Connect with us

RAHOTANNI

Shugaba Xi Jinping A Matsayin Dalibi Da Kuma Amini Na Yara

Published

on

A gaban yara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan dauki kansa a matsayin abokinsu, kuma yana mai da hankali sosai a kan harkokin ilmantar da yara. Sau tari kuma ya bayyana kulawarsa ga yara. Lokacin da ya koma makarantar da ya taba yin karatu, ya ce, “babu shugaba a nan, dukkanmu ’yan makarantar ne.” Yanzu ga wani labari daban dake bayyanaa yadda shugaba Xi Jinping yake kulawa da zaman rayuwar fararen hula.
“Wane matsayi ne ya dace in dauka? To, bari in dauki matsayi na abokin yara. Sauran wasu kwanaki da suka rage za a yi bikin murnar ranar yara, a matsayina na abokinsu, ina taya yara ‘yan kabilu daban daban murnar bikin.”
Da muka waiwayi baya, a shekarar 2013, a karatowar ranar yara ta duniya, a matsayinsa na abokin yara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya yaran kasar duka murnar wannan rana tasu. A lokacin da yake tare da yara, Xi Jinping ya kan bayyana wa yara labaransa a lokacin da yake karamin yaro. A shekarar 2014, a dab da ranar yara ta duniya, ya bayyana wasu labarai biyu da suka faru a lokacin yarintakarsa.

“Na yi matukar farin ciki da na fara zama dan kungiyar fitattun yara, ban san ko hakan kuma kuke ji ba. Me ya sa hakan? Sabo da wannan abin alfahari ne. Na ga makomar kasarmu da al’ummarmu daga wajenku. Daidai kamar alkawarin da muka dauka lokacin da muka shiga kungiyar, wato a shirye muke a kullum mu ci gaba da aikin da tsoffinmu suka gudanar.”
Da ya ga yadda yara ke rubuta “bauta wa kasa”, ya ce,”Kalmomin bauta wa kasa suna burge ni sosai tun lokacin da nake karami. A lokacin da nake da shekaru hudu ko biyar da haihuwa, mamata ta sayo mini littafi, ta kuma gutsura mini labarin yadda mahaifiyar babban jarumin nan mai suna Yue Fei da ya rayu a zamanin daular Song ta gargajiya, ta zana kalmomin bauta wa kasa a bayan danta. Sai na tambaya, bai ji zafi ba? Sai mamata ta ce, dole akwai zafi, amma duk da haka, Yue Fei zai rike wannan a zuci. Ni ma har yanzu na rike shi a zuci, kuma bauta wa kasa shi ne burin da nake neman cimmawa a tsawon rayuwata.”
Tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, shugaba Xi Jinping ya yi ta yin bikin ranar yara tare da yara daga sassa daban daban, inda kuma ya yi musu fatan alheri.
“Yara manyan gobe, ya kamata ku yi kokari, ci gaban yara shi zai kawo ci gaban kasa a nan gaba, kasarmu ba za ta samu ci gaba ba, idan ba ku iya wuce tsoffinku ba. Yara, ku rubanya kokarinku!”

Malanta sana’a ce mai girma. A dab da ranar malamai ta shekarar 2016, shugaba Xi Jinping ya koma makarantar Bayi ta birnin Beijing da ya taba yin karatun firamare da midil. A lokacin ziyararsa, ya kuma gai da da wasu malamai tare da yin hira da su.
“Yau na sake kawo ziyara makarantar nan, makarantar ta samu gyaran fuska sosai, kuma wallahi na kan tuna da lokacin da nake karatu, da kuma yadda malamai suka ilmantar da ni. Duk inda na tafi, na kan tuna da makarantarmu.”
A ganin shugaba Xi Jinping, “Aikin ilmantarwa shi ne tushen ci gaban kasa. Malamai kuma su ne tushen aikin ilmantarwa, wadanda suke daukar babban nauyi na ilmantarwa.” Ya ce, “Tabbas sa’a ce mutum ya samu malami kwararre, kuma abin alfahari ne ga wata makaranta ta samu malamai kwararru, sa’an nan makomar al’ummar wata kasa ta dogara ga malamai masu kwarewa da ake ta samu a kasar. Ya kamata malamai su zama jagorori ga dalibai ta fannin gyara hali, da karo ilmi, da kirkire-kirkire, da kuma bauta wa kasa.” (Mai Fassarawa: Lubabatu Lei, ma’aikaciyar sashen Hausa ta CRI).
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!