Connect with us

MAKALAR YAU

Rashin Fahimta Tsakanin Masu Bambancin Addini Babbar Barazana Ce Ga Zaman Lafiyar Kasa

Published

on

Yawaitar kashe-kashe a sakamakon bambancin Addini a sassa da yawa na wannan kasar abin damuwa ne.
Blessing Bature, ta yi rubutu ne a kan fahimtar ‘yan kasa dangane da ta’addancin kungiyar Boko Haram da kuma irin hadin kan da ke kan siradi fiye da yanda yake a baya can, da yawan al’ummun Nijeriya sun dulmiya cikin rigingimun Addini wanda yake ci gaba da yin barazana da hadin kan kasar nan. ta kai ga ‘yan Nijeriya a baya can za su iya tinkaho da samun saukin fahimtar Addini na tsawon shekaru masu yawa, wanda a yanzun duk babu wannan.
Mutum zai iya cewa, babban abin da ke ci wa al’umman kasar nan tuwo a kwarya a halin yanzun shi ne rashin fahimtar juna ta fuskacin Addini, musamman a arewa da kuma tsakiyar kasar nan.a wadannan sassan, tsatsauran ra’ayin Addini shi ke fifita a kan komai. Rikicin Addini yakan mamayi mutanan da ba su ji ba, ba su gani ba a kowane lokaci. Ta yanda ya zama birane irin su Maiduguri, Bauci, Damaturu, Benuwe da Gombe, duk suna cikin tsoro ne a sakamakon rikice-rikicen na ayyukan Boko Haram.
A sakamakon hakan, ya sanya mutane ba sa iya yin hakuri da makwabtan su da suke cikin wani Addinin, don haka a kullum ake fama da rikicin Addini.
A kan haka ne, shugaban kungiyar hadin kan Addinai biyu na kasa, Mista Hillary Iheanacho, yake bayar da tabbacin makomar kasan nan tana hannun matasa ne, don haka ya zama tilas a saita alkiblar matasan ta yanda kasa za ta samu zama lafiya. Wannan ne ya kai shi da shiga kamfen a kan haka, ya zuwa makarantun Sakandare a matsayin na shi gudummawar na ganin ana samar da zaman lafiya a Nijeriyata hanyar wayar da kan matasa a kan mahimmancin zaman lafiya.
Kamar yanda masana halayyar dan adam ke kallon lamarin, Bryan Wilson, a cikin littafinsa mai suna, ‘Human Balues In A Changing World,’ yake cewa, ba tare da samun ‘yancin yin Addini ba, da kuma ‘yancin barin kowa a bisa abin da mutum ya yi imani da shi, ba yanda za a samu tsayayyar Dimokuradiyya.” Kamar kuma yanda wata kotu a Faransa ta bayyana a kwanan nan, “’yancin yin Addini daya ne daga cikin tubulin ‘yancin dan adam. Wannan yana nufin mutum ya yi imani da wani Addini ne ko ma bai yi imani da wani Addini ba, kowane mutum zai so ya sami ‘yancin yin Addini, domin rikicin Addini yana barazana ne mai yawa ga ‘yancin dan adam.
Tambaya a kan ‘yancin dan adam, shi ne mu sami ‘yancinmu a matsayinmu na mutane. Masu tsatsauran ra’ayin Addini nasu hangen daban ne da wannan. Sai dai rikicin Addini ba marasa rinjaye ne kadai yake addaba ba. Farfesa Abdelfattah Amor, mai bin diddigin rikicin Addini na hukumar kula da hakkin dan adam ta Majalisar [inkin Duniya, yana mai ra’ayin, babu wani Addini da ya kubuta daga keta masa alfarma.
Da yake tabbatar da wannan tsoron, daraktan cibiyar ‘yancin dan adam ta Jami’ar, Unibersity of Essed, ta kasar Ingila, ya yi nuni da cewa, “Duk shaidu sun tabbatar da cewa, matsalar rikicin Addini tana karuwa ne a maimakon a ce tana raguwa ne a wannan zamani.”
Yawanci rikicin Addini yana tasowa ne a lokacin da wasu kanji cewa, Addininsu yana saman sauran Addinai ne. a takaice, wannan shi ake kira da tsatsauran ra’ayin Addini, wanda ke nuna gazawar ma’abota wani Addini da su iya rungumar ma’abota wani Addinin da ba na su ba, su zauna a tare. Hakan kuma yana tattare ne da jin da wannan ke yi, Addinin na shi ne kadai halastaccen Addinin da aka saukar daga sama. A nan, lamarin shi ne, mutum ya kasance mai tsananin soyayya ga Addinin sa abu ne mai kyau, hakan kuma ake tsammani, amma in aka yi amfani da wannan tsananin soyayyan ta hanyar da ba ta dace ba, hakan yana iya zama abu mai hadarin gaske a rayuwar al’umma, wannan kuma take hakkin dan adam ne.
Nijeriya, kamar sauran kasashe masu yawa, kasace da ba ruwanta da wani Addini, kamar yanda tsarin mulkinta ya shimfida. yin dubi a cikin tsarin mulki na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima a gurguje, a sashe na 38 (1) da sashe na 18, suna yin nuni da shelanta ‘yancin dan adam kamar haka, “Kowa yana da ‘yancin yin Addininsa, da ya hada da ‘yancinsa na iya canza Addinin na shi, a kashin kansa ko kuma gabakidayansu a al’ummansu, a kadaice ko a bayyane, ya kuma yada Addinin na shi a wajen ibada, koyarwa da kuma yanda ake yin Addinin na shi.”
Hakanan sashe na 10 na dai wannan tsarin mulkin ya bayyana cewa, “Gwamnatin tarayya ko gwamnatin Jiha, ba za ta dauki wani Addini a matsayin shi ne Addininta ba.” Wannan yana kara nuni da cewa, tsarin mulki ya baiwa kowa ‘yancin yin Addinin shi, sannan ba za a tsangwami wani ba a kan ya aikata Addinin na shi. Yawaitan Addinai mabambanta a cikin kasa yana baiwa kowa ya aikata Addinin da ya ga yafi kwanta masa ne a ransa. Don haka, tilas ne a kare ‘yancin yin Addini ga kowa ko ta halin kaka, ko da masu mulki na zamanin ba sa kaunar wannan Addinin na shi.
Samar da ‘yancin Addini tamkar wani sashe ne na kafa ginshiki. sauran ‘yancin na siyasa al’ada da tattalin arziki duk a bisansa ne ake dora su. in har aka karya wannan ginshikin, duk sauran sassan za su ji jiki. FarfesaFrancesco Margiotta-Broglio, ya bayyana lamarin kamar haka: “A duk lokacin da aka keta alfarman ‘yancin yin Addinin da mutum yake so, sauran ‘yancin ma duk za a keta alfarman su ne a gaba kadan.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!