Connect with us

TATTAUNAWA

Bunkasa Rayuwar Mata Da Kananan Yara Ne Babban Buri Na –Hadiza Abubakar (4)

Published

on

Ci gaba daga jiya…
A lokacin da UNISCO din nan suka zo jihar Bauchi sun nemi wacce kungiya mai zaman kanta ne take da irin wannan shirin da suka zo jihar da su, sai suka gano cewar B-SWEEP tana da tsare-tsare kan irin wannan manufar nan suka gayyace musu muka yi hadaka muna tattaunawa suka duba irin bayanan da muka harhado kan wannan shirin nan take suka ce ai su sun samu wani sauki, tun da ga bayanai da muka tattaro da kiyasin adadin ababen da muka kwaso.

UNISCO sun amshi sunayen mata dari biyar da ashirin daga hanunmu, tunin har sun fara aiwatar da shirin, sun horar da malamai da za su yi aiki, an saye na’urar kwamfuta don ganin yadda za a yi wannan aikin. Yanzu haka ana nan ana ta kan tattaunawa da UNISCO da sauran hukumomin bayar da agaji ciki har da B-Sweep, ta wannan hanyar alakar tamu da UNISCO muke kan aiwatar da wannan tsarin namu na maida yara ‘yan mata da mata da suka fara karatu abun ya tsaya nan domin ilmantar da ‘yan mata.

Wani karin bayani da zan maka, da ya ke a fom din da muka rabar wa mata na shigar da bayanai, akwai wajen zabin ra’ayinka, wasu sai suka zabi a maimakon karatu su sana’a suke son yi, to wannan tsarin sai muka yi horo kashi biyu, na farko akwai wadanda muka yi musu horo da hadin guiwar wata kungiya da ake ce mata Mahema mun fara ne da mutane dari da hamsin, muka horar da su muka basu kayan sana’a, kashi na biyu mun dauki mutane 350 muka horar da su muka basu kayan sana’a a wannan tsarin mun dan sirka har da matasa ba zallar mata ne kawai suka ci gajiyarsa ba, mun basu horo kan sana’o’i irin su alminiyun, masu hada kofa, masu hada jakurkuna, takalma, masu gyaran gashi da sauransu dukkaninsu dai an basu tallafin kayan aiki a cikin wannan shirin. Fom din ne muke bi mu gano mene ne ya kamata mu yi, mu gane cewar wadannan karatu suke son yi, wadannan kuma suna son sana’a ne. muna sa ran cewa tsarinmu da Unisco din nan zai kawo mana sauyi da yadda mata za su samu karin ilimi sosai. Domin yadda aka dauko abun wani tsari ne da ko a waje mace take malami zai shiga ya bata ilimi, ko a gona kike akwai hanyar da za a koyar da ke karatu, in ma a kicin dinki kike akwai yadda za a koyar da ke karatu kina aikinki kina jin yadda za ki samu ilimi. Cikin ikon Allah wannan shirin zai kai ga gagarumar nasara

Da kusan karshe ke ce shugaban matan gwamnonin arewa kawo yanzu me kuka sanya a gaba?

Kamar yadda ka sani a yanzu ni ce shugabar matan gwamnonin arewa wanda shi wannan shugabancin abu ne wanda ake yinsa karba-karba, wata ta yi ta sauka, yanzu nice na ke yi, ni ma zan gama wa’adina. Daman a dokar kungiyarmu ta ajiye kan cewar za a ke shugabancin ne shekaru biyu-biyu. Idan kika kammala shekaru biyu idan ana so sai a sake maidawa, idan kuma ba a so sai a zabi wata. Amma dukkanin aiyukan da muke yi tare muke yi, aiyukanm daya bakinmu daya, manufofinmu daya.

Shi wannan ‘forum’ da aka assasa babbar manufar samar da shi, shine mu matan gwamnoni mu samu wani dandamali wanda za muke tallafa wa mazajenmu gwamnoni domin a samu nasararo ta fannin kawo ci gaba da samun nasarar aiwatar da aiyukan da suke zo da su a jahohinmu.

Da muka yi nazari a wannan lokacin sai muka fahimci babbar abubuwan da suke damunmu a yau a arewa suna da yawa, akwai batun ilimin mata, akwai zancen kiwon lafiya na mata muna da ci baya sosai a irin wannan fannonin, amma kuma sai muka ga akwai wata babbar matsala da ta kunno mana kai ta shaye-shayen miyagun kwayoyi da ‘ya’yanmu suke yi. Wannan dalilin ne ya sanya muka dauki wannan babin a matsayin babban aikin da ke gabanmu a wannan lokacin, shine muka sanya a gaba domin tabbatar da an samu rage shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin jama’a duk da yake akwai matsalar a fadin Nijeriya amma namu na arewa lamarin ya fi kamari ko na ce mu ya fi damunmu don haka muke da burin ganin an samu mafita mai sunan mafita domin rage wa lamarin karfi.
Da in ana maganar miyagun kwayoyi matsalar za ka ji ta ne kawai a cikin matasa, amma da abun ya yi kamari sai muka gano cewar matasa suna shaye-shayen miyagun kwayoyi, mata na yi, har matan aure a gidajensu suna sha, matan masu arziki suna sha, matan talakawa suna sha, samari da tsofaffi suna sha, don haka wannnan babbar matsala wacce idan ba a tashi sosai aka yakeshi ba to babu shakka zai dulmiyar mana da al’umma wanda nan gaba kuma abun ba zai yi mana kyau ba. a bisa haka ne muka dauki matakan gyara da rage kaifin matsalar. A kungiyar matan gwamnonin arewa muna amfani da kwararru hukumomi da kungiyoyin da suke da alhaki kan wannan lamarin da suke yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi a cikin kasa da kuma masu tallafa na kasashen waje irin su ‘United Nations Office on Drugs and Crime’ (NUODC), ‘National Drug Law Enforcement Agency’ (NDLEA), da sauransu muna aikin da su domin cimma nasara. kamar UNODC sun tara matan gwamnonin nan suka yi mana horo ta yadda za mu yi yaki da miyagun kwayoyi a jahohinmu.
Yanzu haka kowace matar gwamna, a jiharta akwai shirye-shiryen da take aiwatarwa da zai kai ga kawo sauki da nasarar rage ta’anmuli da miyagun kwayoyi a tsakanin jama’a. kuma Allah ya taimakemu a cikin irin aiyukan da muke yi mun samu mun kai ziyara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya karbemu hanu biyu-biyu. Matar shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ita ce ta jagorancemu wajen kai wannan ziyarar, mun fada masa damuwowinmu da kuma irin taimakon da muke son a yi a gwamnatance da zai karfafi abun domin yakin da muke yi da shaye-shayen nan ya yi tasiri sosai, a cikin ikon Allah a ‘yan kwanakin baya da suka wuce sai aka kaddamar da kwamiti na musamman kan hanyoyin da za a kawo sauyi a wajen shaye-shayen miyagun kwayoyin nan. mu ma a jihar Bauchi din nan mun yi iyaka namu kokarin wajen shawo kan matsalolin da suke fuskantar shaye-shayen miyagun kwayoyin nan, mun kaddamar da kwamitin yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin jama’a, inda muka samar da Kansiloli 100 da za su taimaka mana wajen aiwatar da wannan shirin na gangamin yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin jama’a.

Hajiya Hadiza me za ki shaida daga karshe?

Kira zan yi ga jama’an jihar Bauchi da babban murya, abun da nake son na fada wa jama’a shine gwamnatin APC ta yi rawar gani wajen tafiyar da gwamnati da ciyar da jihohi da kasashe gaba. Kawo yanzu idan ka duba APC daga sama har kasa za ka tabbatar an samu ci gaba, ka duba yadda aka samar da aikin hanyoyi, tsaro, zaman lafiya, farfado da tattalin arziki, samar da aiyukan yi da shugaban kasa ya kaddamar wanda hakan ya kawo wa jama’a ci gaba. Idan muka dawo jihar Bauchi ma haka gwamnatin APC ta yi, ka duba aiyukan hanyoyi da ake yi idan da za ka zagaya cikin jihar za ka ga hanyoyin da ake yi, ga gyaran makarantu, samar da ababen more rayuwa, zaman lafiya da kwanciyar hankali da sauransu. Don haka muddin APC ta sake samun dama a karo na biyu a jihar Bauchi za a cimma muhimman nasarori don haka ina kiran jama’a a yi APC daga sama har kasa.

Hajiya mun gode gaya?

Ni ma na gode.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: