Connect with us

MAKALAR YAU

Kaddara A Falsafar Musulunci (l)

Published

on

Wanda ya fara karatu zai dauka addininmu ne ya fitar da siyasarmu da akidojinmu. Wanda ya yi nisa a karatu zai gane siyasarmu ita ta fitar da addininmu da akidojinmu. Kusan kaso 80 cikin 100 na duk wani abu da muke aikatawa ko muka kudurce a cikin addininmu yana hade da siyasar rigingimun farko da aka yi a Musulunci bayan wafatin Manzon Allah (saw).
Sheikh Nasirudden Albany a littafinsa “Sahiha” ya inganta hadisin cewa farkon wanda zai canja sunnah wani mutum ne daga Banu Umayya. Dayawan malamai sun ce Mu’awiya bn Abi Sufyan ne da ya canja salon halifanci ya koma mulkin gado. Amma ba na zaton iya wannan ya canja. Siyasar Banu Umayya da sauran wadanda suka biyosu ta shiga kowane sako na cikin imaninmu da ibadunmu. Har shika-shikan Musuluncinmu akwai rigingimun da suka shiga ciki. A nan ina magana akan Musulunci da kungiyoyinsa baki daya ba wai kungiyar Ahlussunnah kawai ba.
Dayawa mutane suna dauka shika-shikan imani tamkar Manzon Allah zama ya yi ya dinga jero su don kowa ya kudurce. Duk da akwai hadisai masu nuna haka a litattafan sunnah amma wannan babban kuskure ne idan muka duba tsarin kowace kungiya. Hakikokin tarihi basu nuna Manzon Allah zama ya yi da sahabbai yana gaya musu shika-shikan imani su kuma suna haddacewa ba. Sai bayan wafatinsa sannan kowace kungiya ta dinga hada shika-shikan imaninta daidai yadda take so. Don haka ginshikan Mu’utazila suka banbanta da na Shi’a, na Ahlussunnah suka banbanta da na Khawarij, da sauransu.
Tamkar halin kowane babban mutum a tsawon tarihi da bai rubuta littafi ya ajiye kan shika-shikan abin da ya zo da shi ba, tamkar Socrates ko Jesus Christ, haka halin Manzon Allah (saw) ya kasance. Magoya bayansa su suka dinga zuwa cikin maganganunsa da tarihinsa suna diban abin da ya dace da abin da suke so sai su kafa kungiyoyinsu da shi. Kada ka manta da abin da masana halayyar dan Adam suke kira da “Confirmation bias”. Mutane sun fi lura su dauko abin da zai karfafa son ransu komai rauninsa amma su kyale wanda ba sa so duk karfin hujjarsa.
Bayan mutuwar Socrates dalibinsa Plato shi ne ya rubuta maganganunsa da falsafarsa. To amma akwai shakku sosai akan cewa tabbas Plato ya debo abubuwan da ya yi masa ne kawai daga maganganun Socrates amma ba duka falsafarsa ba. Misalan rayuwar Socrates da Plato sun tabbatar da haka. Socrates bai yarda da tsarin makaranta na koyarwa ba amma Plato har gina makaranta ya yi! Socrates yana umartar mutanen Athens su yi aure don su dena al’adarsu ta neman maza amma shi Plato ana zarginsa da neman mazan kuma bai aure ba! Socrates ya fi son hada kansa da marasa galihu, bayi da talakawa shi kam Plato yayan masu kudi da sarauta ya dinga koyarwa!
Haka tarihin Jesus ya kasance. Rayuwarsa ta gwagwarmaya ta banbanta da rayuwar Kiristoci daga baya. Abubuwan da ya dinga fadi na nuna cewa shi dan juyin-juya-hali ne sun banbanta da abubuwan da almajiransa suka canja daga baya saboda tsoron kada a kashesu. Tarihin Jesus ya nuna cewa mutum ne da baya tsoron kowa akan fadin gaskiya kuma ba ya tare da sarakuna. Abin da su St. Matthew da St. Paul suka rubuta a matsayin ginshikan kiristanci kuwa ya saba baki daya da abin da Jesus Christ ya yi a rayuwarsa ta gwagwarmayar da ta kai da sarakuna suna nemansa don kasheshi.
Haka tarihin Manzon Allah (saw) ya nuna. Alkur’ani kawai Manzon Allah ya bari kuma wasu hadisan sun nuna har hana rubuta maganganunsa ya yi. Daga baya aka samu kungiyoyin addini kowa yana son ya kare matsayarsa amma yana son ya nuna cewa Annabi ya kwaikwayo, don haka aka dinga kirkirar karairayi ana cewa Manzon Allah ne ya fada. Don haka zaka ga hadisan Shi’a da ban da na Sunnah saboda kowa yana kirkirar hadisai daidai son ransa ne. Sunnah su ne suka fara daga baya Shi’a suka mayar da martani da na su hadisan.
Wanda ya karanta tarihin sauran sahabbai da na Abu Huraira zai sha mamaki! Abu Huraira ya zauna da Annabi kasa da shekara uku amma ya fi wadanda suka zauna da shi sama da shekara ashirin yawan hadisai! Wannan ba ni kadai ya bawa mamaki ba, har sahabbai da tabi’an da suke zamaninsa sun musa yawaitar hadisan da yake rawaitowa. A wani lokacin ya kan ce mutane ne suka dauka maganganunsa na kansa hadisai ne. Wani lokacin kuma yana cewa labaran Isra’eliyyat din da ya samo daga Ka’abul Ahbar ne idan ya bawa almajiransa sai su dauka cewa ya yi Manzon Allah ne ya fada!
A haka fa, da irin wadannan hadisan, muka samo imani da kaddara ya zama daya daga cikin shika-shikan imaninmu! Siyasar Mu’awiya ce ta janyo kungiyar “Jabariyya” masu cewa kowane dan Adam sai ya yi imani cewa komai Allah ne ya kaddara masa ba shi da wani zabi a rayuwa! Har sai da ya zamo kungiyoyin Mu’utazila na farko kamar Kadariyya (su ne masu cewa dan Adam yana da zabin aikata komai) sun dinga shan wahala har da kisa a hannun Banu Umayya saboda basu yarda da wannan “ginshikin imani” ba. A haka aka kashe Giylan Addimashkiy da sauransu.
A gurin Sufaye da irin wadanda suka dauki falsafarsu kamar Baruch Spinoza, mutum tamkar digo ne na dabi’a (nature) mai girman gaske. Ita kam dabi’a ta samo asalinta daga Ubangiji (God) ne ko kuma babbar Dabi’a (Nature). Lokacin da ka hada dabi’a (nature) da Dabi’a (Nature) sai a ce ka yi “Pantheism” amma lokacin da ka ce dukan dabi’a tana komawa ga Dabi’a ne to sai a kira hakan da “monism”.
Kasa banbance irin wadannan yana janyo cakuda “Pantheism” ko “Monism” da “Wahdatul-Wujud”. Akwai siririyar hanya tsakanin ibarorin da sai mai duba na tsanaki ne kan iya banbancewa. Don haka mafi yawan wadanda basu fahimta ba suke zurmewa saboda falsafa ce mai zurfi da fahimtarta sai an nutsu sosai.
Sabanin Baruch Spinoza da yake ganin mutum ba shi da wani yanci saboda duk abin da zai yi a matsayinsa na digon dabi’a (nature) sai babbar Dabi’a (Nature) ta ba shi dama, su a gurin sufaye suna ganin dan Adam yana da yanci tamkar yadda dabi’a take da shi. Ka lura, a gurin Sufaye kalmar “Nature” (da babban baki) tana nufin “God”.
Spinoza na ganin cewa babu wanda ya isa ya kufcewa tsarin dabi’a (determinism) saboda mutum, tamkar sauran dabbobi, yana kan tsarin abin da ya kira a falsafarsa da “thought and edtension” ne. Mutum tamkar “thought” ne da ya fito daga “edtension” na dabi’a. Sai abin da dabi’a ta tsara masa shi zai iya yi.
Ibnul Arabi (rh) shi yana ganin cewa duk da mutum digo ne daga Dabi’a amma yana da yanci (freewill). Tajallin Ubangiji (Nature) akan mutum da kuma busa masa ruhi (soul) da ya yi shi ne ya janyo yake da wannan yancin. Ubangiji ya busawa Annabi Adamu ruhinsa da ya bashi damar daukaka sama da mala’iku ta fifikon sani da kuma yancin zabi. Don haka tun da mu yayan Adamu ne to muma muna da wannan dosanon ruhin da ya bamu damar yancin zabi.
Ibnul Arabi, musamman a littafinsa “Fususul Hikam”, bai manta cewa akwai taisirin dokokin dabi’a a rayuwar dan Adam ba don ya san cewa babu wanda zai iya sabawa dokokin dabi’a. Yana maganar cewa Dabi’a ta tsarawa dan Adam yancin ne ta hanyar ruhin da ta busa masa. Shi yana magana akan ruhi ne (soul) ba wai jiki ba (body).
Sai dai ma’anar yanci (hurriyya) a gurin Ibnul Arabi ba ta nufin mutum ya dinga aikata duk abin da yake so! Ma’anar yanci a gurinsa na nufin ka sallamawa Dabi’a (Ubangiji) ta yi tasarrufi da kai. Kokarin kaucewa abin da Ubangiji ya tsara maka shi ne zai zama karin hijabi tskaninka da Ubangiji.
Da irin wannan fahimtar Sufaye suka fahimci ma’anar “kaddara”. Idan har mutum ya fara gane iya ina ne matsayarsa ta yanci to zai gane ina ne kuma kaddara za ta iya juya shi. Sai dai kada a manta Sufaye suna da ma’anoninsu na daban ba na malaman Tauhidi ko “ilmul Kalam” ba. Cikakken bayani akan Falsafar kaddara da yancin zabi an fi samunsa a gurin Mu’utazila da Ash’ariyya. Su yan Salafiyya da ma wani tsagi ne na Jabariyya a zamanance.
Akwai ci gaba Insha’Allah
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: