Connect with us

RAHOTANNI

APC Ta Kasa Samarwa Al’ummar Yobe Mafita —Atiku

Published

on

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, a babban zaben 2019 mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar, ya nemi goyon bayan al’ummar jihar Yobe, a babban zabe mai zuwa, wanda a gefe guda kuma ya zargi jam’iyyar APC wajen kasa kawo ci gaba ga jama’ar yankin.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma Wazirin Adamawa, ya yi wadannan bayanan ne ga dandazon magoya bayan sa a jihar, a sa’ilin da yake gangamin yakin neman zaben sa, a babban birnin jihar Yobe da ke Damaturu.
Ya ce, “yau kimanin sama da shekaru uku da suka shude, wanda jama’ar Yobe suka zabi jam’iyyar APC, amma ina son ku bani dama in tambaye ku, wanne muhimmin aiki jam’iyyar APC ta aiwatar muku? APC ta yi muku alkawarin kyutatuwar tsaro, to yanzu akwai tsaron? Sannan APC ta yi muku alwashin samun aikin yi, yanzu ina aka kwana? APC ta yi alkawarin inganta tattalin arziki, shin da gaske kun gani a kasa?”
“a halin da ake ciki yanzu, talauci a cikin jama’a sai kara matsowa yayi, ga yunwa da tabarbarewar tsaro a kowanne lungu da sakon kasar nan. Jama’ar jihar Yobe, kunnen ku nawa, abinda zan yi muku shi ne, wadannan mutanen sun dagargaza komai a kasar nan. Saboda haka, kar ku kara zabar jam’iyyar APC, zasu sake mayar da hannun agogo baya, sannan ina son ku sani kan cewa, wannan ba jam’iyyar arziki ba ce”.
“kuma kamar yadda na fada daga fari, abinda shugabanin mu ke cewa shi ne, tun dawowar mulkin dimukuradiyya a shekarar 1999, wannan shi ne karon farko wanda arewa maso-gabas ta fitar da dan takarar shugaban kasa. Idan ba kuna son su sake damalmala lamurran mu ba, to ku zabi PDP”.
A hannu guda kuma, Alhaji Atiku ya fadakar da matasa a jihar da cewa, su kasa su tsare kuma su raka kuri’un su kuma su jira a kirga- a rumfunan zaben da suka yi zaben, har lokacin da aka bayyana sakamako bisa gaskiya da adalci.A na sa jawabin, shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Yerima (Prince) Uche Secondus, dora zargi ya yi ga hukumar INEC a yunkurin murdiyar zabe, ta hanyar amfani da matsugunan yan gudun hijira, da ke jihohin Yobe da Borno, wajen shirya cuwa-cuwar murgude alkaluman zaben, wanda ya ce, hakan ba za ta sabu ba. Inda ya bukaci jama’a su yi fitar farin dango wajen yi wa jam’iyyar su ruwan kuri’u tare da katse hanzarin masu son yi aringizon zabe a yankin.
Mista Secondus ya bayyana Alhaji Atiku a matsayin kwararren mutum a sha’anin gudanar da mulki tare da tsara tattalin arziki, wanda ba zai wangale baki ya bar yan wa-ka-ci wa-ka-tashi (cabal) ba, matukar ya dare shugabancin kasar nan.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!