Connect with us

MANYAN LABARAI

An Sace Akalla Mutum 50 A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja Jiya Alhamis

Published

on

•Al’ummar Rijana Su Bayyana Damuwarsu

Har yanzun dai barayi masu garkuwa da mutane da ke aiwatar da aika-aikar su a kan babban titin Kaduna zuwa Abuja, da kuma na hanyar Abuja zuwa Kaduna din suna ci gaba da uzzurawa al’umman da ke bin hanyar.
In ba a manta ba, kimanin makwanni uku da suka shige mun kawo maku hira da wani bawan Allah da ya sami kubuta daga hannun barayin bayan da danginsa suka biya tsabar Naira 500,000, a matsayin kudin fansan shi, a lokacin da barayin suka sace tare da yin garkuwa da su a kan hanyar kimanin su mutane,18, maza 11 mata bakwai.
Ko a lokacin wanda ya sami kubutan ya shaida mana yanda masu garkuwa da mutanan suka yi ta shaida masu cewa, su ne fa suke aiwatar da wannan aika-aikar a yankin Zamfara, a yanzun haka sun dawo yankin Kaduna ne domin Sojoji suna ta kashe su a can yankin na Zamfara. Abubuwan da suke faruwa a kan hanyar a halin yanzun suna jefa razani a kan ko da gaske ne waccan maganar da barayin mutanan suke yi na cewa na yankin Zamfara din ne suka dawo hanyar ta Kaduna zuwa Abuja a halin yanzun.
A yanzun haka, al’ummar garin Rijana da ke kan babbar hanyar suna cikin wani mawuyacin hali, inda suke kokawa da ayyukan na masu garkuwa da mutane, wanda suka ce kusan a halin yanzun lamarin ya kazanta don kuwa kusan a kullum sai masu garkuwa da mutanan sun tare hanyar sun kwashi mutane musamman fasinjojin da ke bi ta hanyar, a wasu lokutan kuma sukan kai har da kisan wasu daga cikin fasinjojin a nan take, sannan su yi awon gaba da sauran su yi garkuwa da su a can cikin nisan daji har sai ‘yan’uwansu sun biya makudan kudaden fansar su, ko kuma su kashe su.
Majiyarmu daga garin ta Rijana, ta labarta mana yanda ko a wannan makon barayin suka jera akalla kwanaki shida a kullum suna tare hanyar su kashe na kashewa su yi awon gaba da wadanda suka ga dama ba tare da wani ya taka masu burki ba. Kamar yanda majiyar tamu wacce ba ta so mu ambata sunanta a nan ba; ta labarta mana.

Daga cikin wadanda suka rasa ransu a kan hanyar ta hanyar bindigewar da barayin mutanan suka yi masu akwai wani babban jami’in hukumar Kwastan, wanda suka bindige shi har lahira a ranar Litinin. “Tilas ne mu kasance cikin damuwa, domin a kullum cikin garin namu ake kwaso gawarwakin wadanda barayin suka kashe a kawo mana domin mu yi masu jana’iza,” in ji majiyar tamu.
Majiyar tamu ta ba mu labarin yanda barayin suke tsayawa a wani wuri da ke kan hanyar ta Kaduna zuwa Abuja, dab da garin na su na Rijana kadan, wurin da wasu itatuwan Kwakwa suke, kusa da gidan gonar wani babban tsohon jami’in Soja, a akan kira wajen da tafkin Soja, kafin a kai wannan gadar, a nan ne abin ya fi faruwa, in ji majiyar tamu.
“A daren Laraba zuwa wayewar garin Alhamis, 7 ga wannan watan na Fabrairu, 2019, watau a jiya kenan, barayin sun tare wannan wajen inda suka yi awon gaba da akalla mutane 50, har yanzun kuma babu labarin su. a yanzun haka, motoci biyar da suka kwashe mutanen daga cikin su suna nan a ofishin ‘yan sanda na garin namu na Rijana, su ‘yan sandan ne suka kwaso motocin zuwa ofishin na su,” in ji majiyar tamu.
“Duk wanda ya motsa a halin yanzun sai a ce a gefen Rijana ne abin ke faruwa, wannan ya sanya tilas abin yake ta damun mu, kuma a duk lokacin da suka yi ta’asar a nan Rijana ake kawo gawarwakin, in ma wasu kayayyakin ne na daban duk dai a nan Rijanan ne ake kawo su, wannan ya sanya mu a cikin damuwa matuka ainun.”
“Mun jima muna ta kokawa musamman ga hukumomin da ya kamata a ce sun dauki matakan hana aukuwan ayyukan mugayen barayin, amma dai ya zuwa yanzun, lamarin kusan a kullum kara kazancewa yake yi,” in ji majiyar tamu.
Wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna, domin jin ko suna da masaniya a kan halin da babban hanyar ta Kaduna zuwa Abuja ke ciki, da kuma jin matakan da rundunar ‘yan sanda ta dauka ko take shirin dauka don kare dukiyoyi da rayukan matafiya a kan hanyar, sai dai Kakakin rundunar ya shaida wa wakilinmu cewa, shi yana halartar wani, “Workshop,” ne a Abuja, don haka, “sai dai in turo maka lambar 2IC di na,” in ji Kakakin rundunar”.
Daga bisani Kakakin Ýan sandan ya turo wa wakilinmu lambar, wanda wakilin namu ya yi ta kokarin kira amma ba a amsa ba, har lokacin kammala wannan rahoton namu.Har yanzun dai barayi masu garkuwa da mutane da ke aiwatar da aika-aikar su a kan babban titin Kaduna zuwa Abuja, da kuma na hanyar Abuja zuwa Kaduna din suna ci gaba da uzzurawa al’umman da ke bin hanyar.

Daga bisani Kakakin Ýan sandan ya turo wa wakilinmu lambar, wanda wakilin namu ya yi ta kokarin kira amma ba a amsa ba, har lokacin kammala wannan rahoton namu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!