Connect with us

MAKALAR YAU

Zaben 2019: Cancanta Ko Son Rai?

Published

on

Masu karatu barkanmu da sake saduwa a wannan makon domin tattauna batutuwa na musamman kamar yadda muka saba. Kasancewar yanzu muna cikin shekarar zabe da za a gudanar a duk fadin Nijeriya ya sanya kacokan wannan shafi zai mayar da hankalinsa kan batutuwan da suka shafi siyasa da sha’anin mulki a wannan kasa.
Kamar yadda wannan shaffi ya saba, wannan karon ma muna tare da wani maudu’I da za mu yi akan abin da ya shafi wannan babban zabe, wanda sau daya yake maimaituwa duk bayan shekara hudu a dukkan fadin Nijeriya.
Don haka yana da kyau al’ummar Nijeriya birni da karkara su bude ido, suun fahimci yadda gaskiya take da kuma yadda lamura suke a zahirinsu. Wannan zabe da za a fara gudanar a watann Fabrairu mai zuwa, kusan za mu iyta cewar zabe ne da za a yi tsakanin karya da gaskiya, zabe ne tsakanin cancanta da son Rai, zabe ne tsakanin masu kishin kasa da gungun barayi macciya amana da satarr dukiyar kasa.
A saboda haka, lokaci ne da ‘yan Nijeriya za su kaucewa duk wasu barayyi maciya mana, masu satar kudin al’umma duk dadin bakinsu da marairaicewa da za su yi, duk wanda aka taba samu da laifin satar dukiyar al’umma ba biasa ka’ida ba, ko Gwamna yake nema ko dan majallisa yake nema ko ma Shugaban kasa yake nema yana da kyau ‘yan Nijeriya su kaurace masa, su watsar da duk jam’iyyar da ta tsayar da shi takara.
Yanzu kusan kamar yadda ake ta yayatawa mutane, lokacin zabben wata jam’iyya ido rufe ya wuce, don haka mutane su duba cancanta su zabi mutanen kirki masu amana wadanda za su taimake su su sakarwa duk wani mai hakki, hakkinsa, ko wacce jam’iyya ce ta tsayar da mutanen kirki a zabe su, kada mutane su yi la’akari da babbar jam’iyya, duk girman jam’iyya idan ta tsayar da barawo a kauce mata.
Musamman zaben Gwamnoni,yana da kyau mutane su bude ido, kada su kuskkura su baiwa barayi maciya amana da maciya rashawa amanar Shugabancinsu. Gwamnoni kusan muna iya cewar sune babbar matsalar wannan kasa, domin dai na farko yannzu kusan su ne a majalisar dattawa, inda bayyan sun gama shekaru takwas a matsayin Gwamnoni a jihohinsu,yanzu sun mayar da majalisar dattawa a matsayin wajen ritayarsu.
Bayan haka kuma, Gwamnoni kusan yanzu duk ‘yan majalisun dokoki na jihohi da na tarayya duk yaransu ne, dan haka suna nada duk wanda suka ga damma ya zama dan takara a cikin am’iyyarsu, a saboda haka, mutanne su kauracewa zabar irin wadannan Gwamnoni musamman idann rashin gaskiya da rashin amanarsu ya bayyana.
Mutane za su kasance cikin kunci da wahala da rashin sanin ciwon kai, idan har za su kama Gwamnansu da cin amana da rashin gaskiya balo balo kuma su ci gaba da goya masa baya, lallai mutanne su dawo daga rakiyar irin wafdannan mutane komai irin zakin bakin muryarsu da ta ‘yan korensu.
Haka nan, ‘yan majalisun dokoki na jihohi,lallai mutane nsu zabi nagartattun mutane, wadanda za su tsayar da gaskiya su yi aiki bisa adalci da son ci gaban al’imma, a zabi mutanen kirki a duk jam’iyyar da suka tsaya matukar ana kyautata musu zato na alkhairi, ana musu fatan idan an zabe su ba za su ha’inci al’umma ba, irin wadannan mutane su ne ya kamata gungun mutane kirki masu kishhin kasa da son ci gaba su hada kai su zaba a dukkan matakaii na zabe.
Rashin zaben mutane kirki zai sake jefe al’umma cikin mawuyaccin hali na wasu karin shekaru guda hudu nan gaba, dan haka al’umma su sani cewar a duk bayan sshekaru hudu sau daya ake wannan zabe a duk fadin tarayyar Najjeriya, idan mutane suka zabi nagartatttun mutane wadanda suka cancanta, to za su kasance cikin ‘yanci da walwala da sharbar romon demokaradiyya harr na tsawon shekaru hudu, amma idan aka kuskura aka zabi son rai ko son abin duniya, aka zabi mutane dan sun bayar da kudade ba dan sun cancanta ba, to mutane za su dandana kudarsu.
Duk dan takkarar da ya zo ya baka kudi domin kaa zabe shi, ka karbi kudinsa ka zabi cancanta, ka zabi mutanen kirki nagartattu wadanda za su hidimtawa al’umma, su alkinta dukiyar jama’a su yi abubuwan da suka dace.
Mutane su zabi ‘yan takarkarin da za su sakarwa kananan hukumomi cikakken ‘yancinsu na walwala, wadann da za su sakar musu kudadensu da Gwamnatin ntarayya take basu, kada mutane su zabi ‘yan takarkarin da za su kwashhe dukiyar kananan hukumomi su yi kashe muraba tsakaninsu da iyalansu da abokansu da dukiyar jama’a.
Mu sani kuma mu fahimta, wannan dukiya ta kananan hukumomi hakkin al’umma ne da za a yi musu ayyukan raya kasa da ci gaba a yankunannsu, ba hakkin Gwamnan bane ya cinye kudaden kananan hukumomi musamman kauyuka kuma jama’a su ci gaba da binsa, suna ganinsa a matsayin gwarzo.
Maha’inta, ‘yan damfara maciya amana bai kamata jama’a suu sake basu dama ba. Baiwa irin wadannan mutanne dama domin su jagoranci al’umma babban koma baya ne ga ci gaban kasa da walwalar al’umma da ‘yan kasa, lalllai muna sake jadda kira ga a zabi nagartattun mutane wadanda za su yiwa al’umma ayyuka na ci gaba domin samun ingantacciya kuma kyakkyawar rayuwa nan da wasu shekaru hudu masu zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!