Connect with us

MAKALAR YAU

Makircin Turawan Yamma A Sha’anin Zaben Nijeriya

Published

on

Tun gabanin kyankyasar Jamhuriyar Siyasa ta farko a wannan Kasa tamu ta Nijeriya, Turawan, musamman na Ingilishi, ke yin mummunan tarnaki da takidi ga sha’anin Zabe cikin wannan kasa, har kawo lokacin wannan Jamhuriya ta hudu da muke ciki a yau. Sai dai yanayin salon magudin da Turawan ke amfani da, kan canza daga lokaci zuwa lokaci.

Takidin Tsarin Mulkin Baturen Ingilishi

Turawan na Birtaniya, sun yi amfani da mabanbantan Kundinan Tsarin Mulki da suka kirkira a lokuta daban-daban, domin tauye hakkin masu zabe gami da dasa harsashin salon siyasa cikin rigar kabilanci, bangarenci da kuma nuna banbancin addini a tsakanin al’umar Kasa.

Tsarin Mulkin Clifford, 1922, Da Na MacPherson, 1951

Ta tabbata cewa, karkashin tsarin mulkin Clifford, 1922, an mugun tauye hakkin masu zabe, saboda ba a na la’akari ne ba da cancantar mutum na ya kada kuri’a, yayinda Shekarunsa na haihuwa suka kai goma sha-takwas (18) a Duniya. Masana sun cigaba da karin hasken cewa, duk wani tsarin mulki da Turawan suka kirkira har zuwa Shekarar 1954, kawai sun ba da ‘Yancin yin zabe ne ga wani yanki na jama’ar Kasa. Ma’ana ba kowa da kowa ne ba zai mori ‘Yancin yin zabe, sai wadanda Turawan Mulkin Mallaka suka ga dama suka sahalewa.

(Iyayi, Paper Presentation, August 4, 2004 : 4).

Shi ko Kundin Tsarin Mulkin Macpherson, 1951, za a ga ya fi karkata ne kacokan ga haifar da jumurdar irin salon siyasar kabilanci, bangarenci da addini a tsakanin ‘Yan Nijeriya tun a wancan lokaci.

(Fagge & Alabi, 2007 : 131-132)

Manyan jam’iyyu uku (3) dake a Shiyyoyin Gabashi da Yamnaci da kuma Arewacin wannan Kasa, irin su, NPC da AG da NCNC, sun tafka mummunar salon adawar siyasar kabilanci ne da ta bangarenci hada da ta addini a tsakaninsu. Sai da ta-kai ta-kawo, duk Shiyyar da wata jam’iyya ta mamaye, ko kadan ba ta daga kafa ga daya jam’iyyar, domin kuwa za a ga tana kokarin fassara wannan jam’iyya ne a matsayin ba ta ‘Yan Kabilarsu ba ce, ko ba ta ‘Yan Yankinsu ce ba.

A wancan lokaci da al’umar wannan Kasa ke karkashin wancan bakin Tsarin Mulkin MacPherson dake iza wutar nau’in salon siyasar Kabilanci da ta Addini tsakanin jama’ar Nijeriya, sai ya zamana cewa, a duk sa’ad da wani Mutumin Arewacin wannan Kasa ya kulla kawancen siyasa da jam’iyyar siyasar AG ko ta NCNC dake a Gabashi da Yammacin wannan Kasa, sai a ga akasarin al’umar ta Arewa na fassara shi da wani Mutum Kazgi maras tarbiyya, wanda ya kulla kazamin kawance da wasu mutane kafirai makiya Addinin Musulunci, wadanda suke ko kadan ba sa son Shiyyar Arewa ta cigaba.

(Fagge & Alabi, 2007 : 131-132).

Ya tabbata a wancan lokaci, da wani Mutum Bayerabe zai kulla kawancen siyasa da jam’iyyar NPC ko NCNC, ‘Yan’uwansa Yarbawa na yi masa kallon Mutumin Banza ne, wanda ke da burin ya ga can wasu Mutane Baki su hauro su zo Shiyyar Yarbawa su bautar da su. Wadanda samsam ba sa muradin ganin Shiyyar Yarbawan sun cigaba.

(Idem.).

Yunkurin ‘Yan Mulkin Mallaka Na Karkata Ga Wata Jam’iyyar Siyasa

A kan hanyar Turawan Ingilishi na yin kafar-ungulu ga samun sahihin zabe a wannan Kasa tun azal, sai ya zamana cewa, sun ware wasu manyan jam’iyyu uku masu karfin rinjayen magoya baya a Shiyyoyi uku (3) da ake da su a wancan lokaci. Sannan, sai wadancan Turawa suka tashi haikan wajen ganin sun kassara karfin duk wata jam’iyya dake neman yin adawa da wadancan jam’iyyun da ‘Yan Mulkin Mallakar suka mai da su ‘Yan Mowa a Kasar.

Goyon bayan da Jam’iyyar NPC ne da ta samu daga Turawan a Shekarar 1954, shi ya ba ta matsanancin iko da karfin yin dirar mikiya bisa gadon bayan jam’iyyar Adawa ta NEPU.

(Idem., P. 115).

Cikin wani dogon rubutu da Dr Alkassim Abba na Sashin Tarihi na Jamiar Ahmadu Bello ta Zaria (A.B.U) ya yi, a matsayin raddi ga Mujallar Tell, wanda yai masa lakabi da “The Rigging Of Nigerian History” ya tabbatar da cewa, Turawan na Birtaniya, sun nuna matukar goyon bayansu ga jamiyyar AG, don son ganin an nakasa karfin magoya baya da jam’iyyar NCNC ke da shi.

Ya tabbata cewa, wadannan ‘Yan Mulkin Mallaka, sun mara baya tare da yin duk mai yiwuwa wajen karkata ga jam’iyyar NPC, domin ya kasance ita ce jam’iyyar da za ta lashe zaben karshe da Turawan za su gudanar tare da mika gwamnati ga jam’iyyar da ta sami rinjaye. Ba su tsaya ga karkata ga wata jam’iyya kawai ba a wamnan zabe, sun ma yi kokarin kassara sauran jam’iyyun dake adawa da wannan tunani nasu.

(Okonjo, 1974 : 331).

Cigaba Da Tsoma Baki Cikin Lamuran Siyasarmu

Duk da ‘Yanci na zahiri da ake gani an samu daga wadancan makiran Turawan Mulkin Mallaka, da mutane na karanta bayanan Masana akai-akai, za su fahimta cewa ba a rabu da bukar ba har kawo wannan lokaci. Turawan ba su gushe ba wajen shirya makirce-makirce iri-iri a kan hanyarsu ta juya akalar siyasarmu son-ransu.

Masana sun ce, Hukumomin Tsaro na gwamnatocin Amurka da Birtaniya ne ke da alhakin kashe Marigayi Kamar Murtala Ramat Muhammad, wanda ta hanyar hakan ne suka sami nasarar kawar da shugabancin Kasar da gwadaben kishin Kasa.

(Iyayi, Paper Presentation, August 24, 2004 : 15).

Masanan sun kara hakkake cewa, mutuwar Janar Sani Abacha da ta Chief MKO Abiola, wani al’amari ne da ake danganta shi da makircin wadancan Hukumomin Tsaro na Ingila da na Amurka.

Masana na kara tabbatar da cewa, wadancan hukumomin tsaro na Amurka da Birtaniya ne suka dankarawa ‘Yan Nijeriya dakon Chief Olusegun Obasanjo a matsayin Shugaban Kasa a Shekarar Zabe ta 1999, tare da taimakawar gungun wasu mutane da suka jima da mamaye ko shake sha’anin SHUGABANCI a wannan Kasa.

(Iyayi, Paper Presentation, August 24, 2004 : 15).

Daga Illolin Tsoma Bakin Turai Cikin Lamarin Samar Da Shugabanni A Nijeriya

Ko kadan ba wani kayan gabas ba ne ga ko wace Jam’iyya, PDP ce ko APC koko APGA ce, a wayigari irin wadancan Karnukan Turawa Zalamammu ne za su rika dafa musu, don kai wa ga samun nasarar Shugabantar Al’umar Nijeriya.

Cikin rubuce-rubucen Masana a wannan Kasa, sun hakaito irin yadda wadancan Shugabanni da Turawa ke daurewa gindi wajen mulkar al’uma, ke sallama sha’anin tattalin arzikin wannan Kasa ta Nijeriya zuwa ga Azzaluman Kungiyoyi Mashaya-jini na Duniya, irin su Bankin Duniya da Bankin Ba Da Lamuni na Duniya (IMF & WORLD BANK). Hakan na faruwa ne a bisa a bisa dalili na ramawa-kura-aniyarta, tun da duk wanda ya ci ladan Kuturu, yi masa aski wajibi ne. Abin nufi, gagarumin goyon baya da wadancan Mayun Turawa suka bai wa SHUGABANNIN ta karkashin Kasa wajen darewa bisa kujerar shugabantar al’umar Kasa raunana, shi ke wajabta wangale musu lalitar tattalin arzikin Kasa, su ko su yi ta warba ba dare ba rana. A lokacin da wasu marasa lafiya a Kasa ke mutuwa, saboda rashin kudin da za su mika a yi musu magani. A lokacin da wasu ‘Yan Mata ke sayar da budurcinsu, don sayen abincin da za a je gida a ci.

A fili yake cikin tarihin wannan Kasa kamar yadda Masana suka hakaito, Shugaba A Nijeriya, kan fi jimawa bisa madafun -ikon mulkar jama’a ne, yayin da ya zabi zama Dan-Koren Turawan Yamma, sama da son hidimtawa Al’umar Kasa Talakawa Raunana.

Rashin sallamawar son zuciyar irin wadancan gungun Turawa ne, ya jazawa Marigayi Janar Murtala Ramat Muhammed yin Watanni shida (6) kacal yana mai jagorantar Kasar, a karshe akaaike da shi barzahu cikin Shekarar 1976.

Rashin goyon bayan Janar Buhari ga wadancan Turawa sa’ad da yake cikin Kakin Soja ne, ake ganin ya sabbaba hambarar da gwamnatinsa cikin kankanin lokaci da ya yi bisa karagar mulki, daga Shekarar 1983 zuwa 1984.

Janar Yakubu Gowon da ya mulki Kasar tsawon Shekaru tara (9), sai ya zamana Turawan ba su sa masa da zafi ba. Ko da yake Masana na da bayanan da suka nuna cewa, gwamnatin ta Gowon da Gwamnoni, sun nuna tsantsar almubazzaranci da dukiyar al’umar Kasa shan-kai. A karshen lamari, wasu gungun mutane da ake yi musu kallon ‘Yan Kishin Kasa ne suka tintsirar da gwamnatin ta Gowon cikin Shekarar 1975.

Maganar goyon bayan da gwamnatin Obasanjo da ta Ibrahim Babangida ke bai wa Turawan sa’ad da suke bisa kujerun mulki ba shi misalto. Akwai masu danganta tsantsar goyon bayansu ga Turawan ne ya sanya su jimawa bisa karagun mulki ba tare da an cim musu ba.

An Ki Cin Biri An Ci Dila

Da al’umar Kasa za su zurfafa tunani, za su iske cewa, ta’adar Turawan ta yakar magudin zabe da cin-hanci da rashawa musamman a nahiyarmu ta Afurka, tamkar salon maganar da ake wa taken AN KI cin biri an ci dila ne.

Me zai hana mu yi duba zuwa ga hatsabibiyar rawar da ‘Yan Mulkin Mallakar ke takawa a Kasashen na Afurka game da sha’anin samar da SHUGABANCI, gabanin da kuma bayan sun mika ‘YANCIN KAI na da’awa a Kasashen.

Yaya batun yaki da cin hanci da rashawa da Turawan ke ta balokoko a kai? Shin, wai su waye Barayin Kasarmu ke kai musu ajiyar kudaden sata, alhali sun san komai game da haramtacciyar hanyar da aka bi wajen mallakar dukiyar? An yi fashi da makami, an je Kotu, bayan bincike, alkali ya fahimci ba da kai ne ake zuwa yi wa jama’a fashi ba, sai dai, kai ne wanda ke adanawa Barayin Kayan Sata bayan sun tafka fashin. Ko Babanka ne Alkalin, shin, da wane suna ne zai kira ka? Mai yaki da fashi da makami? Amintacciyar ma’ajiyar ‘Yan fashi? Ko Dan ba ruwanmu zai kira ka? Dole dai kam akwai wani suna da Kotu za ta samo daga cikin Sukullufin Doka, ta kira ka da shi.

Kazantar Zabukan 2007

Maganar yadda Zaben Shekarar 2007 ya gudana, wani abin kaico ne da daga hankali ga duk Mutumin dake da gurin a sami kyakkyawan yanayin tafiyar da lamuran zabe a wannan Kasa.

Hakika yadda wannan zabe ya gudana, ya nuna a fili karara cewa, rukunin wadancan Mutane da aka gabatar da munanan ayyukansu a baya wajen dukufa gami da shirya kitimirmirar zabe salo-salo a wancan Zabe na 2003, a wannan Zabe ma na 2007, suna kan bakarsu ne, ta’adarsu ta karairaya Dokokin Zabe na nan daram ba tare da sauyawa ba.

Da yawan Masana da masharhanta, sun yi dogon karin hasken cewa, munanan abubuwa na Allah-wadai da suka afku a wannan Zabe na Shekarar 2007, sun kere na Shekarar 2003 muni. In Sha Allahu nan gaba kadan, za mu gabatar da abinda ya samu game da wancan ikirari na Masana da Masharhanta daki-daki.

Ba tare da jan dogon zare ba, yanzu za mu koma ga duba ayyukan rukunin irin wadancan Mutanen da aka nazarci ayyukansu gami da tufkar da suka da suka tufka a zaben da aka yi cikin Shekarar 2003, tare da kara tabbatar da cewa, rawar da suka taka cikin zabukan biyu na Shekarun 2003 da 2007, duka Danjuma ne da Danjummai.

1-Daga Mugunyar Rawar Da Masu Rike Da Madafun-iko Suka Taka, 2007

Gwamnatin Chief Olusegun Obasanjo, ta yi amfani da hanyoyi iri-iri cikin Zaben 2007, wajen ganin ta kai ga nasarar lashe Zabuka, ko da kuwa yunkurin cimma wannan muradi zai bayu ne zuwa ga asarar rayuka da dukiyoyin al’umar Kasa.

Kamar yadda akasarin Shugabanni a wannan Kasa suka saba, gwamnatin Obasanjo, ta yi amfani da karfin-iko da Kundin Tsarin Mulki na Kasa ya sahale mata, wajen yunkurin canza akalar hakikanin “Alkaluman Zabe” a Shekarar Zaben ta 2007. Ko da yake, ba a ko’ina ne ba gwamnatin ta sami nasarar aikata hakan.

Ba ya ga zuwa da salo-salo na tafka magudin zabe, gwamnatin ta Obasanjo a karshe, ta ma yanke shawarar dawwama ne bisa karagar mulki, duk da cewa wannan makahon yunkuri na gwamnatin, ya tunkuyi Tsarin Mulki na

Kasa (Section 137 (1), 1999 Constitution).

A kan hanyar Obasanjo na zama Shugaban Kasa na dindindin a wannan Kasa ne, ya hadu da muguwar tirjiya daga Mataimakinsa, Atiku Abubakar. Atikun, na daga fitattun ‘Yan Nijeriyar da suka yi tsayuwar gwamin -jaki bisa turbar da Obasanjon zai bi, don ganin wancan mummunan mafarki nasa da yai wa Tsarin Mulki karan -tsaye ya samu tabbata.

(Daily Trust, April 4, 2007).

Dauki-Ba-Dadi Tsakanin Shugaba Obasanjo Da Mataimakinsa Atiku, 2007

Rikicin da ya rufta tsakanin Shugaba Obasanjo da Mataimakinsa Atiku cikin Shekarar 2007, ya yi geza gami da fadada har zuwa ga wasu hukumomi na gwamnati, irin su Hukumar Zabe da Hukumar Shari’a. Da daman bayanai sun tabbatar da cewa, Shugaba Obasanjo ne ke amfani da wadancan hukumomi, don yin ramuwar gayya ga Atikun, sakamakon rawar da ya taka, na yin kafar-ungulun da ta dakile yunkurin Ogan nasa na son yin Tazarce a karo na uku. Atikun da kansa, na fassara wadancan matakai da Obasanjon ke dauka karkashin wadancan hukumomi, a matsayin wani yunkurin da zai kassara shirinsa, na tsayawa takarar Kujerar Shugaban Kasa.

(Daily Trust, April 4, 2007).

Yawan rikice-rikicen da suka rika ruruwa babu kakkautawa tsakanin Obasanjo da Atiku ne, suka jaza tare da tilasawa Atikun ficewa daga jam’iyyar ta PDP zuwa jam’iyyar AC. Domin kuwa, lissafin Atikun ya nuna cewa, burinsa na son zama dan takarar kujerar Shugaban Kasa, ba zai sami cikuwa ba, muddin bai bar jam’iyyar ta PDP ba.

Ashirin da biyar ga Watan Nuwanbar Shekarar 2006 ne Atiku Abubakar ya shelanta bukatarsa ta son tsayawa takarar kujerar Shugaban Kasa. Sannan, a Watan Disamba na Shekarar 2006 ne, jam’iyyar AC ta tsayar da Atikun, a matsayin Dan Takararta na Kujerar Shugaban Kasa, a zabe mai fuskantowa na Shekarar 2007.

Wancan kazamin shiri na Shugaba Obasanjo, na son ganin ya rikide zuwa shugaba na dindindin a Najeriya, an yi jana’izar yunkurin ne a zauren Majalisar Dattijai Ta Kasa, yayinda Sanata Sule Yari Gandi ya gabatar da wani kudiri cikin Watan Mayu na Shekarar 2006.

(Kano Chronicle, October 13, 2010).

Babu shakka, waccan ja-in-ja da aka rika samu a tsakanin Obasanjo da Atiku, ta matukar taka mugunyar rawa daga bangaren gwamnatin tarayya, wajen yin zagon-kasa ga sha’anin  Zaben Shekarar 2007. Nan gaba, yayinda muka fara gabatar da rawar da Kotuna da Hukumar Zabe suka taka a wannan zabe na Shekarar 2007, za a fi fahimtar wannan ikirari.

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da aka fi sani da “Human Rights Watch”, ita ma ba a bar ta a baya ba, cikin masu nuna tsoron su game da illolin da wancan sabanin fahimtar dake tsakanin Shugaba Obasanjo da Mataimakinsa Atiku ka iya haifarwa wajen samun ingantaccen zabe a Shekarar ta 2007.

(Daily Trust, April 5, 2007).

Waccan Kungiya ta kare Hakkin Dan Adam, ta gargadi gwamnatin tarayya game da zargin da ake yi mata, na yin shisshigi gami da yin kutse cikin sha’anin gudanar da zabukan na Shekarar 2007, tare da karin hasken cewa, wancan yunkuri na gwamnati, ka iya zama wata barazanar da za ta  jaza barkewar rikicin Siyasa a Kasar.

Shugaban Kungiyar ta Dan Adam a Najeriya, Mr Chukwuma, ya yi bayanin cewa, tilas ne gwamnatin tarayya ta dauki wasu kwararan matakai, wadanda za su taimaka wajen samar da Ingantaccen Zabe a Kasar. Ya kara da cewa, wajibi ne gwamnati ta kawar da duk wata halayya abar zargi da ka iya jaza barkewar rikicin siyasa. Sannan, ya ja hankalin gwamnati, na ta yi biyayya ga hukuncin Kotu da ake tsimayi, ko da kuwa zai saba da yunkurin da gwamnatin ke yi, na hana ‘Yan adawa tsayawa Zabe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!