Connect with us

LABARAI

Ba Mu Sauya Cibiyar Tattara Zabe Daga Zwall Zuwa Dass Ba – INEC

Published

on

Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Bauchi (INEC) ta musanta zarge-zargen da a ke yi ma ta na kokarin tafka magudin zabe a sakamakon wasu sauye-sauyen da jama’a su ke zargin hukumar ta bijiro da su daf da fara zaben 2019 da ke tafe.
Kwamishinan hukumar zabe (INEC) a jihar Bauchi, Alhaji Ibrahim Abdullahi, shi ne ya karyata zarge-zarge da bayanin cewar babu wani yunkurin yin magudi da su ke yi ko tauye ma wata jam’iyya hakkinta.
Kwamishinan INEC ya musanta zargin ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a sakariyar ‘yan jaridu jimkadan bayan da ya kammala jawabinsa a wajen taron kara wa ‘yan jarida sani kan yadda ake daukowa da sadar da rahotonnin zabe, wanda NUJ ta shirya.
Idan ba ku mance ba, jam’iyyun adawa da kuma masu ruwa da tsaki daga Tafawa Balewa, Dass, da kuma Bogoro sun yi ta zargin shirya magudi daga INEC a sakamakon take-taken da su ke ganin na kokarin sauya mu su cibiyar tattara sakamakon zabe daga Zwall zuwa Dass daf da lokacin zabe, wanda su ka bayyana hakan da cewar shirin magudi ne muraran.
Kana kuma wasu zarge-zarge sun biyo bayan aikin da INEC take yi na yin kwaskwarima wa ofishinta da ke karamar hukumar Ningi inda nan ma wasu jam’iyyun adawa suka bayyana cewar yunkurin janyo dalilin da zai sanya a kai cibiyoyin tattara sakamakon zaben zuwa barikin ‘yan sanda ko na soji ne kawai.
To sai dai Kwamishinan INEC din ya yi watsi da dukkanin zarge-zargen da kuma yin bayanin abun da ke faruwa a zahirance, kamar yadda yake cewa, sun amshi takardar korafi daga wasu mutanen mazabar Dass T/Balewa da Bogoro inda suke bukatar a sauya cibiyar tattara sakamakon, a yayin da kwanaki guda bayan amsar wannan bukatar kuma wasu ayarin jama’a suka yi zanga-zangar kin amincewa da hakan.
A cewar shi: “Wannan zargin ba gaskiya ba ne. dangane da zargin da ake yi kan za a sauya cibiyar tattara sakamakon mazabar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro daga Zwall zuwa Dass, abun da ya faru shi ne, na samu takardar korafi daga mutanen da suke cewa su mutanen wannan mazabar ne inda suka bukaci na sauya cibiyar, washe garin ranar da na amsa kuma na sake samun wani takardar korafi wanda shi kuma ke cewa su basu yarda a sauya cibiyar tattara sakamakon zaben ba.
“Abun da na yi shi ne, tun da akwai kwamiti da masu ruwa da tsaki a yankin, sai na umurci baturan zabe a wannan mazabar da su gayyaci masu ruwa da tsaki a wadannan mazabar kan cewar ga takardun korafi guda biyu da muka samu, sai su tattauna a zartar da matsaya kan abun da ke akwai,” Inji shi
Ya kuma kara da cewa; “An yi wannan taron an tattauna da masu ruwa da tsaki an kuma kawo mana sakamakon da aka zartar. Ni kuma na tura wannan sakamakon wa magabatana, ni dai na aike da sakamakon zaman, kuma har zuwa yanzu babu wani abun da aka ce min, don haka wannan cibiyar tattara sakamakon zaben mazabar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro har zuwa yanzu yana nan inda yake a Zwall,” Inji Kwamishinan.
Kan zargin da ake yi wa INEC na kokarin tafka magudi a yankunan Ningi a sakamakon ganin sun bayar da aikin kwaskwarima wa ofishin INEC da ke Ningi daf da fara zabe, kwamishinan ya yi karin haske, “Abun da ke faruwa gabanin zabe daman akan yi dan gyare-gyare a ofisoshinmu da suke bukatar gyara. An bayar da irin wannan aikin a Dambam da Alkaleri wanda ‘yan kwangilar sun kammala aiyukansu na wannan garuruwan.
“Abun da ya faru a Ningi shi ne dan kwangilar ne bai zo da wuri ba. amma a bisa rahoton da na samu dan kwangilar na kan aiki sosai, yanzu ina shawartar duk mai son tabatarwa ya je ya duba,” inji shi
Ibrahim Abdullahi ya kuma bayyana cewar tabbas za a kammala wannan aikin kafin a fara aikin zaben. Ya ce, ba wani shiri ne suka yi domin tafka magudi ba.
Ya kuma yi amfani da damar wajen bayyana cewar sun kammala nasu shirye-shiryen, illa kawai suna jiran ranar gudanar da zabe da sauran kayyan aiki masu bukatar taka-tsantsan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: