Connect with us

TATTAUNAWA

Munafurci A Tsakanin Marubuta Ya Yi Yawa –Saifullahi

Published

on

Matashin marubuci Saifullahi Lawan Imam, ya fadi haka ne a cikin doguwar hirar da suka yi da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, ADAMU YUSUF INDABO, hirar da mu ka soma kawo muku ita makon da ya gabata. Ga cigaban hirar:

Cigaba daga makon jiya

To, wacce nasara kake ga ka samu daga fara rubutunka zuwa yau duk da tarin kalubalen da ka fuskanta?
Na samu nasarori masu dimbin yawa da daukaka ta ban mamaki, kadan daga ciki sun hada da, sanin manya da fitattun mutane da nayi, da kuma suna da daukaka, domin takai ta kawo daga garuruwa ana kawomun ziyara, wani lokaci idan naje taro soyayya da kauna da kulawar da ake nunamun har kuka na ke yi saboda farin ciki, sannan sanadin rubutu babu inda ba zan iya shiga ba, komi matakan tsaron dake wajen kuwa, babu mutumin da ba zan iya gani ba, baya ga alfarma da nake da ita. Masha Allah ko nan na tsaya na godewa Allah. Sannan duk dai saboda rubutu na zama dan gwagwarmayar kare hakkin dan adam, inda na jagoranci kwato hakkin mutane masu yawa a kotuna daban daban, hakkin da suka hada da kadarorin gidaje, shago, filaye ,da nau’in zalunci akan marayu da marasa galihu, gwagwarmayar da sai da ta yi sanadin zuwana gidan yari har sau uku, sannan sanadin rubutu,na zama dan jarida , duk wadannan ababen silar rubutu na same su, kaga wannan nasara ce babba.

To, bisa la’akari da yadda mata suka kwace kasuwar littafi kai ba ka karaya ba ne da na ji ka ce kana aikin littafinka Mace Baiwar Allah?
Kwace kasuwa da mata suka yi ba zai shafi farin jinin adabin bariki ba, ai kasan sai an kasa kanwa a kasuwa ake sanin aukinta, ina tabbatar maka da cewa littafin Mace Baiwar Allah, zai bada mamaki, zai zamo zakaran gwajin dafi da zai danne duk wani littafi a kasuwar adabin Kano, saboda ba alfahari ba, na yi amfani da wani salo tare da wasu rikitattun zaruruwan labari da ba a saba gani ba, idan ko marubuci ya yadda da kanshi kamata ya yi a ce ya san duk wata hanya da zai zo ko fito da wani salo na daban wanda barazanar mamayar kasuwa da mata marubuta suka yi ba za ta shafe shi ba.

Amma me kake ganin dalilin da ya sa mata suka kwace kasuwar adabi?
Saboda mata sun kware wajen rubuta labaran da suka shafi, rayuwar aure da matsalolinshi tunda su ne ke gida kai namiji kana waje, sannan ciwon ya’ mace na mace ne, sun fi ka sanin kan abun, kai kuma namiji sai ka biye musu ka dauki alakalami kai ma ka rubuta soyayya da rayuwar auren da baka da ilimi a kai, ta yaya kake tunanin na matan ba zai fi naka armashi ba, kaso 90% na makaranta mata ne, idan suka je kasuwa suna neman littafin matsalolin aure ko soyayya ta ina za su damu da littafin namiji tunda mai daki shi ya san inda ke masa yoyo, wannan dalili ya sa mata suka kwace kasuwa. Shi ya sa ni kuma na fito da salon da zai rage musu armashi a kasuwar.

Ko ka san ba mamayar da mata suka wa harkar ce kawai ta sa marubuta maza suka ja da baya ba har da matsalar kasuwa?
Matsalar kasuwar littafi wallahi ban dauke ta wata matsala ba, mu marubuta mu muka so hakan,in ba mu so ba ‘yan kasuwar littafi ba su isa su raina mu ba,inda marubuta za su hada kai su tunkari wannan matsalar ina tabbatar maka sati guda yayi yawa muga bayanta, inda matsalar take shi ne munafunci a tsakannin marubutan yayi yawa, ban manta da wani gagarumin yunkurin saita kasuwar adabi da mu ka yi ba na Mu Gudu Tare Mu Tsira Tare, ina ce munafunci ne ya tarwatsa tafiyar? Shi ya sa na cema matsalar kasuwar littafi na marubuta ne ba ‘yan kasuwar ba, idan suna musu su hada kai, tafiya daya da murya daya su gani idan yan kasuwa basu shiga taitayinsu ba.

Ai matsalar kasuwa a yau ita ce ta rashin ciniki, ko kana da shawarar hanyar dakile wannan annoba da ta cuso kai duniyar rubutu?
Ba ciniki ne ba ayi ba, ai wani salon kabilanci da wariyar launin fata muka samu awajen ‘yan kasuwar littafi, inda suke zaben ya’yan mowa da na bora, misali idan marubuta suka kawo littafi kasuwa, abunda ’yan kasuwa suka fi dubawa shine matsayinka a harkar rubutu, misali anty Fauziyya D Suleman ta kawo littafi Amrah Auwal ta kawo nata,to koda na Amrah yafi na Anty Fauza armashi, haka za su jibge shi a sama su manta da shi saboda Amrah sabuwar marubuciya ce, ita kuma Anty Fauziyya ta jima sosai tana da masoya, haka za ai ta maka jeka ka dawo daga karshe ma a fito fili a gaya maka littafinka ya ki siyuwa alhalin ko kasa shi ba su yi ba. Misali na biyu. Ina tunanin ba ku san cewa ‘yan kasuwar ke dankwafar da cinikin littafanmu ba, hujja a nan ita ce, ai ‘yan kasuwar labari suke siya a wajen kananan marubuta, sai su saka sunayen matansu ko kanninsu ko ma su kirkiri wani sunan daban su sakawa littafi, su dauki nauyi a buga, idan makaranta suka zo siyan littafi haka dan kasuwa zai ta kuranta nashi yana kushe na marubutan, zai nunawa makaranta cewa ai nashi din yafi dadi da komai, wanda a rana zai siyar da nashi, fiye da kwafi ashirin amma bai siyar da na marubuta kwafi biyar ba, sai lokacin amsar kudi yayi a kama kwan gaba kwan baya tsakannin dan kasuwa da marubuta,don haka matsalar kasuwa bakin ciki da kyashi daga ‘yan kasuwa ya kawo haka. To hanya daya ta yi wa wannan matsalar kwaf daya shi ne marubuta su hada kai su bude babban bookshop da za su rinka dillancin littafansu da kansu, kamar yanda aka fara samun wannan yunkurin daga mabambantan mata marubuta kamar, mace mutum bookshop na Rahma Albdulmajid, da Teemah bookshop na Fatima Danborno,ga na Anty Sadiya Kaduna, duk da hakan ma yunkuri ne mai kyau, amma hada kai a bude guda daya kwakkwara a Kano shi ya fi in ya zama daga baya a bude branch a ko ina, a maimakon a ci gaba da zama a tsitstsinke, hada kai ne mafita kawai akan duk wata matsalar marubuta.

Ko kana da abun cewa game da rubutu a yanar gizo da a yanzu shi ma ya samu tagomashin yawaitar marubuta da makaranta?
Marubutan yanar gizo ko ince online writers suna da amfani kuma suna da hatsari ga rubutun Hausa da marubuta, amfaninsu shi ne saukaka karatu da taimakawa wajen habaka harshen Hausa, sannan marubutan online sun fi marubutan gidi saukin cusa sha’awar karatu ga Hausawa da ma wadanda ba Hausawa ba, ban da wadannan ba zan karar da wani abu na amfani ba, sai dai rashin amfani da hatsarinsu.
Za mu ci gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!