Connect with us

TATTAUNAWA

Yi Wa Doka Karan-tsaye Da Gwamnati Ke Yi Ya Sa Wasu ‘Yan Kasa Ke Karya ta – Sannen Lauya

Published

on

Wakilinmu ABUBAKAR ABBA ya tattauna da wani sanannen lauya matashi da ke jihar Kaduna, BARISTA AMINU ABDULRASHEED Esk a kan zaben 2019, musamman kan yada kalaman batanci da yada labaran karya da wasu kafafen yada labarai suke yi a kasar nan, da sauransu, da kuma yadda gwamnati ke yi wa dokokin kasa karan-tsaye, da yadda al’ummar kasa ke amfani da wannan da wajen karya doka da oda. Ga kuma yadda tattaunawar ta kasance:

Yallabai a ganinka ‘yan siyasa da masu rike da madafun iko a kasar nan suna girmama doka da oda kuwa?
Abin yana da fuskoki da dama, a makarantar da ake koyar da harkar Shari’a, za a gaya maka cewar dan’adam yana kallon dokar ce da za ta yi masa amfani kuma duk dokar da za ta hukunta shi ko hana shi yin abin da ransa yake son yi, duk yadda zai yi, zai yi don ya bijere mata, sai dai idan ya tabbatar da abin da ake cewa hukunci da zai iya biyo baya.
To, idan ka duba abin da ke sa sanya a bi doka da oda, shi ne idan akwai matakai na tursasa a bi doka da odar kuma idan aka ki bi, a hukunta wanda ya ki bi. Idan kuma ka dauki ‘yan siyasa ko kuma in ce gwamnati, a yanzu takan bi doka da oda, amma akwai wa’adin da takan bi. Akwai wani lokaci za ka ga doka da oda a kanta ne, to sai ka ga an kauce wasu abubuwa wanda misali ka san cewar, ya saba wa ka’ida amma kuma misali a gwamnatance, su ne ke da hurumin na idan aka ki bin doka da oda ya zamo shi ne mai karya doka da odar, za ka ga babu wani hukunci da ke biyo baya.
Hakan kuma zai bayar da kafa kowa ma ya taka doka da oda ko kuma idan ya samu sako-sako ya kaya doka da oda domin akwai abubuwa da dama da gwamnati ke yi da a shari’ance, sai ka ga ya saba wa ka’ida ko kuma karya doka ce wani lokacin ma har da kundin tsarin mulkin kasa wanda shi ne babban jagora na tafiya da mulki. Haka su ma ‘yan siyasar, wani lokacin gwamnati ta nemi a yi wani abu sai a shigo da siyasa a ciki duk da a wani lokacin za ka ga gaskiya ce suka yi, haka wannan abin ya shafi fannoni da dama.

Ba ka ganin hakan ne ke janyo wasu ‘yan kasa suke taka doka da oda?
Ai shi ne dama matsalar, da ake samu domin daga lokacin da gwamnati ta saba shi ne ke sanya wasu ‘yan kasa su ma suke saba wa su kuma ‘yan siyasa, su siyasantar da hakan.

Babu wani tanadin hukunci a kan kalaman batanci a kasar nan da wasu keyi, musamnan idan aka yi la’akari da zaben 2019 da ke tafe?
Akwai su da dama a cikin kundin tsarin laifuffuka na kasa da suka hana yin kalaman tunzura jama’a, cin zarfin jama’a wani lokacin har hakan yakan janyo kashe-kashe ko kone-kone, akwai hukuncin dauri da sauransu, wani lokcin ma in har ta kai ga rasa rai, wanda ya janyo hakan shi ma za a yanke masa hukuncin kisan. kuma duk masu yin kalaman, suna sane suke yi.

Maganar labaran karya yana kara zamo wa rowan-dare a Nijeriya, shin babu wasu kwararan matakai da aka tanada a shir’ance na hukunci?
Ka san shi maganar hukunci, matakai ne da dama da kan hada har su kai ga samun kai ga yanke hukunci. Na farko, in aka samu laifi, akwai hukumomin gwamnati na bincike wadanda suka hadada ‘yan sanda, DSS, Cibil Defence da sauransu, idan abin ya kai ga hankalin su, ko kuma aka gabatar masu da korkafi sukan yi bincike bayan sun tara hujjojin su sai su gurfanar a gaban kotu. Wasu kafafen yada labaran ma ko rijista basu da ita, haka kafafen sadarwa na zamani da suke yada labaran karya. Al’umma su ma suna masu ruwa da tsaki ne a kan dakile yada labaran karya domin ba ko ina ne ba jami’an tsaro suke ba amma in an gabatar da korafi, a gaban hukumomi sai su bi kadin har a kai ga kotu don yanke hukunci, kotuna da dama sun yanke hkunci a kan yada labaran karya a kasar nan.

Wasu Jigajigan yan siyasa a kasar nan suma suna kara rura wutar kalaman kiyayya ina mafita akan hakan?
Wayar da kai kadai bai isa ba, sai ana daukar matakai da daman a hukunta mutum komin girman sa da yake yin kalaman kiayya a kasar nan ta hanyar hukunta mutum komin girmasa kuma komin matsayinsa.

Wasu ‘yan siyasar suna yin amfani da matasa wajen yin bangar siyasa, wacce shawara za ka bai wa matasan?
Babbar shawara ta ga irin wadannan matasan ita ce, su kasance masu neman ilimin zamani dana addini da kuma rungumar sa’aoin yi don kauce wa zama karnukan farautar ‘yan siya wajen yin amfani da su don tayar da tarzoma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!