Connect with us

RAHOTANNI

Dalilanmu Na Nema Wa Sanata Kabiru Gaya Kuri’u -KSAF

Published

on

Wata kungiya daga mazabar Sanatan jihar Kano, Sanata Kabiru Gaya mai suna ‘Kano South Awareness Forum (KSAF)’ ta bayyana cewa ba wai kawai tana goyon bayan sake zaben Sanatan ba ne, har ma tana yi masa yakin neman zabe don ganin ya sake maimaita wannan mukami nasa da al’ummar jihar Kano ke matukar amfana da shi.
Shugaban kungiyar, Alhaji Idris Kachako ne ya bayyana wa manema labarai wannan kuduri nasu jim kadan bayan da Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya mika wa Sanata Gaya tutar tabbatar masa ta yin takara a wannan mazaba, wanda ya gudana a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano a kwanakin baya. “Duba da irin ayyukan da Sanata Gaya ya yi mana a matsayinsa na Sanata, ya wajaba al’ummar Kano su sake sabensa don ya ci gaba da yi mana wadannan ayyukan alhairi,” in ji Kachako.
Alhaji Idris Kachako ya kuma bayyana cewa ayyukan alhairi da Sanata Gaya ya jawo, ba wai ga al’ummar mazabarsa ta Kano ta Kudu kawai abin ya tsaya ba, duk al’ummar jihar ne suke amfana da su. Wanda haka ta sa Kachako ke ganin cewa duk a Sanatocin da ke fadin kasar nan babu wanda yake wakiltar al’ummarsa kamar irin na Sanata Kabiru Gaya, wanda ke share wa al’ummarsa hawaye.
Alhaji Kachako ya kuma bayyana cewa a kan Sanata Kabiru Gaya ne aka fara samun wani dan Arewa da ya Shugabanci kwamitin kula da ayyuka na Majalisar Dattawan, wanda kuma wannan mukami nasa ya ba da dama wajen samar wa jihar Kano da sauran jihohin Arewa ayyukan ci gaba, musamman hanyoyi da gadoji da sauran ayyuka.
Haka kuma Shugaban kungiyar ta al’ummar mazabar Sanatan na Kano ta Kudu, ya bayyana cewa tsayin-daka da Sanata Kabiru Gaya ya yi wajen gabatar da kudurin samar da Hukumar kula da yankin Arewa maso Gabashin kasar nan, wato ‘North-East Debelopment Commission (NEDC)’ ba karamin tunani da sanin ya-kamata ba ne da Sanata Kabiru Gaya ya nuna.
Daga nan sai Alhaji Kachako ya yi kira ga sauran ’yan takarar wannan kujera daga sauran jam’iyyu da cewa su sauka su janye wa Sanata Kabiru Gaya girma da arziki, domin a cewarsa ba za su ja da shi ba, musamman bisa la’akari da irin ayyukan alhairin da ya jawo wa mazabarsa, jihar Kano da ma Arewacin kasar nan baki daya.
A karshe Alhaji Kachako ya yi kira ga al’ummar mazabar Kano ta Kudu su fito kwansu da kwarkwatarsu su zuba wa Sanata Gaya ruwan kuri’u fiye da wannan suka zuba masa a zaben 2015 da ya gabata. Yana mai cewa ta haka ne kawai za su iya nuna wa Sanatan godiyarsu game da ayyukan da yake yi masu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!