Connect with us

RA'AYI

Budaddiyar Wasika Ga Mai Martaba Sarkin Kano

Published

on

Daga Bello Sagir

‘Aikatau ai yanzu a Kano ya koma wurin mata’ inji wata yarinya ‘yar kimanin shekara 14 da ta ce ita ce, take daukar nauyin gidan su.
Ya Mai Martaba Sarkin Kano, a kullum idan na bi hanyar Sharada, Dakata, Bompai har ma da ta Tudun Murtala hankali na in yayi dubu wallahi yana tashi! Za a ga tururuwan Hausawa mata ‘yan asalin jihar Kano, kamar zawarawa, mata da mazajen su suka mutu suka bar musu marayu, tsofaffi, matasan ‘yan mata da yara, da kuma musamman matan aure da ‘yan mata suna tafiya ko kuma suna dawo wa daga aikin kamfani.
Idan ba a lura da abu biyu ba za a zaci daga gidan biki suke, abubuwan kuwa su ne, rashin ado da kwalliya tattare da yawancin su da kuma alamun matsin rayuwa dake jikkunan su da fuskokin su. Suna fita a kafa kullum tun kafin fitowar rana izuwa Tudun Murtala, Dakata, da kuma Bompai. Sanna su dawo bayan faduwar ta. Sukan yi aikatau din a kamfanin nika daban-daban musamman na zobo, gyada/mai, roba, takalmi da sauran su.
A wasu unguwanni wadanda titi ya raba su, daya na karamar hukumar Nassarawa dayar kuma Ungoggo, da asussuba wadannan mata na rukunai dana ambata a sama, za a ga sun cika motar bas da suka dauko haya sun cunkushe wasu ma wasu lokuta sun zauna a cinyoyin wasu, direban ya tafi dasu can Sharada yana tuka motar da kyar, domin yin aikatau. Sannan ya dawo dasu bayan Magariba. Wadan nan mata, musamman kananan yara daga cikin su, hakika suna bukatar agajin gaggawa, ya Mai Martaba!
Ya Mai Martaba Sarki, a shekaru kadan da suka wuce, lokacin muna kananan yara, idan lokacin tashi daga aikin wani kamfani dake makotaka damu yayi, har zuwa kallon kabilu mata dake aiki a wurin muke yi cike da mamaki wai ga mata suna aikin kamfani, domin mu a tunanin mu, ai aikatau fage ne na maza kadai duba ga karfi da aikin yake bukata da kuma hatsari da yake tattare da shi, wanda yake kaiwa ga mashin ya guntule ‘yan yatsu ko kuma hannun ma-akaci dungurun gun, mafi akasarin lokuta ma ba tare da ya samu diyya da kulawa yadda ya kamata ba daga mahukuntan kamfanin, kamar yanda doka ta tanada, bamu san cewa wasu daga cikin mata daga unguwannin namu za su maya gurbin wadannan matan ba shekaru masu zuwa! Wadan nan mata, musamman kananan yara daga cikin su, hakika suna bukatar agajin gaggawa, ya Mai Martaba!
Ya Mai Martaba Sarki, akwai wani abin burgewa a irin wadannan kamfanin nikan, inda za a ga aure yana kulluwa tsakanin wasu ma’aikatan, duk da dai yawanci bai fiye yin karko ba, kuma abin haushi sai kaga in an samu akasi auren ya rabu, macen ta dawo an kara daukar ta aiki a kamfanin, ko kuma ta canza izuwa sayar da abinci a kusa da kamfanin.
A tunani na, wadan nan mata sun can-can-ci yabo na musamman domin jarumtar su wajen neman halak, in akayi la’akari da yawancin su mata ne masu jini a jika, da za su iya bada jikin su a basu kudi, sannan kuma abin su Hausawa ne ‘yan asalin Kano, kabilar da matan ta basu gaji aikin wahala ba.
A gani na, kamar bai kamata ba mazajen matan aure daga cikinsu su rinka barin matan su suna fita domin nemo abin da za su ciyar da kansu ta irin wannan hanyar ba. A gani na, kamar akwai barazana ga tarbiyyar ‘yan matan da ke irin wannan aikatau din, musamman idan akayi la’akari da wasu shugabannin kamfani maza da wata kila za su kasa hadiye kwadayin su. A gani na, kamar makomar karatun zamani wata kila ma har da na Islama na yara da matasan ‘yan mata dake cikin irin wadannan ma’aikatan babu ce, duba ga cewa a lokacin zuwa makaranta suke yin akin. A gani na, kamar akwai bautar wa da ci da gumin yaran da matasan ‘yan matan. Wadan nan mata, ya Mai Martaba, musamman kananan yara daga cikin su, hakika suna bukatar agajin gaggawa! A gani na, kamar irin wannan aikatau din yana zubar da kimar kabilar Hausa musamman na birnin Kano, la’akari da cewa shekarun baya, kabilun daba Hausawa ba ne kawai suke irin wannan aikin, musamman da Allah ya azurta Hausawa da sana’oin gargajiya na mata daban-daban. Ya Jagoran Muminai, a gani na, kamar mabiya wasu addinan daban za su yi mana kallon hadarin kaji a matsayin matan na musulmai, musamman duba ga barazana da hakan yake ga addinin matan. A gani na, kamar ‘yan matan dake cikin wadannan ma’ikatan basu shirya sosai ba domin zama uwayen ‘ya’yan da muke fatan za su haifar da al’umma ta gari ba.
Ya Mai Martaba, akwai bukatar a dau mataki akan lokaci, domin gudun kada nan gaba fitintinu su fara afkuwa ko kuma bayyana daga wadan nan kanfanin nika, musamman da wani ma’aikaci a irin wadan nan kamfanin nikan ya shaida min cewa, a kamfanin su babu bambanci tsakanin bandakin maza da na mata. Ya Sarki mai share kukan talakawan sa, a gani na, kamar wannan ne lokacin da ya fi dacewa a dau matakin hana faruwar wata matsala a irin wadan nan kamfanin nikan.
Ya Mai Martaba Sarki, rokonmu ga mata shi ne, su rika kara yin hakuri suna tattalin aurensu domin gudun mutuwarsa. Su ma mazan su kara hakuri da matsalolin mata, domin kaucewa yawan sakin su. A ci gaba da hakuri da juna, wata rana sai labari. Ya Mai Martaba kiran mu shi ne, irin wadan nan mata su koma ga sana’oi na gargajiya da aka san Hausawa mata dasu, musamman na birnin Kano, tun asali. Masu hannu da shuni, hukumomi da kungiyoyin tallafawa mata su ninnin ka tallafi da suke baiwa mata, musamman wadanda aka bar musu marayu. Anan gabar, Ya Mai Martaba, Uban Talakawa, ka can-can-ci a yaba maka matuka dangane da taimako ga marasa karfi da ka shahara wajen yi tun kana karami, musamman bayan ka zama Sarki, kamar wanda kake yi a kofar fadar ka da sauran su. Allah ya jikan magabata ya hada ka dasu a gidan Aljanna. Allah ya saka maka da alkhairi, ya tsare ka daga dukkan sharri, ya kuma baka tsawon kwana mai albarka, sannan ya tsare gami da albarkar iyalin ka. Ya Sarki Mai Adalci, wadan nan matan, talakawan kane, kuma basu da wani mai taimaka musu sai kai.
Na tabbata baka san da faruwar wannan al’amari ba, domin da tuntuni ka dau matakin ceto rayuwar su, shi yasa na yi wannan rubutun, ina mai kyautata zaton cewa za ka share musu hawaye, domin mu a wurin mu, Allah ya kara maka lafiya, matan nan, kakanin mu ne, iyayen mu ne, yayyan mu ne, kuma uwa uba, kannen mu ne! Wadan nan mata, musamman kananan yara daga cikin su, hakika suna bukatar agajin gaggawa!
Daga talakan ka, Bello Sagir, belsagim@gmail.com
0813251714
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!