Connect with us

RA'AYINMU

‘Yan Nijeriya Ku Yi Watsi Da Obasanjo, Shi Ba Komai Ba Ne

Published

on

Obasanjo ba shi da alkibla ko wata martaba a idon ‘yan Nijeriya. A makon da ya gabata, tsohon Shugaban kasan ya kira taron manema labarai inda ya yi soki-burutsu da kareyarin banza. Ya ci mutuncin wasu mutane, ya kuma zargi gwamnati mai mulki da shirya magudin zabe da sauran wasu zarge-zarge da dama. Amma fa Obasanjon bai kawo ko da dalili daya tak da zai iya tabbatar da zargin nasa ba, ya yi tsammanin har yanzu shi mutum ne mai mutunci ko muhimmanci da maganarsa za ta iya yin tasiri a wajen ‘Yan Nijeriya, bai san tuni kan mage ya waye ba.
Da zargin da tsohon Shugaban kasar yake yi a kan wadannan mutane masu mutunci da kima gaskiya ne, da tuni asirinsu ya tonu duk da cewa shi nasa matsalolin (Obasanjo) sun wuce batun mutunci ko kima. Wannan dalili ne ma ya sa fitaccen marubucin littafin nan Wole Soyinka ya fada wa duniya wane ne tsohon shugaban kasan, inda ya ce “Obasanjo mutum ne wanda zantukansa ke cin karo da juna, suke kuma cike da son zuciya kamar yadda kowane mutum idan ya ga dama yakan iya yi. Amma a nan abin tambaya shi ne, wane ne zai girmama zantukan makaryaci?”. Haka nan mutum ne da a koda yaushe ke son nuna isa da dagawa, wanda wannan ke nuna cewa ya kamata a binciki lafiyar kwakwalwarsa. Gani yake yi kamar ya fi kowa muhimmanci da daraja a Nijeriya, bai san cewa shi ba komai ba ne, illa mutumin banza wanda ba ya gudun abin kunya, bai dauki karya a matsayin wani abu na zub da mutunci ba. Haka zalika, shi irin Kawun nan ne da babu Uban da zai amince ya hada shi tafiya da ‘yarsa ba tare da wanda zai sa masa ido ba.
A ko’ina a duniya, kyakkyawan tsari da shugabanci na kwarai ne ke dora ko wace irin kasa a kan tafarki na ci gaba, wannan dalili ne ya sa ya kamata a tabbatar an hukunta dukkanin masu laifuka duk kuwa da tsawon lokacin da shari’a za ta dauka ana yin ta, don samun al’umma tagari a wannan kasa baki daya. Babu shakka da ana hukunta ‘yan ta’adda masu aikata miyagun laifuka a Nijeriya, da babu yadda za a yi mutane irin su Obasanjo su ci gaba da yawo har suna zargin wasu da yunkurin shirya magudin zabe da sace dukiyar kasa ba.
Har ila yau, wannan tsohon Shugaban kasa ya aikata laifuka iri daban-daban na cin amanar kasa ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Don kuwa a tarihin Nijeriya zabe mafi muni da aka taba yi a lokacinsa ne kuma shi ya shirya. Wato zaben shugaban kasa da aka yi a 2007, shi ne zabe mafi muni da aka taba yi a Nijeriya, zaben da har yanzu babu takamaiman sakamako na gaskiya da wani zai iya fada maka. Don kuwa ana tsaka da tattara sakamakon kuri’u a wasu bangarori da dama na wannan kasa aka yi wuf aka sanar da sakamakon zaben.
Babu wani zabe da aka taba aiwatarwa karkashin jagorancin Obasanjo da ba a yi magudi ba daga 1999 har zuwa 2007. Wai wannan shi ne mutumin da yanzu yake zargin wasu da shirya magudin zabe. Ya manta cewa, abin da ya shuka a zaben 2007 shi ya girba a lokacin da ya sake neman tazarce a karo na uku, inda kafatanin ‘Yan Nijeriya suka hada kai suka fatattake shi.
Haka nan, a kokarinsa na sake neman tazarce a karo na ukun, ba boyayyen abu ba ne Obasanjon ya raba wa ‘yan majalisar tarayya cin hanci don yi wa dokar kasar kwaskwarima. Inda mafiya yawan su suka karba suka kuma yi fatali da bukatar tasa nan take. Haka zalika, a dai lokacin da yake shugaban kasa, Obasanjo ya yi abubuwa da dama na kama-karya da sauran abubuwa masu matukar hadari da barazana ga ‘Yan Nijeriya. Akwai lokacin da ya tilasta wa shugaban Jam’iyyar PDP da ke rike da Jam’iyyar yin murabus ko ya halaka shi ta hanyar yi ma sa barazana da bindiga. Sannan shi da kansa a dai-dai lokacin ya saita wa yaransa yadda za su sace gwamna mai ci da mai cikakken iko na Jihar Anambara. Wakazalika, a matsayinsa na shugaban kasa sai da ya hana ‘yan sanda gayyatar duk wani mai laifi ko dan ta’addan da ke yi ma sa aiki.
A dai lokacin Obasanjo ne, fadarsa ta zama babbar cibiyar hallaka ‘yan siyasa da masu mulki. Mutane irin su Antoni Janar na kasa Bola Ige, wanda aka harbe shi har lahira a cikin gidansa na Ibadan, da rana tsaka ba tare da daukar wani kwakkwaran mataki ba. Sannan duk wasu da ake zargi da aikata kisan aka kama daya-bayan-daya ya sa aka sake su a sirrance ba tare da kowa ya sani ba.
Haka nan mutane irin su, Marshall Harry, Funsho Williams, Barnabas Igwe da matarsa da ke dauke da juna biyu, Abigail da sauran mutane da dama da ya ga bayansu. Kazalika, lokacin da aka kashe mataimakin shugaban PDP na yankin (kudu-maso-kudu) Aminosari Dikibo a 2004, su biyu ne a motar amma nan take Obasanjo ya ce ‘yan fashi ne suka kashe shi, kai ka ce a gabansa aka yi kisan ko kuma ‘yan fashin ne suka fada masa. Duk da cewa babu wanda ya zargi tsohon Shugaban kasan da aikata kisan, amma dai ba abin mamaki ba ne idan an ce shi ne ganin yadda yana barin mulki ta’addancin ya tsaya cak.
Haka zalika, wannan Obasanjon ne wai ya rubuta wa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan wasika yana zarginsa da yin amfani da ‘yan ta’adda a gwamnatinsa. Ya manta cewa, shi ne ya fara daure musu gindi tare da ba su mafaka a tasa gwamnatin da ta shude.
Amma kuma babu laifi ko guda daya da Obasanjo ya aikata ya kuma bayyana a cikin littafin da ya wallafa. Duk da cewa shi ne Shugaban Nijeriya na farko da ya fara yi wa dokar kasar kutse ta hanyar shigar da wasu abubuwa da babu a cikinta kawai don biyan bukatar kashin kansa. Bugu da kari, ya yi amfani da wasu yaransa ‘yan ta’adda sun kafa wani kamfanin ‘Transnational Corporation Of Nigeriya’ (Transcorp), sannan ya rika bawa kamfanin rijiyoyin Man Fetir da wasu manya-manyan kwangiloli.

Haka nan, Obasanjo a matsayinsa na Shugaban kasa ya rika daure wa cin hanci da rashawa gindi babu kunya ba tsoron Allah. Sannan ya bawa gonarsa da ke Ota lasisi na lamba ta daya a bangaren kasuwancin Kajin gona, duk Kamfanin da ya ga yana neman yin gogayya da shi, sai ya kwace lasisinsa. Har sai da Umaru Musa Yar’adu da ya gaje shi ya zo sannan ya kwace ragamar daga kamfanin nasa.
A matsayinsa na shugaban kasa, haka ya yi ta faman mallakar tarin kadarori da hannayen jari a bankuna da Kamfanoni Man Fetir da sauran manya-manyan Kamfanoni tare da tutse Milyoyin daloli. Sannan ya daure wa cin hanci da rashawa gindi ya kuma sake ba shi gurbin zama. Wannan dalili ne ya sa, da za a dora shi a kan sikeli ko tantama babu shi ne zai kasance shugaban kasa mafi kwarewa da shahara a bangaren cin hanci da rashawa da wannan kasa ta taba samu. Shi ya sa duk da tashin gwauron zabi da farashin Man Fetir ya yi a duniya zuwa dala 140 a ko wane gangan Mai, babu wani abu da ya tsinana wa kasar. Babu wutar lantarki, babu matatun Man fetir, babu komai amma duk da haka sai dan banzan surutu.
Mai abin kunya irin wannan! Da a wata kasar ce ba Nijeriya ba, da tuni kana can a Kurkuku a daure har karshen rayuwarka, ana azabtar da kai ta hanyar yin aiki mai wahalar gaske ko ma fiye da haka. Babu wanda ya ce Shugabanni Ma’asumai ne, amma ana kyautata musu zaton sauke nauye-nauyen da ke kansu ta hanyar kyautatawa da kamanta adalci a tsakanin wadanda suke mulka.
Ko wace kasa na kokarin zaba wa kanta shugaba mafi inganci, amma Nijeriya sai ta zaba wa kanta shugaba mafi lalacewa a 1999, inda har yanzu kasar ke dandana kudarta sakamakon kuskuren da ta tafka. Tsohon shugaban kasan ko shakka babu babban shedani ne wanda babu alheri a zuciyarsa, fasikin da ya mayar da Fadar Gwamnatin Nijeriya wajen aikata masha’a da neman mata, kama daga kan matan aure, matar dansa (sirikarsa) kai har da ma ‘ya’yan cikinsa ba su tsira ba.
Haka Obasanjo ya hana Jihar Legas kason kudinta, kawai saboda ya yi kokarin murde zaben Ahmed Bola Tinubu abin ya faskara, har sai da wanda ya gaje shi ya zo sannan ya tattara ya biya baki daya.
Obasanjo ya samu damar mulkar wannan kasa har sau uku. Sai ka ce kasar da aka tsine wa. Bayan ya bar mulki a 1979, sai ya nuna kamar ya mika wa gwamnatin demokuradiya mulkin ne da son ransa, bayan Janar T.Y Danjuma ne a dai-dai lokacin ya tilasta ma sa yin hakan, amma shi so ya yi ya ci gaba da mulkin kamar yadda ya yi a 2006. Haka zalika, shi kansa Marigayi Janar Murtala Muhammed ya yi yunkurin korar sa a matsayin mataimakinsa sakamakon laifuka da dama da aka kama shi da su dumu-dumu, har sai da Sunday Awoniyi ya shiga tsakani.
Wannan tsohon shugaban kasa, bai taimaki kansa ba idan aka dawo da batun Abacha. Abachan da Obasanjo ya tsana ya kamata a san ko mene ne dalili? Kuma ko babu komai Abachan ya yi wa Obasanjo alfarma ta kin yi masa hukuncin da ya dace da shi (kisa), tunda dai Obasanjon shi ne ya yi dokar da ya yi amfani da ita ya hallaka gwamnansa Joseph Godwalk a 1976 lokacin da yana Shugaban kasa na Soja. Dokar dai ta ba da damar kashe duk wani wanda ke da masaniya a kan yunkurin juyin mulki bai fallasa ba, ko da kuwa yana da hannu a ciki ko babu.
An zargi Gomwalk din ne bisa sanin shirya juyin mulki ga Janar Murtala Muhammed, amma ya yi shiru da bakinsa bai fallasa ba, duk da cewa ba shi da hannu a yunkurin juyin mulkin. Amma haka Obasanjo ya yi masa haddi ba tare da daga kafa ba. Hakan da ya yi shi ma ya kamata a ce Abachan ya yi masa ba tare da wani bata lokaci ba.
A ko da yaushe, Obasanjon na kokarin bayyana Abacha a matsayin mafi lalacewar shugaba da Nijeriya ta taba samu. Amma lokacin Abacha ya fi na Obasanjo sau dubu a wajen ‘Yan Nijeriya. Don kuwa har Abacha ya yi mulki ya gama Dala ba ta taba haura Naira 80 ba, amma a lokacin Obasanjo sai da ta kai Naira 160. Saboda haka, bai ma kamata Obasanjo ya rika magana a kan Abacha ba, saboda ko babu komai ya yi masa fintinkau ta ko’ina.
Har ila yau, lokacin da Obasanjo ya fito daga Kurkuku, ba shi da ko sisin kwabo talauci ya yi masa katutu, ba shi da kadarar da wuce tarin takardu, daga nan bayan shekara guda ya zama shugaban kasa. Amma bayan shekara takwas da shiga fadar Abuja, nan da nan ya zama Biloniya na gani da fada, wannan dalili kadai ya isa a gane cewa Obasanjo ba Shugaba ne nagari ba, illa cikakken maha’inci wanda ya daure wa cin hanci da rashawa gindi.
Babban abin mamaki shi ne, yadda har yanzu Kotun Da’ar Ma’aikata (CCT) ba ta gayyace shi ya yi mata bayani a kan dukiya da kadarorin da ya bayyana a 1999, kafin a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa da kuma dinbin dukiyar da ya tara bayan ya sauka a ranar 29 ga watan Mayun 2007 ba. Don rashin ta ido, wai wannan mutumin ne ke da bakin zagin shugabannin yanzu da wadanda suka gabace shi. Shugaban da hatta hukumar da ya kafa ta yaki da cin hanci da rashawa, sai da ta ba shi digirin girmamawa a matsayin shugaba mafi shahara da kwarewa a bangaren cin hanci da rashawa.
Wannan Kamfanin Jarida a koda yaushe a cikin sanya wa Obasanjo ido yake bisa abubuwa na rashin gaskiya da yake aikatawa a matsayinsa na tsohon shugaban kasa. Kazalika, mun taka muhimmiyar rawa wajen lalata tazarcenka a karo na uku da ka yi yunkurin yi a 2007. Muna nan a kan matakin da muka dauka a kanka ba za mu canza ba: Don haka, ‘Yan Nijeriya ku yi watsi da Obasanjo, shi ba komai ba ne!
Fassarar Sani Anwar
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: