Connect with us

SIYASA

Ni Na Tura Mutum 2,000 Zuwa Kamfen Din Buhari A Ebonyi -Gwamna Umahi

Published

on

Gwamnan Jihar Ebonyi, Dabid Umahi, ya ce shi ya tura mutane 2000 domin su halarci taron yakin neman zabe na shugaba Buhari, a Jihar, domin ba ya son shugaban kasan ya ji cewa, mutanan Jihar da kuma yankin na su ba sa kaunar sa.
Kamar yanda jaridar, Daily Sun, ta nuna, Umahi ya fadi hakan ne jim kadan da wucewar Shugaban kasan.
Ya ce, ba kawai ma ya baiwa Jam’iyyar ta APC daman yin amfani da filin taron ne ba kadai, ya ma gyara masu shi ne, kuma idan ba cewa ya tura mutane filin taron ba, to kuwa da shugaban kasan ya tarar da filin taron babu kowa a cikinsa.
“Mutanan da ka gani a wajen taron nan, 2000 daga cikin su ni ne na tura su, saboda na san APC ba su da kowa a nan Jihar Ebonyi.”
“Domin ba na son Shugaban kasa ya dauka cewa mutanan Ebonyi ba sa kaunarsa, shi ya sanya na tura mutane 2000 domin su yi maraba da shugaban kasan.
“Shi ya sanya, in ka kalli taron mutanan a lokacin da su shugabannin APC din suke ta suka ta ba gaira ba sabar, sam mutanan ba sa tafa masu, domin mutanan ba sa jin dadin hakan. Amma saboda kadai, su girmama shugaban kasa ne suka yi masu shiru kadai, amma da ihu za su yi masu.”
“Muna goya masa baya ne, wannan kuma shi ne goya masa bayan da muke yi. Mun bayyana wa Duniya abin da shugaban kasan ya yi mana a Jihar Ebonyi, wannan kuma shi ne goyon bayanmu a gare shi.
“A bisa dabi’a da kuma ka’ida, bai kamata na fito ina ihun ku zabi APC ba, alhalin ina rike ne da katin shaidar Jam’iyyar PDP.
“Amma akwai hanyoyin masu yawa da zan iya ba da goyon baya na, a matsayina na shugaban kungiyar gwamnonin sashen kudu maso gabas, mun yi wa shugaban kasan tarban da ya dace da shi a shiyyar namu ta kudu maso gabas, tabbas kuma hakan zai kara masa yawan kuri’u a bisa wanda ya samu a baya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: