Connect with us

TATTAUNAWA

Yan Takaran Wasu Jam’iyyu Da Ba APC Da Suke Hada Hotonansu Da Na Buhari Mayaudara Ne, Inji Kwamared Sabo

Published

on

KWAMARED SABO MUHAMMAD Shine dan takarar da APC ta baiwa tuta da zai fito mata a zaben 2019 neman kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bauchi. A hirarsa da KHALID IDRIS DOYA ya shaida cewar alkarsa da shugaban kasa Buhari za ta bashi damar da zai tafi majalisa domin taimaka wa kudurorin Buhari, ya kuma shaida cewar ilimi da amana ce ja gaban dalewa kujerar majalisar tarayya, a cikin hirar ya bayyana cewar ya fi kowani dan takarar da ke neman wannan kujerar dacewa ga hirar:

Ka gabatar mana da kanka?
Sunana Kwamared Sabo Muhammad dan takarar dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bauchi a jam’iyyar APC.

A wacce kaba ake kan neman wannan kujerar?
Daidai gwargwado muna nan muna shiga cikin karamar hukumar Bauchi muna magana da mutane maza da mata, dattabai da sauran masu ruwa da tsaki a cikin karamar hukumarmu ta Bauchi, kuma kasancewar ni ba sabon shiga ba ne kan neman takarar dan majalisar tarayya domin nine na yi wa tsohowar jam’iyyar ANPP takara a shekarar 2011 kuma a 2015 ma na nema wanda yanzu haka wanda yake kai ya kadani da wasu ‘yan kuri’u kalilan da basu gaza 15 ba, don haka ya zuwa yanzu muna nan muna ci gaba da sa’ayin neman sa’a a zaben da ke tafe.

Ba ka razana da shirin abokan takaranka ba ganin cewar akwai wanda fitilarsa kamar tana haskawa a cikin karamar hukumar Bauchi?
Kana manta karamar hukumar Bauchi ne, karamar hukumace fa ta Firaminista Abubakar Tafawa Balewa, ta Marigayi Malam Sa’adu Zungur, karamar hukumace da ta yi fitattun mutane irin su marigayi Alhaji Adamu Tafawa Balewa da Dakta Ibrahim Tahir, idan ka duba tarihin Bauchi za ka gane cewar zaben nan da ke tafe bai yi zafi ba idan ka duba zaben 2007 ka duba na 2011 ka duba na 2015, mene ne ya sanya haka shine jama’an Bauchi suna saurin banbance abu mai kyau da marar kyau, da abu mai inganci da marar inganci, da kuma yadda jama’a suke kara fahimtar aikace-aikacen ‘yan majalisu da irin mutanen da ya dace su tura kan kujerunsu. Don haka ina ganin ma zaben 2019 zabe ne da za a yi mai sauki wanda zai nuna haske da dubu jama’a su fayyace, a tsakanin dacewa da rashin dacewa, don haka na tabbatar ina da nagartar da jama’a za su zabe ni.

Wani abu da jama’a suke cewa, akwai daya daga cikin ‘yan takarar kujerar da kake nema, ka fi shi ilimi amma ya fika alkairi da mika ribar demokradiyya ga jama’a don haka da iyuwar su zabi mai basu, me za ka ce kan wannan?
To alherin ma ai dubawa za ka yi ka yi nazarinsa sosai. Na gode wa Allah da har jama’an karamar hukumar suka shaidi ina da ilimin da zan iya wakiltarsu a majalisar tarayya, na kuma gode da aka gamsu inda kwarewa da amana da mutunta mutane. Shi alheri da kake gani kowa da yadda yake yinsa, abu na farko dai jama’a ya kamata su gane akwai fa aike (sakon) da za a baka ka kai a madadin wani, da kuma kyautar da za ka yi a madadinka (kashin kanka). Misali, dukkanin wani dan majalisar jiha idan ka ga ya bayar da wani abu indai a wannan gwamnatin yake kashi biyu bisa uku na gwamna ne, kuma yanzu abun da za ka tambayi jama’an daga lokacin da suka bar jam’iyyar nan ta APC ma waye suka yi alkairi tun bayan barinsu cikin jam’iyyar? Muna da labarin ma yanzu kusan tafiyar takararsu din ma ya gagara iyuwa a sakamakon rashin abubuwa, kamar yadda a da baya suke samu a jikin wannan bawan Allah da suke son su tozarta a yanzu shine Muhammad Abdullahi Abubakar wanda cikin ikon Allah shi ne ya basu dukkanin wani zarafi da za ka fada. tun da kafin su samu wadannan mukaman ba wai sun fi mu da wani abu bane, ba kuma sun fi mu rufin asirin cancan ba, akwai banbancin a aikeka ko kuma ka yi aiki da dukiyar gwamnati ka ce kaine ka samar. Abun da yake bani yakinin jama’a sun gamsu da tafiyata na jima ina bauta wa mutane wajen ilimantar da yara da kuma tallafa wa yara kan harkar ilimi wannan ko makiniya zai fada maka babu na biyuna a cikin karamar hukumar Bauchi a wannan harkar da muke na takarar dan majalisar tarayya. Ina sake samun kwanciyar hankali na ga na shiga cikin kauyuka na tarar daga wanda na koyar ya zama wani abu ne sai wadanda na koyar suka zama mutanen kwarai, yanzu abun alfahari ne a gareni ina da wadanda na taimaka musu suka yi karatu mai zurfi har da masu digiri na uku. kuma wani salo na yaudara da wasu ke yi wa jama’a, sai ka ga wani ko wasu ba ‘yan APC ba ne amma sai su hada hotunansu da na Buhari suna tallata wata jam’iyya, yaudarace kawai suke yi, idan za ka so Buhari ka zo jam’iyyar da yake, ni da yake masoyin Buhari na hakika ne ai na fada maka mun yi ANPP da shi wanda a lokacin nine Darakta yada labarai na jam’iyyar.

Wani tabbaci za ka baiwa jama’an karamar hukumar Bauchi da in ka tsunduma kafarka a Abuja ba za ka yaudaresu ba?
Da farko dai jama’a sun yarda da cewa ni ina da alaka da Janar Muhammadu Buhari domin muna tare da shi a jam’iyyar ANPP a lokacin da nake Daraktan yada labarai na jam’iyyar, babban abun da yanzu jama’a suke da imani shine dan jam’iyyar APC ne kawai zai goyi bayan Janar Buhari, mu kuma a cikin APC dai mu wasu abu ne da mu aka kafata, da muka aka yi gwagwarmayarta duk wanda ya sanmu ya san mu da akidar Janar Buhari. Don haka ina tabbatar ma wadanda za su zabeni akidar da Buhari yake a kai na ‘yanta talata da yaki da cin hanci da rashawa za mu dafa sosai kan hakan, ka ga batun cin hanci da rashawar nan yanzu haka wasu ‘yan takarkarun suna can suna ta yawon zuwa kotuna daga ana zarginsu da cin amana sai ana zarginsu da zamba cikin aminci, abun kunya ne a ga dan takararka yana zuwa kotu kan zargin rashin gaskiya.
Sannan idan na je majalisa ba zan taba dum ba tare da kare hakkin mazabata ba, mu tabbatar mutumcinmu da bukatun ‘yankunmu da muka fito za mu tabbatar da samarwa, dukkanin wani hakkin da ya kasance namu ne zamu tabbatar da karbo wa jama’an mazabar karamar hukumar Bauchi. Don haka lallai mu zamu je majalisa ne mu yi aiki wa talaka mu gabatar da kudurorin da zasu taimaki talawa da samar masa da ababen more rayuwa.

Ta yaya zaka tsamo kanka daga dangi domin jama’an Bauchi suna cewa sak ta kare?
Ko cancantar za a bi kowa ya san waye ya cancanta ai, mene ne mizali na cancantar? Na farko dai ilimi na biyu gogewa da kwarewa a aikin gwamnati na uku kasan cikin karamar hukumar Bauchi dukkanin ‘yan takarar da suke neman wannan kujerar je ka tambayi talakawa waye ya fi za ka ji ana cewa Kwamared Sabo ne ya fi kowa a cikinsu.

PDP na neman wannan kujerar shin za ka yi nasara kuwa?
Ai jama’a sun dawo daga rakiyar PDP a jihar Bauchi dukkanin matakai da suka dace na yin zaben cancanta APC ne ta dace kuma jama’a sun san da hakan. Ka duba jam’iyyar PRP mana mafiya yawan ‘yan takararsu daga APC suka fita wanda zai nuna maka su fusatattu ne ko mutanen da dai mun yi mulki dole, dukkanin wani zagin da suke yi wa APC da su akaa yi, idan an yi mai kyau a APC da su, idan marar kyau ne ma da su. Don haka muna ganin alamar nasara da yardar Allah ni zan yi nasara a wannan kujerar ta majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Bauchi a zaben 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: