Connect with us

MANYAN LABARAI

Kakakin Rundunar Soji Birgediya Kuka Sheka Ya Yi Ritaya  

Published

on

Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, mai Magana da yawon rundunar sojin Nijeriya, ya yi ritaya daga aikin soji, a cikin takardar da Kuka Shekan ya sanya wa hannu, ya ce daga gobe Juma’a zai tafi hutun karshe wanda daga shi zai yi ritaya daga aikin soja.

Kuka Shekan ya mika wa Kanal A.A Yusuf aiki, a matsayin jami’in rikon, kafin rundunar sojin ta nada wanda zai maye gurbin Birgediya Kuka Shekan, Kuka Shekan ya mika godiyarshi a cikin takardar ga duk wadanda suka taimaka mishi wajen gudanar da ayyukansa a cikin rundunar ta sojin Nijeriya.

‘Ina mika godiya ta ga al’ummar Nijeriya, domin damar da na samu wajen yi wa kasa ta aiki na tsawon shekaru 30 da duriya, gashi lokaci ya zo da zan ajiye aiki, bayan duk ilimin da na samu a a fagen wannan aikin, da mu jama’a daban-daban da na samu damar yin aiki ko abokanta da su a fagen aiki na, wannan ba abu bane da zan manta a rayuwata.’ Inji Birgediya Kuka Sheka

Kuka Sheka ne kakakin rundunar sojin Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa 2018 inda ya je ya yi kwas din manyan jami’ai a (NIPSS) da ke garin Kuru, bayan ya kamala kwas din a sake nada shi a matsayin kakakin rundunar sojin Nijeriya a karo na biyu, inda daga nan ne kuma sai ritaya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!