Connect with us

TATTAUNAWA

Amfani da Magungunanmu Da Abincinmu Na Gargajiya Ne Babbar Mafitarmu: Bakuwarmu Ta Wannan Makon Ita ce Dakta Hajja Fanna

Published

on

Dakta Hajja Muhammed Kawu na daya daga cikin ‘yan majalisar Sarkin maganin jihar Kano Dakta Rabilu Muhammed wadda ke da matsayin sarkin yakin sarkin maganin a tattaunawarta da Editanmu a gidanta da ke Kano ta bayyana tarihinta da yadda ta tsinci kanta a harkar bayar da maganin gargajiya da kalubalen da take fuskanta da nasarorinta a rayuwa. A karshe kuma ta bayyana burin da take da shi a rayuwa. Masu karatunmu ku biyo mu don jin yadda babbar bakuwar ta mu ta baje kolin bayanai domin amfaninku:

Da farko masu karatunmu za su so ki gabatar da kanki.
Sunana Dakta Hajja Muhammed Kawu(Sayyada Fanna). Ni haifaffiyar Maiduguri ce ‘yar asalin kabilar Shuwa-Arab. Na fito daga zuriyar Sharif Maijiri. Muna da dangartakar sarauta ta Dambuwa. Na taso a garin Maiduguri, inda cikin ikon Allah kamar yadda aka saba iyayena sun sani a makaranta, ta koyon karatun Kur’ani da kuma ilimin addinin Musulinci. Sannan kuma a lokaci guda ina karatun boko, wannan ya ba ni damar sanin Kur’ani da ilimin addini da na zamani daidaidai gwargwado.
Na taso na samu iyayena na da baiwar bayar da maganin gargajiya, saboda haka tun daga wannan lokaci na fara sanin magunguna. Na fara bayar da magani tun ina ‘yar shekara tara. Na gaji bayar da magani ta bangaren mahaifiyata. Asalin mahaifita kuma Bagobira ce, ita ma tana da dangantaka da masautar Dundu ta Gobir. Saboda haka daga bangaren mahaifiyata ina da dangantaka ta Bawa-jangwarzo.
Shi kuma mahaifina bangarensu sharifai ne, kuma malamai. Yana da dangantaka da sautar Mai a cikin Maiduguri. Su ne wazirai wadanda aka samu yarjejeniya tsakaninsu da Barebari lokacin da suka zo Borno. Arab ne kakanninmu. Kankanninmu suka kawo addinin Musulci Borno. Lokacin da suka zo wad a sarakunan kasar Borno Musulinci kafin su karba sai da suka yi yarjejeniya, cewa za su karbi Musulinci amma ba za su ba su sarauta ba, in ma za su ba su sarauta, ba za ta wu ce sarautar waziri ba. Su kuma suka amince da wannan yarjejeniya. Saboda burinsu shi ne su karbi Musulinci kuma sun karba.

Kasancewarki mai bayar da magani, a halin yanzu wadanne cututtuka kika fi kwarewa wajen bayar da maganinsu?
Fagen da na fi kwarewa wajen bayar da magani shi ne, na cututtykan da suka shafi ruhi, wato gagararrun cututtuka wadanda aka je asibiti aka rasa gane kansu. Ni kuma cikin ikon Allah nakan bayar da maganin irin wadannan cututtuka kuma a dace, a samu lafiya. Baiwar da Allah ya ba ni da ilimin abubuwan da ke boye ke taimaka min wajen bayar magungunan irin wadannan cututtuka.

Me za ki iya tunawa a matsayin nasarar da kika samu a wannan sana’a ta ki ta maganin gargajiya?
Akwai nasarori da na samu masu yawa, amma dai daya daga ciknsu shi ne, wani aikin cire duwatsun matsalmama da na yi wa wani bawan Allah kuma ya samu waraka. Saboda lokacin da ya zo wajena kusan in ce yana ganin anya kuwa, abin zai yiwu, amma cikin ikon Allah na cire masa kuma bayan na cire na ce ya je asibiti a yi masa hoto domin ya tabbatar. Ya kuma je likitoci suka tabbatar masa da cewa babu wadannan duwatsun. Na yi matukar farin ciki da wannan aiki fiye ma da shi wanda na yi wa aikin, domin Allah ya fid da ni kunya.
Sannan kuma wata babbar nasara da samu ita ce, ta wannan matsayi na sarkin yakin sarkin maganin jihar Kano. Domin kuwa wannan ba karamar karramawa ba ce da shi sarkin maganin ya yi mini. Wannan mukami nawa hakiman kananan hukumomi arba’in da hudu da dagatansu na magani duk suna karkashina. Ka ga wannan babban nasara ce da kuma karramawa a gare ni.
Sannan da tafiya ta yi tafiya aka ga kokarin da nake yi a harakar magani, sai aka kara min wani mukamin na sarauniyar magani ta ‘yan Borno mazauna Kano. Duk wani dan kasar Borno da ke bayar da magani a jihar Kano ni sarauniyarsa ce.
Haka kuma cikin ikon Allah Kungiyar kasashen Afirka ta “Common Wealth” wadda ta kunshi kasashen rainon Ingila ta tabbatar min da sarkin yakin magani ta Arewacin Nijeriya baki daya. Jihohi goma sha tara ne ke karkashina. Saboda haka a takaice wadannan su ne nasarorin da nake alfari das u cewa, na samu a sana’ata ta sayar da magani.
Bisa wannan matsayi da na samu ne, nake da shirin fita zagaye wadannan jihohin yadda zan duba yadda harkokin bayar da maganin gargajiya ke guna. Domin mu kara karfafa gwiwar masu wannan sana’a yadda za su ci moriyarta sosai, sannan kuma al’umma su amfana kamar yadda ya kamata. Sannan kuma lokacin ziyarar za mu ba masu magani shawarwari yadda za su kara inganta sana’arta su, mu nuna musu hanyoyin da za su kara bayar da gudummowa ga al’umma.

Kalubalen Da nake Fuskanta A Rayuwa.
Babban kalubalen da na fi fuskanta shi ne idan aka ce ni ke bayar maganin kaza, idan aka kale ni sai a ga kamar na yi kankanta ko kuma kamar ya za a yi na iya bayar da magani musamman da yake kamar yadda na gaya maka a baya cewa, na fi kwarewa a bayar da maganin gagararrun cututtuka. Wannan ta sa da yawa sai sun samu waraka suke kara tabbatar da abin da na gaya musu, ko kuma idan sun je asibiti an ce musu cuta kaza ke damunsu suka kuma zo wajena na gaya musu kamar yadda likita ya gaya musu.
Haka kuma wani babban kalubalen shi ne, musamman ga mu masu bayar da maganin gargajiya sau da yawa wasu na kallonmu a matsayin bokaye, gaskiya wannan ma ba ya yi min dadi a zuciyata. Shi ma yana daga cikin kalubalen wannan sana’a.
Sanna ga mace kamata wadda ke da iyali da maigida dole akwai kalubale, duk da cewa, ina yaba wa mai gidana kwarai da gaske, bisa taimakon da yake yi min wajen ganin na samu nasarar wannan sana’a tawa. Saboda haka gudummowar da yake ba ni ce ma ta sa na samu karfin gwiwa har nake amfani da baiwar da Allah ya ba ni wajen warkar da marasa lafiya.
Yanzu haka ina da yara guda uku kuma dukkansu na sa su hanyar ilimin magani a zamanance wadanda dukkan karatunsu yana da dangantaka da magani. Kuma cikin ikon Allah ina fatan su taso su bayar da gudummowarsu fiye da yadda na bayar a cikin al’umma.
A karshe, ina kira da babbar murya ga masu bayar da magani da su fadada bincike a kan harkar sana’ar tasu yadda za su kara samun damar taimaka wa al’umma sannan kuma su samu abin biyan bukata na yau da kullum.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: