Connect with us

RAHOTANNI

Ba Ci Gaban Da Maku Ya Kawo A Nasarawa –Al-makura

Published

on

Gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Umar Tanko Al-makura ya kalubalanci dan takarar Gwamnan Jihar na jam’iyyar APGA cewa idan ya isa ya bayyana wa al’umman jihar Nasarawa ayyukan da ya yi lokacin da yake rike da wani mukami .
Gwamna Al-makura ya bayyana hakan ne a wajen yakin neman zaben dan takarar gwamnan APC da ya gudana a garin Akwanga ranar Alhamis.
Da yake bayani cikin shagube Gwamnan ya ce, “Kodayaushe mutum sai ya rika cika baki cewa, ya rike mukamin kwamishina ya yi, mataimakin gwamna ya yi minister”.
To da ya rike wadannan mukamin, ya bayyana wa al’umman jihar Nasarawa wani ci gaban da ya kawo jihar din. Ya kara da cewa, ba batun rike mukami ba ne, batun ci gaba ne da aka yi wa al’umma .
Al-makura ya kara da cewa “dan takarar gwamnan na APGA ba ya komai sai siyasar addini kuma mu al’umman jihar Nasarawa babu ruwanmu da siyasar addini”.
“Ba zai taba yiwuwa mu dauki addini mai tsarki na Musulinci da Kiristanci mu sa siyasa a ciki ba. Addini ba abin wasa ba ne”.
Sanan ya kalubalanci dan datakarar PDP da cewa, kifin rijiya ne, babu inda ya sani . Amma dan takarar APC kwararre ne, ya yi aiki a kasashe daban-daban.
Sanan ya kara da cewa, babu adalci a ce a siyasar jihar Nasarawa yankin Lafiya sun yi mulki shekarar goma sha biyu yankin Keffi sun yi Gwamna shekara takwas amma yankin Akwanga ko minti daya ba su taba yi ba, shi ya sa na tabbatar da cewa, yankin Akwanga ya kamata dan takarar gwamna a APC ya kamata ya fito daga wannan yanki, kuma Allah ya ba A.A.Sule.
Saboda haka, ya roki al’ummar Akwanga da su tabbatar sun zuba kuri’arsu ga dukkanin ‘yan takarar APC daga sama har kasa.
Ya ce, na tabbata aikin da A.A.Sule zai yi sai ya fi wanda na yi, saboda kwararre ne, ya kuma cancanta.
Shi ma a nasa jawabin dan takarar gwamnan na jam’iyyar APC Alhaji A.A.Sule ya yi godiya ga abokan takararsa na APC da suka rako shi kamfen inda ya yaba da mataimakin gwamnan jihar Nasarawa Mista Silas Ali Agara da Aliyu Ahmad Wadada.
Ya kara da cewa “Mulki na Allah ne kuma yana ba wanda ya so. Saboda haka, Allah ya ba ni bai kamata wasu su koma gefe suna nuna adawa ba”.
Ya kuma kalubalanci duk wani dan siyasar da ya ce zai kawo musu matsala cewa su ma za su ba kowaye matsala.
Ya kumayi kira ga al’ummar yankin Akwanga da su fito kwai da kwarkwata, su zabe APC da dan takarar shugabancin kasa .
Ya ce, idan ya ci zabe zai kawo ayyukan yi da al’umman jihar Nasarawa za su amfana za su mayar da jihar Nasarawa tamkar jihar Legas.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: