Connect with us

ADABI

Daga Littafin ‘Mene Ne Sanadi?’ Na Rabi’atu SK Mashi (4)

Published

on

Cigaba daga makon jiya

Ya jinjina kai, “Kai keda abun mamaki fa, ya wuce mamaki har ma ya fara ba ni tsoro, tayaya ka gano inda nake? Bayan nafi wata daya a asibitinnan ko waje ban leka ba”
“Ni fa ko nemanki banyi ba, kawai dai ki dauka Allah ne ya sake hadamu”
“Ki yi break fast din mana”
“Ba na jin yunwa yanzu”
Ya tabe bakin daya zame mishi jiki, ko don yaga yana mishi kyau?
“Yanzu abunda kika fi so kenan? Ki raunata jikinki ki zauna jinya?”
“Ita fa mutuwa da kike gani Habiba lokaci ne da ita, idan har lokacin ki baiyi ba, bazata taba zuwa, sai dai kiyita wahala kaman yanda kika kare a gadon asibitin nan, shin bazaki hakura ba? Ki bude idanuwanki, ki fuskanci rayuwarki a yanda tazo miki, duk abunda ke faruwa dake jarabawa ne Allah yake miki, ki daure kici jarabawar nan Habiba, Allah baya daurawa bawansa abunda yafi karfinsa, karki bari zuciyarki ta kaiki ga halaka”
“Wacce irin rayuwa zanyi a duniyar da kowa kanshi kadai ya sani? Wacce irin rayuwa ce da zan iyayinta ni kadai? Duniya ita ta juyamun baya, kuma mutuwa take gudu na, ya zanyi da bakin cikin dake zuciyatah?”
“Ka fara sauraren labarinah kafin ka yanke mun hukunci, ka fara sanin dalilina sannan.”
Mikewa tsaye yayi, ta daga kai tana kallonshi,
“Na dauka saboda alkawarin dana maka ne ka nema inda nake, ko ka fasa jin labarin nawa ne?”
“Ban fasa saurare bane, kawai na tabbatar sanda kikamun alkawarin bani labarinki, baki taba tunanin sake haduwarmu bane, don haka ki bari sai kin shirya bani labarin naki don kanki”
“Alkawari na maka, ya zama dole na cika maka, ina son sauke nauyin dana dauka a kaina”
“Ba damuwa, ki sakamun lokacin da kike so”
Duk da cikin matsuwa yake da son jin labarinta, anma hakanan ya ji ya na tsoran jin dalilinta na son kashe kanta, yana son jin labarin, anma tsoran dake ransa yafi yawa.
Ya na fita yaa juya baya, sai ga doctor Salihi shima ya shigo, tana tsaka da break fast.
Shi ma gaishe shi ta yi, ya amsa mata cikin murmushinsa kamar ko yaushe,
“Za mu fara Round ne, na biyo inga yanda kika kwana”
“Godia nake doctor, yau ma dai babu maganar sallamar tawa kenan?”
“Za mu sallameki mana, damun tabbatar kin karasa warkewa”
“Na warke fa, babu inda kemun ciwo a jikina, ba wani magunguna na ke sha ba, hakanan nake zaune fa, sai yaushene zaku sallameni in tafi yin abunda ya kawoni?”
“Ki kara hakuri, yanzu bara in dawo sai mu karasa.” Ta jinjina kai alamar yarda da hakan.
Daya fita ya dade tsaye a kofar dakin, meyasa ya kasa sallamarta? Meke faruwa dashi da yake son kasancewa da ita ko yaushe?
Ya na bukatar shawara, don haka ya fiddo wayarshi don kiran Aminin nashi, wanda shi kadai ne yasan sirrinsa, kuma yake neman shawara a wurinshi.
Sai da gaban Deen ya fadi ganin kiran Dr. Salihi a lokacin, ya tsaya tunanin kodai ya ganshi ne sanda yaje wurin Habiba? Yadai da ke ya daga kiran.
“Ka na ina Abokinah?” Zargin da yake ya kara tabbata, “Lafiya dai na jika wani iri?” “Lafiya lau, kawai ina son ganinka ne yanzu” “Kai banson iskanci, kaman wata mace zaka ce kanason ganina”. “Kai fa dan iskane, ka tsaya kaji mezan fada maka mana, wallahi ina cikin damuwa, kuma bansan meke damuna ba, wai kasan har yanzu na kasa sallamarta?”
Wani yawu daya makale mishi a makoshi ya hade, sannan yace, “wacece wai?”
“Patient dinnan da nake baka labari, wani iri nakeji a raina game da ita, abunda ban taba ji game da wata mace ba”
“Wannan ai ba wata sabuwar magana bace, ka saba fadamun hakan duk lokacin da kaga wata budurwa”
“Kai wai meka mai dani? Nifa ba ce maka nayi ina sonta ba, kaga yaushe zan shigo muyi magana?”
“Ba sai ka shigo ba, anjima zan shigo kaman lokacin jiya”
“Yauwah ko kai fa.”
Haka abotar tasu take, Deen mutum ne mai zurfin ciki, ba komai ne ya ke faɗldi ba, koda laifi mutum ya mishi bai iya magana, sai ma idan abun ya ɓata mishi rai ne yake iya fadawa babban Amininsa Dr. Salihi, anma ko shi ba komai ne ya sani na sirrinsa ba, bawai don bai yarda dashi ba ne, kawai dai wasu abubuwan yafi son ya barma kansa sani ne.
Yayin da shi kuma Dr. Salihi, bashi da wani sirrin da Deen bai sani ba, surutu ne dashi da yawan son fara’a.
Ta na makale a jikin kofa tana saurarenshi, abunda take zargi ya kusa tabbata kenan? Don me Dr. Salihi zai ki sallamarta? Kar dai ace son ta ya ke, wata zuciyar take take ce mataa, inaa karki tsaya, karki kara barin ma wani saurayi damar dazai fada miki kalmarso, duk haka suke, duk karshen labarin nasu daya ne Yaudara, duk da wani gefen na zuciyarta cike yake da tausayinsa.
Da sanyin marece/yamma, Habiba ta shirya barin asibitin don ta san lokacin Dr. Salihi bai cika zuwa inda take ba, cikin takardun magungunanta, ta dauka wata ta rubuta mishi,
“Thank You”
Kawai, ta daura mishi saman laptop dinsa dake ajiye gefen gadonta, sannan ta sulale ta bar asibitin.
***
Da fitar ta daga Asibitin ta samu mai Napep ta tsayar, sai da ta shiga ta mishi kwatancen unguwar dazai kaita, suka tafi.
Dai-dai lokacin shi kuma Deen ya iso asibitin wurin Doctor Salihi, kaman ance ya daga idonsa, ya ganota tana shiga cikin Napep din, aikam ya juya akalar motarsa yabi bayanta.
Suna tafiya yana biye da ita daga baya, har suka dauki hanyar zuwa Unguwarsu, Estate ne da sai wanda ya amsa sunansa mai kudine yake zuwa wurin yayi gini, gaba daya gidajen unguwar masu kyau ne da tsada
Mai Napep din da take ciki ne ya ce, “Hajia ko dai laifi ki kai? Na lura fa motarnan ta bayanmu tun daga Asibiti take bin bayanmu?”
Gabanta ne ya fadi? Ta dan matsa inda zata iya ganinta ta mirrow, sannan ta ce, “dan shiga kwanar nan mu gani”
Ya juya Napep din ya shiga, sai ga motar Deen ta sake shiga layin, ta shaida motar sosai, bata sha wahalan fahimtar shine a cikin motar ba,
Tace da mai Napep ɗin, “Tsaya nan kawai” “Hajiya kin tabbata a tsaya ba matsala?” “eeh, ka ajeni nan kawai”
“Toh Hajiya” ya tsayar da motar, ta zaro dubu daya ta mika mishi, ta fita zata tafi,
“Hajiya canjin fa?” “Ka je da shi kawai.”
Yanata mata godia ta tafi inda motar Deen take, daman tunda yaga sun tsaya, shi ma ya tsayar da tashi motar.
Bude gaban motar kawai tayi ta shiga, ya tsaya yana kallonta, “Mu je ko?” Tana nuna mishi hanyar da zai bi, Ya tada motar ya fara dribing, sannan yace mata, “har yanzu kina tunanin akwai inda zaki boye ba tare dana gano ki ba?”
Ba ta ba shi amsa ba, sai dai ta sake nuna mishi da hannu, “nan za ka bi,” Ta cigaba da nuna mishi inda zai je, har zuwa kofar gidan nata. Fita tayi zuwa wurin gate din, ta daga wani murfi, malatsai su ka bayyana, ta latsa password sai ga kofar ta bude, ta shiga daga ciki ta bude mishi gate din, ya shiga da mota.
Garin dadi na nesa, inji angulu data leka masai, in tsaya fada muku haduwa da tsaruwar gidan da Habiba take ciki bata lokaci ne, duk da kyaun gidansu Deen, ganin gidan da Habiba take ciki, duk sai ya raina tsaruwar nasu gidan.
Gidan kanshi tituna ne a ciki, ga furanni a gefen kowanne titi, da kuma fitulu masu launi, titinnan shine zai sadaka da duk inda zakaje a cikin gidan, akwai wanda yayi hanyar lambu, da kuma wanda yayi hanyar wurin wasanni da motsa jiki, idan aka mike kuwa shine zai sadaka da cikin gidan.
A nan tsaruwar take ta ban mamaki, bene ne zai sadaka da cikin gidan, gaba daya ginin gidan da glass aka yishi, harta benen da za a taka zuwa babban falon na glass ne, a ciki ne sauran dakunan suke, duk dai yanda kuke tunanin haduwa da tsaruwa na gidan da Habiba take ciki ya wuce nan. Wurin ajiye motocin gidan, mota biyu ne duk masu tsada, banda wacce ya tada ganinta da ita, da itane tayi accident.
Zuciyarsa ta fara bugu, ganin mahaukatan kudin da aka kashe wurin gina gidannan kawai, nan take ya fara tunanin kodai Habiba ta na cikin mutanen nan dake tara dukiya da jinin wasu? Yayi ta maza dai ya nema wuri ya zauna cikin daya daga cikin kayatattun kujerun dake falon.
“Ni kam Habiba sai Yaushe ne zaki daina bani Mamaki?”
“Duk lokacin da kasan ko wacece ni, zaka daina mamaki na, kuma zaka daina ganin laifina don na nema kashe kaina.” Ta ajje mishi lemun data dauko a fridge, sannan ta zauna kujerar dake fuskantarsa, har lokacin yana cikin karewa dakin kallo.
“Mutane da yawa na fadin, kudi sune jin daɗin duniya, anma…” Ta katse shi da cewa, “duk wanda kaji yana faɗar hakan, yana tare da duk wani abunda zai saka shi farin ciki a kusa dashi, kawai dai kuɗin yafi gani”
“Ban fahimci maganar ki ba”
“Za ka fahimta ne a lokacin daka gama sanin labari na, ka shirya saurarar labarin nawa ko har yanzu baka gama bibiyar tawa ba?” “Ina saurarenki”
Ya katse dogon firar nasu, saboda yanda ya kara matsuwa yaji ta yanda ta tara wannan dukiyar mai yawa haka.
“Yanzu zakaji labari nah, zakasan kowacece Habiba, labari na yana da yawa, sai dai banson ka manta komai daga ciki, idan na gama sai ka yakemun hukunci da kanka, idan ya dace na kashe kaina ko akasin haka”
Ya gyara zama yana saurarenta…

Za mu cigaba a makon gobe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!