Connect with us

ADABI

Asadul Muluuk (27)

Published

on

Kashegari da yamma Asadulmuluuk ya sa aka kirawo masa Zuhairu ya ke ba shi labari cewa, shi fa baya jin dadin jikinsa, Zuhairu ya ce; “Haba ranka ya dade yaya za ka zauna cikin rashin jin dadi ga Gimbiya a kusa da kai?” Asadulmuluuk ya ce; “Gimbiyarku ta sanya min ciwon da har na koma ga mahaliccina ba zai warke ba, kuma ta yi biris da al’amarina.

Ba na nadamar sonta kuma har abada ba zan yi ba, saboda a kanta na fara son ‘ya mace a rayuwata, sannan kuma na fahimci tana da nutsuwa da kan gado, amma ina mamaki yadda na dauki sonta a raina da yadda na bayyana mata, kuma ta ke nuna min halin ko in kula.

Ashe kenan wannan wani haske ne da yake alamta min cewa ‘yan matan kasar nan zuciyarsu cike take da yaudara da nufaka?”

Zuhairu ya ce; “Ranka ya dade ai ba haka abin yake ba, ni dai na yi imanin tana kaunarka fiye da yadda kake kaunar ta, kawai dai ina zaton wani lamarin ne daban ya sha mata kai a cikin gida, don haka ka ke ganin banbanci.”

“Haba Zuhairu ban yi niyyar shiga gidan don wani abu ba sai don ita, amma da ta samu labarin na je, sai dauki wasu tufafi ta sanya, wanda hakan shi ya alamta min ba ta yi na’am da zuwana ba. Mu a kasar mu duk irin tufafin da mutum ya sa ya fito sai an fahimci abin da kwalliyarsa take nufi, in har wani abu ya faru.

Tufafin da Uwargiyarku ta sanya yana nuni da cin fuska ga bakon da ya zo musu a wannan lokaci, wanda ya kai matsayin da har Umma babba ta yi mata magana a kan hakan. Shi so ya kan riski mutum sa’i guda, amma fitarsa sai an yi da gaske, tun da shi baya kwankwasa kofa ballantana ka yi masa tanadi. Idan ka ji ana maganar cire so a zuciya to wannan zuciya lamarinta ya muguzta.” In ji Asadulmuluuk.

Zuhairu ya ce; “Ka ga kuwa a zuwan da na yi jiya labari na zo in baka cewa na ji an ce ranar Juma’ar gobe gimbiya za ta ziyarci babban lambu, lambun da ya ke hade gamayyar samari da ‘yan Mata, wanda na baka labari a farkon marra, cewa ita ba ta son zuwa. Kuma wannan shi ne karo na farko da za ta halarci wannan lambu.”

Asadulmuluuk ya gyara zama ya ce; “Ashe maganar da ka ce Umman ta ce ba ta son zuwan ta wurin ya zama zancen kawai.” “Ba haka ba ne, ranka ya dade ai wannan wani lamari ne da ya yi kama da sakin fuska da ta samu a karo na farko daga mahaifiyarta, ni kuma ina ganin yin haka kamar sabawa shari’a ne a ce budurwa na zuwa wani wuri da ake cudanya maza da mata, hakan zai zama kamar ana talla da ita ne, to amma da yake ya zama al’adarsu ba za a kalli lamarin ta fuskar yadda na fahimce shi ba.

A daya bangaren kuma ana alakanta zuwanta lambun da cewa ta samu mijin aure don haka ta samu wannan ‘yanci.” In ji Zuhairu. Idanun Asadulmuluuk ya yi yawur jijyoyin jikin sa suka fito rada-rada, gashin jikin sa ya tashi. Ganin haka Zuhairu ya razana sosai, ya ce; “Ranka ya dade Allah ya huci zuciyar ka,”  Asadulmuluuk ya ce, “Baka yi min laifi ba, kuma kada ka yi la’akari da abin da ka gani a jikina, haka nan Allah ya yi ni, a duk sa’adda wani al’amari ya sha min kai hakan ce take alamta wa jama’ar mu bana cikin kyawun yanayi.

Ba kasafai na kan ziyarci irin wadannan wurare ba, amma idan Allah ya kai mu ranar za mu je tare da kai ko da ba za mu hadu da ita ba, kuma ba zan je muhallin da za ta san mun zo ba.” In ji Asadulmuluuk.

Da suka gama hirarsu Zuhairu ya shiga cikin gida ya samu Ummu Nazifah ya ba ta labarin abin da ya faru, sannan ya ce; “Idan Allah ya kai mu ranar Juma’a su fito kawai kada su yi fargabar komai.”

Ranar Juma’a La’asar sakaliya aka fito da Taguwa aka shirya Darbuka fara a kai, aka kawata ta, ta daga nesa idan ka hangota kai ka ce wani kunshin zinare ne abin taskacewa, shi kansa Asadulmuluuk da ya fito ya ga yadda aka kawata Darbukar, sai ya yi ta ta’ajibin lamarin. Sai ya jiyo sautin wata irin busa da bai taba jin busa mai dadinta ba, ya tambayi Zuhairu wannan wace irin busa ce, wa ake yi wa, kuma waye gwanin iya busa haka?” Zuhairu ya ce; “Ranka ya dade ai wani matashi ne da aka dauko shi daga kasar Sin shi ne ya ke wannan busa, kuma duk karshen makonni biyu a kan biya shi zambar dinare ridili goma, ka ga kuma ba ta fitowa sai bayan shekara guda. Amma duk da haka ya na nan ana biyansa ko da babu in da za ta fita, sannan duk kasar nan da kewayenta babu in da za ka je ka ji irin wannan busa, ka ga yau za ta fita kuma babu wanda ya san da fitar, kai lallai yau za mu yi kallon kwalliya, yau za ka ga taron da yafi taron Sarki in za shi ran gadi, don ko shi Sarki ba irin wannan busar a ke yi masa ba.” Yana gama kalamansa kawai sai suka ji wani irin kamshi ya feso, kai ka ce suna cikin gonar almiski ce, Asadulmuluuk ya ja da baya ya koma masaukinsa.

Can sai ya jiyo karar kayan karau na kwalliya caras-carasss, ta na tafe suna hira da Ummu Nazifah, amma babu wanda ya ke jin abin da suke fada, saboda ko ina na jikinta a rufe yake, ba ka iya ganin komai sai kyalkyalin kwalliya.

Suna cikin wannan hali ne take tambayar Ummu Nazifah cewa; “Yalla ko za ki iya yi min ishara ga in da Yarima yake zama?” “La la! ranki ya dade ai ba mu fito don mu nuna masa hakan ba, mun fito ne mu nuna mu ma mata ne da ya zama wajibi maza su bi mu, ki bar wanga batu za mu wuce idan yana yi zai biyo mu.”

Shi kuwa Asadulmuluuk yadda ya ke jin karar kayan kwalliyarta haka nan zuciyarsa ke bugawa ba adadi, ya hange ta tagar dakinsa ya ga wucewarta kamar kunshin zinare. Mai busa ya sauya salon busa, kafin wasu ‘yan dakikoki kofar gidan Sarki ta cika makil da jama’a, kowa yana mamakin yadda ya ji busar da baya jinta sai ranar Sallah babba. Sai kirari ka ke ji kowa da irin na sa, aka dotara a kan Taguwa cikin Darbuka, akwai dawaki guda shida farare a gaban taguwarta, daga gefenta na dama kuma an jera guda shida bakake gefen hagu kuwa an jera shida masu launin danda, daga bayan ta kuma an jera guda shida suma farare.

Haka aka fito masu yi mata hidima ‘yan majalisarta daga mata sune bisa kan dawaki na gaba da na gefenta, na bayanta kuma duk bayi ne maza dauke da kayan abin da za ta sha don nishadi.

An dauko dawisunta bisa wani doki da ban dan ya dinga yawo a gabanta tana jin dadi, har aka isa muhallin da za su zauna. Wani wuri ne aka ware an girke wata karaga ta danayar ciyawa koriya mai laushi kai ka ce wata Atafa ce abar sanyawa cikin wata rumfa. Nan ne inda Gimbiya Badee’atulkhairi za ta zauna, haba ai kafin su karaso wuri fa ya sake cika makil da jama’a, wanda bai yi niyyar zuwa ba ma ya zo don ya ganewa idanunsa wannan ‘yar Sarki wadda a da sai dai su ji labarinta.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!