Connect with us

ADABI

Tarihin Jihadin Shehu Usmanu Mujaddadi Danfodio

Published

on

Cigaba daga makon jiya.

Fara Yakin Jihadi

Sa’ar da Shehu Usmanu da jama’arsa suka yi hijira, sai Sarkin Gobir Yumfa ya umarci sarakunan garuruwansa da cewar, su kame duk wani mai shirin zuwa ga Shehu Usmanu.
Ai kuwa sai su ka shiga fitinar Musulmai mabiya Shehu Usmanu da kisa, azabtarwa gami da kwace dukiya.
Da wannan hali ya kazanta, sai Musulman da sukayi hijira suka soma fita yakin jihadi izuwa garuruwa.
Ya zama suna kame kananun garuruwa a hankali har sukazo wani gari waishi Giniga, yaki kuwa yayi tsamari anan.
An ce duk da an halaka Musulmai da dama a yakin, wasu manya kuma daga tawagar Shehu sunyi shahada, amma dai saida sukayi nasarar kame garin. Suka kashe na kashewa, wasu kuma aka kame su.
Daga nan su ka fita yaki zuwa Matan Kari, nan ma suka ci garin da yaki, suka sake nufar wani gari mai suna Wata Alkarya, shima suka cinyeshi da yaki, sannan suka samu nasarar cinye garin K’wanni da yaki.
A wannan shekara ta farko dai, an gwabza yake-yake masu tsauri, amma cikin ikon Allah duk mutanen shehu ke samun nasara.
Akwai Yakin Kwato da akayi a shekarar, shikuwa yaki ne mafi girma wanda sai dai a Kwatantashi da Yakin Badar a tarihin kafuwar Musulunci, ko kuma yakin Daukar girma a tarihin Yakin Jihadin mutanen shehu Usmanu a Kano.
Sarkin Gobir fa sai hankalinsa ya dugunzuma, ya shiga shirin yaki haikan.
Ya aike da takardu na neman taimako izuwa sarakunan Katsina, Kano, Zazzau, Daura da Azbin, duk kuwa saida suka bashi tallafin daya nema, sannan suma suka kaura kamarar yaki da duk wani mai alaka da Shehu Usmanu a biranensu.
Daga nan Sarkin Gobir Yumfa ya fita daga garinsa, ya kwana a ‘Bore, sannan yahau ya riski Gamba, yabi ta Makida, sannan ya sauka a Tsara ya kwana. Daga nan sai gashi a Janar-Sarki ya kwana biyu anan yana sauraren wasu k’arin dakaru. Bayan sun isone ya fuskanto Gudu da gagarumar runduna.
Koda Shehu da Mabiyansa suka ji Labarin yaki na gabato su, sai suka dau harama suma.
Wazirin Shehu, kuma kaninsa, watau Abdullahi, ya taso da rundunar mayaka izuwa gefen wasu gidaje suka sauka suna jira, har yamma tayi basuji komai ba, sai suka koma da baya.
A kwana na biyu ma suka sake yin kamar haka, amma babu abinda ya faru.
Sai a kwana na uku ne wasu ‘yan uwansu fulani suka iso garesu a sukwane, suka shaida musu cewar daga cikin rundunar sarki Yumfa suka sato jiki, kuma yaki ya kusa zuwa garesu, tunda kuwa rundunar tana garin Ayame ne, tsakaninsu da garin kuwa tafiyar yini daya ce..

Kashe gari, Musulmai suka sake fita jiran Sarkin Gobir da tawagarsa, suka fake tsakanin wasu duwatsu da ake kira Maliba.
Can kuwa babu jimawa sai ga runduna ta iso gagaruma, sarkin Gobir na tsakiya ana buga masa tambari.
Koda rundunonin suka fuskanci juna, sai suka aukawa juna da yaki.
Yaki yayi tsamari, amma sai girgije ya hadu a sama, aka soma zubda ruwa. Don haka kowa ya koma sansaninsa.
Da ruwa ya tsagaita, sai kowa ya sake dawowa fagen fama, aka sake abkawa fada gagarumi.
A wannan rana, mabiya Shehu Usmanu ne sukayi rinjaye, sune kuma harda rarakar magoya bayan Sarkin Gobir Yumfa da gudu.
Mutanen Sarkin Gobir dashi kansa suka sauka acan kusa da tafkin kwatto, Wazirin Shehu Usmanu, Abdullahi ya kwashi jama’a izuwa can, mabiyansa suka sha ruwa a tafkin kwatto sannan suka yi kabbara sau uku, suka afkawa Rundunar gobir da yaki.
Koda rundunar Sarki Yumfa taga haka, sai suma suka suka bugi tamburansu, sannan suka ce dawa aka hadamu ba daku ba, suka nufarwa mabiya shehu Usmanu da gudu makamai a zare. Kafin kace haka wani sabon yakin ya sake karkewa.
A lokacin kuwa, sai da aka yiwa Mabiya Shehu Usmanu dan fodio kawanya, dakaru dama da hagu, an sanya su a tsakiya, gashi kuma yakinsu yafi ga harbi, tunda dawakansu ance basufi ashirin ba. Su kuwa mabiya sarkin gobir dawakansu basa misaltuwa.
Amma dai cikin ikon Allah, sai Allah ya warwatsa rundunar Sarki Yumfa tayi dai-dai.
Sarkin da kansa yahau ingarman dokinsa ya arce zuwa garinsa, ya bar jama’arsa karkashin takubban mabiya shehu Usmanu, ya bar takalminsa da gadonsa na sarauta, da tamburansa da takobinsa da kayan goro da guzurinsa na alkaki da irinsu.
Wani mawaki yayi baitin waka akan haka da cewa:-
Yayi jifa da takardu dan Sassabtama taguwarsa.
Da guzurinsa, har ma da ‘yar sanda tai.
A haka mutanen shehu Usmanu suka rabauta da gagarumar ganima a wannan waje.
A cikin wannan shekara ta daya dayin Hijirar Shehu Usmanu dan fodio, akayi yakin Mane.
Sannan a shekarar ne Shehu Usmanu ya dauki tawagarsa izuwa Magabci, koda yake wasu sun ruwaito cewar kafin yabar yankin, sai da sukayi kokarin karde iko da Alkalawa babban birnin gobir, amma basu samu ikon haka ba, ga kuma yunwa ta damesu, don haka suka bar yankin.
Acan magabci Shehu Usmanu ya rubutawa sarakunan Kasar Hausa takardu yana mai sanar musu dalilinsa na yin yaki da sarkin Gobir, tare da neman hadin kansu da tallafinsu wajen yaki don tabbatar da Musulunci bisa turbar gaskiya da kuma kawar da bidi’o’i.
Sa’ar da Sarkin Katsina ya samu wannan takarda, sai ya keta ta. Yayi magana ta batanci ga shehu da magoya bayansa.
Sa’ar da Sarkin Kano kuma ya samu wannan takarda, sai bai keta taba, amma kuma bai amshi kiran shehu Usmanu ba.
Amma sarkin Zazzau dana Rumo duk sun karki kira, sai dai kuma jama’arsu sun bijire a kaiwa shehu tallafi.
Shehu Usmanu dan fodio ya baro Magabci izuwa sifawa, sannan ya tashi izuwa Barkiya, sai kuma ya karasa Sokoto.
Daga nan suka nufi Dangeda, suka karasa Godewa duk suna yin yaki tare da samun ganima mai yawa, sannan suka isa Makada, sai kuma suka tashi izuwa Kirare.
A kirare suka hadu da wasu jama’ar Katsina da sukayi hijira daga katsina izuwa garesu bayan sunsha matsananciyar wahalar tafiya cikin dazuka. Ance a kalla kwanaki talatin suka shafe suna tafiya daga katsina izuwa wannan wuri.
Daga nan kuwa, sai shehu da jama’arsa suka tashi izuwa wani wuri mai suna Tsuntsuwa.

Cigaba a makon gobe in sha Allah.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: