Connect with us

TATTAUNAWA

Masu Shirya Finafina Na Bayar Da Gagarumar Gudummowa A Harkar Zabe –Kwamared Yarima

Published

on

KWAMARED YARIMA SHATTIMA, Jigo ne a cikin kungiyoyin Matasa da ke fadin tarayyar Nijeriya, ya shaida wa ‘yan jarida a cikin wata tattaunawar da ya yi da su a Kaduna cewa babban dalilin da ya sa suka yi taro da Jaruman masana’antar shirya Finafinai shi ne irin yadda kowane zamani yake zuwa da tsarin, don haka suka yi la’akari da irin yadda ‘Yan uwa, kanne da kuma Yayye da ke sana’ar Fim suke kokarin fadakar da mutane a kan harkar al’adu , addini da wasu abubuwa domin Jama’a su san me ake bukatar su sani, musamman mutanen Arewa.

Wace rawa kake ganin masu shirya finafinai za su iya bayarwa a harkar zabe a kasar nan?
Wannan ne ya sa muka ga ya zama dole wannan fadakarwa, kamar yadda muka lura Gwamnati na kokarin yin amfani da wasu daga cikin ‘yan Fina-Finan nan da muke wa addu’ar Allah ya sa su gane, domin hadarin da ake ciki a yanzu. Shi ya sa muke kokarin ganin mun yi dukkan mai yuwuwa a aika wa Talakawa da sako ta yadda za su fahimci abin da ake ciki a yanzu.
Shi ya sa wadannan masu sana’ar Fim da suke mu’amala da mutane, musamman talakawa da sauran al’umma baki daya shi ya sa dole a yi amfani da su ta yadda sako zai sauka a wurin talakawa ta yadda kowa zai fahimci abin da ake ciki.
Saboda haka aka ga cewa a bar su haka nan kara zube a bar su, ba zai yuwu ba, don haka su ma su zo a tafi tare da su a yi tare duk da ba siyasa suke yi ba, amma su dai su taho a yi da su domin al’umma su fadaka su gane abin da ake ciki, domin ana yin siyasa ne saboda a samu ci gaba a dukkan inda al’umma take baki daya, wannan ya sa ka ga sun zo baki dayansu kuma mun kira Jama’a da suka hada da manya na kasa baki daya domin su halarci taron domin su kara fadakar da mutane irin ci gaban da za a samu idan an samu sabuwar Gwamnatin da cikin ikon Allah muna saran za a samu, hakan nan gaba kadan.
Kuma idan ta zo, lallai za a juya abubuwa har ya zamanto su wadannan masana’antar Fim din nan su samu wani abu da za su kara bunkasa harkokinsu saboda za a ba su gagarumar gudunmawa sosai.
Suma kowa ya sani suna bayar da gudumawa, saboda a madadin a bar wadannan yara da ‘yan mata suna yin abubuwan da bai kamata ba, za a samu ingantuwar al’amura, musamman ganin irin yadda masana’antar Fim ke sama wa wadansu dimbin jama’a aikin yi.
Kuma hatta yara maza, yin Fim din zai kawar da matasa su daina yin shiga cikin bangar siyasa da sauran wasu abubuwa na alfasha da abubuwan ki a cikin al’aumma, saboda sako ne suke aika wa ‘yan siyasa na yi, su ma suna yi da fatar za a samu nasara kwarai, wadanda kuma suka ta fi suna ta shiga harkar Gwamnati. Da fatan za su dawo domin su fahimci irin hadarin da yake a cikin wannan Gwamnatin. Domin a yanzu, gaskiya ba Gwamnati ake yi ba, Yarbawa ake yi wa Gwamnati, haka kawai. Saboda haka ba za mu yarda ba, Arewa ba ta samu nata kason ba.
Kasar Yarbawa ba su da wata asara idan Gwamnatin ta tabarbare, domin duk abin da suke bukata sun samu, kuma yau ko da babu wannan Gwamnatin, suna ganin tun da an yi tsarin cewa Mataimakin Shugaban kasa zai fito daga kasar Yarbawa suna ganin cewa za su iya karbar mulki su ci gaba.
Saboda haka mu abin da ya dame mu a nan shi ne, muna son sake wata sabuwar yarjejeniya ta shekaru takwas, domin Arewa ta samu fita daga cikin halin kuncin da ta shiga shekaru, ba wai muna batun shekaru hudu ba, saboda shekarun nan hudu ba abin da dan Arewa ya samu banda kunci da wahala.

Yanzu ana ganin cewa mafi yawan mawakan fim din nan sun ta’allaka a bangaren gwamnati, sai ga wannan taro da ake ganin kamar zai iya kawo masu farraka a tsakaninsu?
A’a, gurbatattu ne kawai suka je can, akwai wasu a nan da a da can suka bi waccan tafiya, amma Allah ya taimake su sun dawo, duk abin da ake takama za a dauka a ba ka, domin kana gwamnati ai wata rana za a wayi gari ba ka Gwamnatin, to wane tanaji aka yi maka?
Kuma alkawarin da APC ta yi masu, za a yi masu kaza da kaza. Shin me ake cika masu alkawarin? Amma saboda yaudara da kuma kwadayi na wasu sai suka bangare suka koma can, ai wannan ya zama an ci baya, tun da an ce ba a san mutuncin ku ba sai ku dawo ku hada kanku saboda a gudu tare a tsira tare. Ba wani abu ya sa an debi waddannan ba, kwadayi ne kuma ko a zuciyarsu sun san ba a yi masu adalci ba. Don haka muna nan hannun mu a bude a matsayinmu na shugabannin matasa, a karbesu in sun dawo su zo a kafa sabuwar Gwamnati ta za ta iya tafiya da kowa da kowa. Don haka kusan in ce wannan mulki na APC ba abin da ya kawo ma Arewa illa ci baya da masifa da kuncin rayuwa, domin babu wani abu, in kuma an ce ba haka ba, to a gaya mini wani abu daya da aka yi wa Talakan Arewa da za a iya nunawa a ce ga abin da aka yi. Wannan shi ne batun Gaskiya.
Abin da muke yi shi ne fadakar da mutane domin wata rana za a tuna da abin da muka yi na fafutukar ceton kasa da jama’arta baki daya. Ko ba yau ba, za a tuna cewa mun gano wannan hadarin da ke gabanmu. Don haka a Ankara, kada mu fada cikinsa.
Na farko, babu wani zamanin da aka yi Gwamnati da ta raba kawunan jama’a kamar wannan, kai ya bace babu tunani irin wannan lokacin ko a cikin Arewa ma kai ya rabu, ba ma wai tsaknin Arewa da Kudu ba, in an taba su su kawo mana maganar addini, in an yi magana su kawo batun kabilanci, amma idan sun zo batun raba kudin talakawa raba wa kawai suke a tsakaninsu, ba wani batun bambanci ko kadan, wannan dole ne mu haramta shi mu yake shi, mu ga yadda za mu ceci babban kalubalen da ke gabanmu baki daya.

Kaddamar da tashar jirgin ruwa da Shugaban kasa ya yi a jihar Neja, wasu na ganin aiki ne da ba a taba samun irinsa ba?
Su suka yi shi, ai ba su taba yin abu sun kare shi ba. Hanyar Jirgin ba su suka yi ba, dama ita gwamnatin da ce kawai ta yi, domin Jonathan dai ya yi aiki. Da ma maganar hanyar Jirgin da ake yi ba su taba faraway sun kare ba, duk yaudara ne kawai. Don haka a gaya min abu daya da suka fara (as Policy) suka kare shi babu ko daya babu.
Saboda haka wannan yaudara ne ana samun mutanen da ba su da fahimta, domin jama’a ba su da wani cikakken bayani, ana rudarsu da karya da yaudara, kuma duk wannan yaudarar nan da wata daya ta kare. Don haka ina kira ga jama’a da su fito da karfin mu da kuri’armu da duk abin da za mu yi amfani da shi mu karya wannan Gwamnatin.
Maganar magudi bai ma taso ba, domin ‘yan Nijeriya idanunsu ya bude. Muna kiran al’ummar kasashen waje, kamar yadda muke mu’amaloli da su, da su tabbatar sun sa idanu sosai domin wannan babakeren da Gwamnati ke ganin za ta yi, ba zai yi wu ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!