Connect with us

TATTAUNAWA

Manufar Tukunyar Gwari Shi ne Tallafa Wa Manoma — Bawa Kaya

Published

on

Wakilinmu da ke Zariya, BALARABE ABDULLAHI ya sami damar zantawa da Babban Manajan kamfanin TUKUNYAR GWARI cibiyar da ke Zariya, ALHAJI AHMEDBAWA KAYA,wanda makasudin kafa wannan kungiya shi ne na ganin an tallafa wa manoman da suke karkara da sauran wurare a ciki da wajen jihar Kaduna.

Ga yadda tattunawarmu ta kasance da babban manajan wannan kamfani da aka ambata Za mu son ji daga bakin ka dalilan da suka sa aka kafa wannan kamfani da ya ke da jibi da harkar noma.
Babu ko shakka babban dalilin day a sa mu kafa wannan kamfani na mu da mu ka rada ma sa Tukunyar gwari shi ne ganin a karkashin wannan kamfani, manoma da suke tare da mu, sun amfana da wannan kamfani, da kuma amfana da noman da suke yi, maimakon yadda manoma ke yin noma, amma ba sa amfana da noman na su, wato ta yadda tattalin arzikinsu zai bunkasa, a cikin dan kankanin lokaci.
Yanzu ga shi mun shiga sabuwar shekara ta 2019, za mu so jin nasarorin da ku ka samu, a shekarar da ta gabata, wato shekara ta 2018.
A gaskiya, ba abin da za mu cewa Allah a halin yanzu, na yadda mu ka tsinci kanmu a shekarar da ta gabata 2018, sai dai mu ce mun gode wa Allah, na yadda mu ka sami nasarori,kuma manoman da suke tare da mu, su ma sun fi kowa sanin nasarorin da mu ka samu.Har ila yau, dykkanin nasarorin mun same su ne, daga farkon damuna ya zuwa karshen damuna, sai kuma sabuwar shekarar da mu ka shiga, zuwa yau, sai dai godiya ga Allah.

Wane dalilai suka zama silar nasarorin da ku ka samu ?
A gaskiya,mun sami nasarorin ne a yau, saboda yadda mu ka ba manoma iraruwa a kan lokaci, na bashin da mu ke ba su a cikin sauki kamar yadda wannan kamfani na Tukunyar gwari ta saba bayar wag a manoman da suke tatre da mu kimanin shekara bakwai zuwa takwas da suka gabata.

A kalla, daga farkon shekarar da ta gabata, wato a watan Janairu zuwa watan Disamba, manoma nawa suka amfana da tsare-tsaren da kuke aiwatar wa ?
Babu shakka, manoman da suke hulda da mu a wannan kamfani, sun kai dubu uku, daga kananan hukumomi guda shida a jihar Kaduna, kananan
hukumomin su ne, Giwa da Zariya da Kubau da Ikara da Birnin Gwari da Igabi da kuma karamar hukumar Sabon gari.Kuma dukkanin kananan hukumomin da na bayyana ma ka, a nan ne wadannan manoma dubu ukun suke, kuma zan iya ce ma ka, su suka amfana da dukkanin abubuwan da mu ka tsara a shekarar da ta gabata.

Ya batun kungiyoyin da manoma suka kafa, ya nuna ba ku mu’amala da kungiyoyi ke nan ?
Ai lallai mu na mu’amala da kungiyoyi kuwa, domin zan iya ce ma ka, mu na hulda da kungiyoyi guda dari biyu da saba’in da shida [ 276 ], mu ke tare da su, a duk ayyukan da mu ke yi daga kafa wannan kamfani na mu, zuwa wannan shekara ta 2019 da mu ke ciki.
Kuma wannan kamfani na mu,bai tsaya aiwatar da ayyukansa a jihar Kaduna kawai ba, mu na hulda da manoman da suke jihar Neja da jihar Nasarawa da kuma jihar Jigawa, su ma duk suna karkashinmu a wannan kamfani na mu da ken an Zariya.

Ku na nuna wa manoma yadda za su yi amfani da wannan sinadiri ke nan ?
Ai babu ko shakka, mu na nuna ma su, ta yuadda za su yi amfani da wannan sinadiri ako wane kadada da suka noma, misali a shekarar da ta gabata 2018 , mun tsara ake wane kadada, shi ne Naira dubu hamsin da bakwai da dari biyar, tun da duk tsare-tsarenmu babu inshora a cikinsa, sai mu ka tabbatar wa manomi lallai ya fahimci wannan tsari ban a gwamnati ba ne, na TUKUNYAR GWARI ne, domin a shekarun baya, gwamnati tan a bayar da tallafin, amma wajen dawo da kayayyakin sai ana samun matsaloli, inda manoma ke yin koke-kokensu daban-daban, kamar ba su kayayyaki da wuri ba, ko kuma rowan sama ya dauke da wuri, da dai sauran matsaloli da suke fitowa daga manoma.
Mu na bayar da iri kilo ashirin ne a kadada daya, wannan masana ayyukan gona suka amince da wannan tsari da mu ke aiwatarwa, sai buhu shida ako wane kadada, sai wannan sinadari da na bayyana ma ka a baya, in an tattara abubuwan da aka ba manomi, shi ne zai buna yawan kudin da aka ambata a baya., da farko sai kamfani ya ce, manomi ya bayar da Naira dubu bakwai da dari biyar , wato tamkar shigar ciniki ken an, ya yadda zai hulda da wannan kamfani na mu, mu kuma za mu ba bi shi bashin Naira dubu Hamsin, mu na bayar da kayayyakin da aka ambata a watan hudu, kayayyakin za su kasance a wajen manomi, wata hudu kafin faduwar damuna.

Mene ne ka’idarku bayan manomi ya kammala noman da ya yi ?
In ya cire masarar day a shuka a gonarsa, maimakon ya ba mu Naira dubu hamsin da mu ke binsa, sai ya ba mu masara.kuma mu mu ke sayen masara da tsada daga hannun manoma a duk Nijeriya, a kan dubu takwas da dari biyar, kuma a halin yanzu, duk kasuwannin da ka je, ana sayar da masara kasa da dubu bakwai ne, amma mu mu ka karba a farashin Naira dubu Takwas da dari biyar.A ko wace kadada manomi zai ba mu buhu shida, amma manomi ako wace kadada, zai sami buhu arba’in zuwa arba’in a biyar.Wato ya sami buhunan da mu ka ambata, shi buhu shida kawai zai ba mu, shin ba a tallafa wa manomi ba ?

A nan wasu shawarwari ka ke da su ga manoma?
Shwarwarin su ne, da farko manomi, tun a watan daya, ya fara tunanin gonarsa da kuma yadda zai yi noman da kuma abin da zai shuka a gonarsa ko kuma gonar da ya sami aro, to in manomi ya yi wadannan abubuwa da na bayyana ma ka, zai yi nomansa a cikin kwanciyar hankali a karshe kuma ya sami ribar day a kamata, da kuma zai yi mamaki.

Kafin ku fara hulda da manomi, ku kan tabbatar da gonarsa, ta ziyarar gani da ido, kafin ku fara ba shi abubuwan da ka bayyana ma na a baya ?
Lallai mu na kai ziyarar gani da ido ga gonakin manoma, domin wani sai ya ce, ya na da kadada biyu, in mun je, sai mu ga kadada daya ya ke dashi, wannan na faruwa ne ga ma su son yin noma, amma ba su san yadda kadada ta ke ba.

In manomin da ku ke hulda ya sami matsala a abin da ya shuka, misali masara, a kwai mafitan da ku ka tsara, domin daga wa manomin kafa ?
Ba mu da wannan tsarin, domin tun farko na bayyana ma ka wannan tsari ba inshore, in har manomi ya bi tsare-tsaren da mu ka nuna ma sa, da kuma shawarwarin da mu ka ba shi,ba a cika samun wata matsala ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: