Connect with us

LABARAI

Matasa Sun Kona Mace Da Ranta A Nasarawa

Published

on

A jiya alhamis ne wasu gungun matasa suka kona wata mata da ranta a garin Nasarawan Eggon. Abin ya faru ne a tsakiyan gari kusa da ofishin hukumar tsaro ta farin kaya ta (NSCDC), abin ya faru ne da misalin karfe daya na rana. Lokacin da wasu kananan yara suka taso daga Makarantar Boko, sai matar ta kira daya daga cikin kananan yaran ta janye shi gefe.
A lokaci guda hankalin jama’a ya kai kanta, saboda ita matar tana da siffar Mahaukata, da ka ganta, ka ga mahaukaciya. Duk da cewa jama’a sun lura babu alamar hauka a tattare da ita, amma shigarta ta mahaukata ne. Kuma ya zo daidai da halin da al’umman garin Nasarawan Eggon, suke ciki na fama da sace-sacen yara kanana.
Hakan ya sanya suke zargin ire-iren wadannan mahaukatan saboda duk da cewa ita a siffar mahaukata take, amma tana amsa wayar salula na hannu.
Kiran yaron da ta yi zuwa wani sako, kan ka ce me! Jama’a suka yi ca a kanta, duk da cewa shedun gani da ido sun ce a lokacin da aka kamata da yaron ta fara magana cewa ba ita kadai ba ce, ta fara jawabi amma zuwan wasu jama’an suka afka mata da duka da sanya wuta nan take ta yi kasa.
Duk da kokarin da jami’an tsaron (NSCDC) suka yi domin su cece ta a hannun matasan amma abin ya ci tura har sai da suka kona ta.
Ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin babu wani jawabin da Hukumar (NSCDC) ko ta ‘yan sanda suka fitar duk da kokarin mu na neman jin ta bakin jami’an tsaron, amma ba mu samu lokaci ba, saboda rashin shigar wayansu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!