Connect with us

SIYASA

APC Ce Kawai Za Ta Samar Wa Da ‘Yan Nijeriya Jin Dadin Rayuwa –Fashola

Published

on

Ministan ayyuka, lantarki, da gidaje, Mista Babatunde Fashola, ya bukaci al’ummar Nijeriya da su sake zabar jam’iyyar APC, ministan ya yi wannan kiran ne yau Asabar a daidai lokacin da jam’iyyar take yakin neman zabenta a jihar Legas.

Fashola din ya bukaci al’ummar Nijeriya su zabi APC, in har suna son su samu jin dadin rayuwa, ya yi wannan kiran ne a filin wasa na Teslim Balogun da ke jihar Legas, a daidai lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda ya bukaci al’umma da su tabbatar sun karbi katin zabensu, kafin ranar da hukumar zabe za ta rufe ba da katin zaben.

‘Sannan bayan kun kada kuri’unku kun tabbatar da kun tsaya a kidaya kuri’un, saboda ba zamu yi wasa da kuri’unmu ba, dole mu kasa, mu raka, mu tsare, mu jira a bayyana sakamako.’ Inji Fashola
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!