Connect with us

KASUWANCI

Hukumar NSE Ta Ci Tarar Kamfanoni 38 Tarar Naira Miliyan 429.5 A Kan Rashin Bin Ka’idar Aiki

Published

on

Hukumar NSE ta kasa ta ci kamfanoni guda 38 tarar jimlar naira miliyan 429.5 saboda bin bin ka’idar aiki ta gudanar da hada-hadar kudin takardun su. A bisa bayanan da aka samo daga NSE sun Nina cewar, kamfanoni 38 aka ci tatar akan laifukka da ban-da-ban har guda 52. Kamfanonin sune, bankin Unity Plc, FTN Cocoa Processors Plc, Academy Press Plc, Union Dicon Salt Plc da kuma Standard Alliance Insurance Plc. Bankin Unity shi ne tararar da tadi yawa Inda ta kai ta naira miliyan 79.7, said kamfanin FTN Cocoa Processors anci shi tarar naira miliyan 78.7. Bankin Unity da FTN Cocoa Processors anci su tara saboda gazawa tantance takardun hada-hadar su ta shekarar 2017 a farkon zangon shekarar 2018 da kuma a rabin shekarar 2018 da zango na uku na shekarar 2018. Kamfanin Academy Press anci shi tarar naira miliyan 35 saboda gazawar sa na gabatar da takardun sa na tantancewa a shekarar 2017.Kamfanin Union Dicon shine na hudu a jerin cin tarar, Inda akaci shi tarar naira miliyan 30.8 akan gabatar da takardar sa a farkon zango da kuma rabin zangon shekarar 2018. Kamfanin Standard Alliance anci shi tarar naira miliyan 28.7 saboda gazawar san a gabatar da takardun hada-hadar sa a shekarar 2017 da kuma a farkon zangon shekarar 2018.
Rahoton ya ce, kamfanoni biyar an cire sunayen su a shekarar data wuce inda uku kuma Seben-Up Bottling Company Plc, Paints da Coatings Manufacturers Nigeria Plc and Great Nigeria Insurance Plc suka janye na kashin aknsu. Sauran biyu African Paints Nigeria Plc da kuma Afrik Pharmaceuticals Plc, suma an cire su. Shugaban kungiyar CSAN ta kasa Shehu Mikail, ya ce, NSE ta tsaurara da yawa akan takunkumin nata. Shima a nasa bangaren Babban jami’i na NSE, Mista Oscar Onyema, ya ce, a watan da ya gabata hukumar ta rage yawan nauyin dake kan kamfanonin.
Onyema y ace a kwanan baya mun tura masu wasiku akan basu goyon bayan su ci gaba da hudda damu. Shima mataimakin shugaba kungiyar ASHN ta kasa Akinsola Akeredole-Ale, za su ci gaba da basu goyi bayan su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!