Connect with us

ZAMANTAKEWA

Buhari Zai Iya Rasa Kashi 50 Na Kuri’un Bauchi, Cewar Aminu Tukur

Published

on

An bayyana cewar da iyuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya iya rasa kusan kashi 50 na daga cikin dumbin magoya bayansa a jihar Bauchi, a sakamakon daga hanun gwamnan jihar Bauchi Muhammad A. Abubakar da ya yi a matsayin dan takarar gwamnan jihar a zaben 2019 da ke tafe.
Tukur, wanda yanzu haka dan majalisar dokokin jihar Bauchi ne, ya shaida hakan ne a lokacin da ke ganawa da wasu kebantattun ‘yan jaridu har da wakilinmu a gidansa da ke Bauchi, ya kara da cewa, al’ummar jihar Bauchi sun gama gazawa da gwamnati mai ci a jihar a sakamakon gaza aiwatar da aiyukan raya jihar da gwamnan jihar ya kasa yi, ya misalta gwamnatin da cewar ta kasa-kasau.
Honorabul Aminu Tukur ya shaida cewar Buhari zai rasa tulin kuri’un da ya saba samu da kashi 50 a jihar a sakamakon biyewa M.A da ya yi, inda yake mai shaida cewar jama’an Bauchi ba su ji dadin wannan matakin ba.
A a bakinsa; “Buhari ba zai samu gagarumar nasara kamar yadda ya saba samu a jihar Bauchi a wannan zaben da ke tafe ba. Tabbas Buhari yana da magoya baya kashi 90 a jihar Bauchi, amma yanzu Buhari ya rasa magoya baya kusan 50. A bisa dalilin zuwansa da ya yi da ya daga hanun Muhammad Abudllahi Abubakar, wannan dalilin ya rage wa kansa farin jini a cikin al’umman jihar.
Ya kuma ce hakan zai baiwa Buhari wuyar samun nasara a jihar Bauchi a zaben 2019, “Ina shaida wa jama’a ko shi Buhari zai sha wuya kafin ya ci zabe a jihar Bauchi. Ko ni kaina da kuke gani ba zan sake zaban Buhari ba kuma, haka kuma ina tabbatar da cewar da dama na sun dauki wannan matakin,” Inji Aminu Tukur
Da yake bayani kan zaben 2019 a matakin jihar Bauchi, Tukur ya zargi gwamnatin jihar da kokarin tafka magudin zabe, “Muna da tulin dalilai da za mu iya bayyanawa da ke nuni da cewar gwamnati mai ci a jihar Bauchi tana shirin kawo rudani a yayin zaben 2019.
“Zai kasance da abun mamaki idan gwamnati mai ci tana fadi wa jama’a cewar jam’iyyun adawa suna yunkurin tayar da hargizi a zaben 2019, kawai dai ita gwamnatin ba ta gamsu da sahihinacinta ba ne ya sanya take kame-kame, domin kuwa gwamnatin ta gaza wajen kyautata rayuwar jama’an jihar.
“Gazawa na ban mamaki kuwa, ba mu taba samun gwamnati a jihar Bauchi da ta gaza gudanar da aiyukan raya jihar ba kamar gwamnatin Muhammad A. Abubakar domin ta baiwa jama’a mamaki sosai; gwamnatin da ta shafe shekaru uku da kusan wata bakwai amma ta gaza nuna wasu aiyuka na sama da naira miliyan 50 a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar, wannan babban gazawace ga gwamnati. abu daya da ya dace kawai ita ce, gwamnati ta amince ta gaza ta nemi hanyoyin shawo kan gazawarta domin jihar ta samu ci gaba,” Inji shi
Aminu Tukur ya jawo hankalin jami’an tsaro domin su gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta shimfida musu, ya kuma shaida cewar dukkanin wani shirin amfani da wata hukuma don yin magudi jama’an jihar Bauchi suna shirye da su dakile hakan, “Kowa ya ga yadda jama’an jihar Bauchi suka kwaci ‘yancinsu a zaben 2007 da makamancinsa da ya wakana a zaben 2015, ina shaida muku a 2019 ma jama’an jihar Bauchi sun san hanyoyin da za su yi wajen sauya shugabanin da basu gamsu da shugabancinsu ba, babu wani da zai iya tsayar da yadda jama’a za su sauya wadanda basu gamsu da su ba, domin jama’an jihar Bauchi sun gama wayewa a kan siyasa,” in ji shi.
Honorabul Tukur ya yi fatan a yi zabe lafiya, inda ya jawo hankalin hukumar INEC a jihar da jami’an tsaro da su tabbatar da sun yi aiyukansu kamar yadda doka ta shimfida domin kauce wa shigar da magudi a zaben da ke tafe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!