Connect with us

RA'AYINMU

Sauya Sheka Ba Ita Ce Mafita Ba, Yi Wa Jama’a Aiki Shi Ya Fi

Published

on

Sau da yawa idan lokacin siyasa ya zo a Nijeriyasu ‘yan siyasar sune ke kara ruruta wutar, siyasa har wani lokaci ma su magoya bayan su ‘yan siyasar, sune zasu daurewa ma su zabensu kai, su rasa wurin da zasu sa kansu, ko hankalinsu ya kwanta su gane ina ya kamata ne su dosa a tafiyar tasu. Kafin zabubbukan shekarar 2015 akwai ‘yan siyasa wadanda suka canza sheka musamman ma daga jam’iyyar mai mulki a lokacin PDP zuwa babbar jam’iyyar adawa a lokacin wato APC. Kowa kuma ya san abinda ya faru har lokacin da aka yi babbar taron jam’iyyar, aka ce shugaban kasa mai ci a lokacin Goodluck Ebele Jonathan, shi ne dan takarar jam’iyyar a lokacin.
Idan dai ba mantawa aka yi ba wannan dalili ne ya sa, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya jagoranci gwamnonin Kwara, Adamawa, Sokoto, Kano, Ribers, da tsohon shugaban jam’iyyar PDP suka je, Shehu ‘Yaradua Centre, inda suka bayyana kafa sabuwar PDP. Daga nan ne kuma sai a hankali suka ma fita daga jam’iyyar gaba daya zuwa babbar jam’iyyar adawa a lokacin APC.’Yan siyasa zuwa yanzu dai ya kamata su gane su Talakawa musamman na Nijeriya, ba maganar canjin sheka daga wannan jam’iyyar zuwa waccan ta dame su ba, babban abinda suka fi bukata shi ne yi masu ayyuka tukuru wadanda zasu bunkasa rayuwarsu.
Duk kuma dan siyasa wanda ya san shi dan siyasar ne, ba muna siyasa ba, abinda ya dace ke nan yayi la’akari da shi cikin zucuyar sa, irin ayyukan da ya yi ma al’ummar shi. Sune zasu ja ra’ayinsu, suce ai ya dace ya tsaya masu takara saboda ya wakilce, a kujerar dan majalisar jihar, ta wakilai ta tarayya, ta dattawa, har zuwa ta shugaban kasa ma. Ba sai ya ma taba miyon bakin shi ba, yana cewa ai ya cancanta ya tsakara, idan ma ya cancantar ai ya sani. Wasu ‘yan siyasa suna ganin kamar idan sun canza sheka daga wannan jam’iyya zuwa wancan, hakan zata sa a su al’ummar nasu su sake zabarsu, amma wani idan ma har ya riga ya canza to yafa tafi ke nan, a daina jin duriyar shi akan harkokin siyasa. Shi da kan shi ma wani lokaci yak an gogawa kan sa kashin kaji ya gane cewar ashe shi yadda yake ganin kan shi ba hakanan bane.
Babban abinda ake bukata a rayuwa shi ne hakuri, saboda sau da yawa sai an yi shi ake samun cimma burin na komai a rayuwa, ba ma kawai al’amari na siyasa ba, saboda shugabannin siyasa na farko da basu yi irin shi namijin hakurin ba , suka a hankali da har yanzu matakila muna karkashin mulkin mallaka na Turawan Ingila. Abinda suka yi shi ne sun bi a hankali ne saboda dai Hausawa sun je sannu bata hana zuwa, ana dan dadewa ne ba a je wurin da aka yi niyya ba, amma cikin ikon Allah watarana za a kai ga zuwa can, amma je saboda ai tuni muka samu ‘yancin kanmu kusan shekarau hamsin da takwas ke nan. Allah ya jikan maza su Alhaji Abubakar tafawa Balewa, Dokta Nmamdi Azikwe, Ahmadu Bello Sardauna, Chief Obafemi Owolowo, Chief Ladoke Akintola, Dokta K. O. Mbadwe, Sir Kashim Ibrahim, da dai sauransu sun jajirce suka nuna cewar Nijeriyar ce cikin zuciyarsu, ba wai wani mukamin da zasu rike ba. Duk kuwa a lokacin da akwai bambance bambance na addini, kabilanci, da kuma harshen da kowa ya tashi ya ji ana magana da shi a gidansu, hade kansu suka yi, su kashe su rufe ba wanda ya sani, sukan samu rashin jituwa, amma wani lokaci ma basu barin ma wasu su ji halin da suke ciki.
Yanzu dai ba maganar canza sheka ta kamata ace ta mamaye zuciyarsu ba, saboda ai ba a dade da amincewa,da kasafin kudin wannan shekara ta 2018 ba, akai kuma ayyukan da ya kamata su yi ma al’ummarsu, ba maganar canza shekar siyasa ba. Saboda suna da damar su da kuma matsayin su na ’yan Nijeriya, suna da wannan damar. Kamata yai an yi taka tsantsan kada abin ya kawo rarrabuwar kawuna, domin kuwa, dama duk wanda ya mallaki gida yana da ikon ya kwana duk dakin da yake bukata ba wanda ya isa ya hana shi.
Ba fa jam’iyya su Talakaa ke gani ba har abin ya basu sha’aar yanke shawarar dan siyasa ba ,, kamar dai yadda aka yi bayanai, akwai wadanda sun fara daga shugaban karamar hukumar, sannu a hankali sai da suka kai, ga takarar kujerar Sanata. Alal misali Sanata Lado Danmarke ya fara ne daga shugaban Karamar Hukuma, sai da ya yi Sanata da kuma tsayawa takarar gwmna, amma kuma na sai da aka hada da haduri.
Talakawa dai suna kallon yadda al’amura ke tafiya, daga cikinsu kuma akwai wadanda suka ga jiya, shekaran jiya, da yau akan harkokin siyasa, idan annhada kai dasu ma za a daukai darussa masu yawa da zasu yi amfani, danagane da ita siyasar, saboda ai dama mai daki shi ne ya san inda ruwa ke zubar mai.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!