahanah ta tabbatar da rashin halaccin musulma ga kafiri, kin ga cigaba da zamanku akwai matsala a addinan ce.
Allah ya hana saduwa da mace mai haila a suratul Bakara aya ta: 222, Saduwa da mace da rana a Ramadhana babban zunubi ne kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 616 ya tabbatar da hakan.
Saidai zunubin barin sallah shi kadai ya isa ya raba aure, idan har bai sake ki ba, za ki iya kai shi kotu, alkali ya raba ku.
Don neman Karin bayani duba Al-minhajj na Nawawy 2\69.
Allah ne mafi sani

Ana Biyana Albashi, Amma Ba na Zuwa Wurin Aiki, Yaya Hukuncina?
Assalamu Alaikum Warahmatullah? Barka da dare Dr dafatan kawuni lafiya Allah Yasa haka Shaikh Inada wata Tambayane a taimakamin da amsa. Dr, Matace tana aikin Gwamnati a wata jaha sai kuma barin Jahar ya kama su ita da mijinta ma’ana suka tashi kwata-kwata daga Wannan Jahar sai ya zama bata zuwa aikinta amma kuma Ana bata Salary duk wata amma Principal din makarantar da take aiki yana sane shi ya amince mata ta tafi sai kuma wani Ma’aikacin ma’aikatar Ilmi to amma ma’aikatar ba ta da masaniya, to Dr. Yaya kudin da take karba duk wata ya halatta ta ci gaba da karba ko ta daina karba? don Abin yana damunta tana ta tunanin abun koda yaushe. A taimaka min da Amsa Dr. Bissalaam.

Wa’alaikum assalam, Bai halatta ta ci ba, saboda albashi ana bayar da shi ne ga wanda ya yi aiki, halattawar da principal ya yi mata ba zai ba ta damar cin kudin ba tun da ba mallakarsa ba ne, kudin al’uma ne mabukata.
Hukuncin yana zagayawa ne tare da sanuwar dalilinsa ko rashinsa.
Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi a rai, kuma ka ji tsoran kar mutane su tsinkayo kai, kamar yadda hadisi ya tabbatar.
Allah ne mafi sani

Hallacin Addu’a Da Hausa A Sujjada!!
Assalamu alaikum. Akramakallahu mutum zai iya yin adduar neman wani abu a sujudar sallar farilla da wani yare koma bayan larabci?
To dan’uwa Annabi ﷺ yana cewa: “Amma sujjada to ku dage da addu’a saboda ya kusa a amsa muku” kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 479,
Malamai sun yi sabani akan yin addu’a a sujjada da yaran da ba larabci ba, amma zance mafi inganci shi ne halaccin yin addu’ar da take ta neman wani abu a wajan Allah da yaran da ba larabci ba ga wanda bai iya larabci ba, saboda Allah ba ya kallafawa rai sai abin da za ta iya, sannan kuma Allah yana gane duk yaren da mutum ya yi addu’a da shi, amma wasu malaman sun karhanta yin zikirorin da suka zo a hadisi da yaran da ba larabci, saboda Annabi ﷺ ya fade su ne don su zama ibada, wannan yasa ba za’a canza su da wasu lafuzan ba.
Allah ne mafi sani.
Duba: Muhallah na Ibnu hazm 4\159 da Majmu’ul fataawa na Ibnu-taimiyya 22\488.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: