Connect with us

KASUWANCI

Wutar Lantarki Ta Karu Da Kashi 100 A Cikin Shekaru Uku – Fashola

Published

on

Ministan Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola, ya sanar da cewar, wutar lantarki a Nijeriya ta karu da kashi 100 bisa dari a a cikin sehkaru uku da suka wuce. Babatunde ya sanar da hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Wakilan Kungiyar Masana’antyar Gine-Gine FCI a ofishin sa a ranar Litinin da ta gabata a garin Abuja. Babatunde Fashola, ya ce, musamman wutar ta karu daga megawatts 4,000 a shekarar 2015 zuwa megawatts 8, a shekarar 2018. Wannan yasha banban da adadin wutar da aka samo daga kamfanin samar da wutar TCN a ranar Litinin sata gaba. Kamfanin na TCN ya ce, karin na wutar, an same shine a ranar 3 ga watan Fabirairun shekarar 2019, wanda ya kai megawatts 4,976. TCN ya karada cewa, yawan karuwar makamshi ya kai megawatts 557 an kuma samu wannan ne a ranar 2 ga watan Fabirairun shekarar 2016. Acewar TCN, ta samar da megawatts 5,222, inda kamfanin ya kara da cewa, an samu adadin ne a ranar 18 ga watan Disambar shekarar 2017. Sai dai, Babatunde Fashola a cikin sanarwar da ma’aikatar sa ta fitar a ranar Litinin ya shedawa bakin cewar, yan Nijeriya a yanzu suna kashe yan kudi kadan wajen sanya mai a janaretocin su saboda kara samar da wutar da akayi a daukacin fadin kasar nan. Acewar Ministan, gwamnatin ta zage wajen fadada tattalin arzikin kasar nan. Babatunde Fashola ya kara da cewa, ma’aikatar sa, tana kara bayar da dauki wajen kammala shirin samar da gidaje a daukacin fadin jihohin kasar nan kuma gwamnatin tana ci gaba da aiwatar da aikin gina sakatariyar ta tarayya a jihohin Bayelsa, Anambra, Zamfara da Nasarawa. Babatunde Fashola ya shedawa bakin nasa cewar, Gwamnatin Tarayya tana sane da kokarin da kungiyar take yi wajen taimakawa masu fasa duwatsu saboda yawan aikin da ake ci gaba da yi. Acewar Babatunde Fashola, a lokacin da muka hadu da farko akwai korafe-korafe na rashin biya daga shekaru uku zuwa hudu kafin zuwan wannan gwamnatin. Acewar Babatunde Fashola, amma a yanzu ina son in baku tababcin cewar, a yanzu zuwan wannan gwamnatin babu dan kwangilar da gwamnati bata biya ba. Ya kara da cewa, doka ta gwamnati ta 5 ta bukaci yan Nijeriya da kamfanoni masu zaman kansu su shigo, ganin cewar, ma’aikatar sa tuni ta fara tattara sunayen yan Nijeriya da kuma kamfanonin dake cikin kasar nan don gudanar da aikin. Babatunde Fashola ya yi nuni da cewar, Dokar ta gwamnatin tarayya ta 7 da Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya sanyawa hannu, zata tabbatar da kara fadada aikin.Darakta janar na FOCI, wanda ya jagoranci tawagar wakilan Olubunmi Adekoje, ya jinjinawa ma’aiakatar ta wutar lantarki, ayyuka da kuma gidaje a kan daukin da take samarwa kungiyar don ciyar da fannin gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!