Connect with us

KASUWANCI

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Hasashen IMF A Kan Tattalin Arzikin Kasa

Published

on

Ministan Kasafin Kuidi da Tsare-tsaren kasa Sanata Udo Udoma, ya mayarwa da Bankin Bayar da Lamuni na Duniya IMF akan cewar da ya yi tattalin arzikjin Nijeriya zai karu da kashi 3.01 bisa dari a cikin wannan shekarar, idan aka kwatanta da kirdadon kashi biyu bisa dari da Bankin. Bankin na IMF ya sanar da hakan ne a cikin rahoton sa da ya fitar akan tattalin arzikin duniya da ya sabunta, inda Bankin na IMF ya ce, a cikin watan Janairu, tattalin arzikin Nijeriya zai kara fadada wajen yin kasa a cikin shekarar 2019 fiye da a baya sabannin saukar da farashin danyen mai ya yi a duniya. A sboda hakan ne, Bankin ya sanya ya yaja tattalin arzikin Nijeriya baya zuwa kashi biyu bisa dari daga kashi 2.3 bisa dari da Bankin ya yi kirdadon a cikin watan Okutobar shekarar 2018.
Sanata Udo Udoma ya ce, kasafin kudin shekarar 2019 anyi kasafin ne da nufin daidai tattalin arzikin Nijeriya don a dora shi akan turbar data dace da kuma rage radaddian talauci a tsakinin yan Nijeriya. Sanata Udo Udoma ya mayar da maratnin ne a jawabin sa a taron da aka gudanar akan tattalin arzikin kasar nan na shekarar 2019 da aka gudanar a jihar Legas. Kafar yada labarai ta TheCable, inda Sanata Udo Udoma ya yi nuni da cewar, hauhauwan farashi ana sa ran zai ragu da kashi 9.98 bisa dari a shekarar 2019 daga kashi 11.44 bisa dari a cikin watan Disambar shekarar 2018.
Ministan ya kara da cewa, hakan zai iya yuwa saboda samun ci gaba da akayi a tsare-tsren kudi da karin ci gaban da aka samu wajen fitar da mai zuwa waje da samun kudin shiga da kuma daidai asusun ajiya na kudin musaya na kasar waje da Babban Bankin Nijiya CBN ya samu nasara yi. Acewar sa, Gwmatin Tarayya tana yin iya kokarin ta akan ciyar da tatalin arzikin Nijeriya gaba kuma tana kan ci gaba wajen baiwa tattalin arzikin kasar taimakon da ya dace. Sai dai, Sanata Udo Udoma ya yi nuni da cewar, akwai alamun tattalin arzikin Nijeiya a yanzu yana dan yin tafiyar Hawainiya, musamnan ganin cewar, Nijriya bata jima da ficewa daga cikin matsin tattalin arzikin kasa ba kuma akwai alamun samun ci gaba, musamman a fannin da bai shafi man fetur ba. Ministan ya ce, “ burin mu shine, mu dauki matakai don tabbatar da kara ciyar da tattalin arzikin Nijeriya gaba.” Da yake tsokaci akan kirdadon farashin mai da aka sanya a cikin kasafin kudi, Sanata Udo Udoma ya ce, farshin mai zai tabbatar da hudda a tsakain fitarwa da kuma bukata akan mai na kasuwannin duniya. Sanata Udo Udoma ya ce, samarwar ce dalilin da ya sanya aka samu karin farshin mai a shekarar 2018 a ragin da aka samu a baya.Shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya umarci kamfanin NNPC da ya yi aiki tukuru don cimma burin kasafin kudi na samar da gangunan dayne mai miliyan 2.3 a kullum. Sarrafa danyen mai na ERGP da ake son samu a shekara 2019 zai kai 2.4mbpd kuma kamfanin NNPC zai sarrafa 2.45mbpd. Acewar Sanata Udo Udoma, mun sabunta ERGP da kuma kirdadon da akayi na NNPC zuwa 2.3mbpd a a cikin kasafin kudin na shekarar 2019.
Acewar Sanata Udo Udoma, abinda akayi kirdadon a cikin kasafin kudin na shekarar 2019 ya yi kadan dana shekarar 2018 saboda bukatar da ake da ita na kula da gibiwajen ciwo bashi. Ya ce, gibin na naira tiriliyan 1.859 na shekarar 2019 ya kai kimanin kashi 1.33 bisa dari na tattalin arzikin kasa wanda ya kai kashi uku bisa dari kamar yadda dokar (FRA) ta shekarar 2007 ta gindaya. Sanata Udo Udoma, Gwmanatin Tarayya za ta tallafa wa masanaantu masu zaman kansu don su samu su ci gaba da gudanar da ayyukan su yadda ya da kuma ciyar da tattalin arzikin kasar nan gaba da samar masu da sukunin gudanar da kasuwancin. Sanata Udo Udoma a karashe ya ce, zamuci gaba da mayar da hankali don kawar da dukkan mastalolin don a samarwa da masau masana’antu yanayin kasuwanci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!