Connect with us

TATTAUNAWA

Zaben Sak Ya Kawo Tsaiko Ga Dokar Kananan Hukumomi — Hamidu Ghani

Published

on

HONORABUL HAMIDU SA’IDU GHANI Dan jam’iyyar APC ne kuma tsohon shugaban karamar hukumar Bauchi a hirarsa da jaridar LEADERSHIP A YAU ASABAR ya yi karin haske kan batun zaben Sak da kuma illarsa, inda ya shaida cewar da bukatar jama’a su yi zaben cancanta domin zabar wadanda suka dace da kawo musu ababen ci gaba, a yi tsokaci kan kudurin cin kashin kan kananan hukumomi inda ya shaida cewar rinjayen jam’iyya guda a mafiya yawan kujerun da suke da ruwa da tsaki kan wannan babin ne ya janyo koma bayan dokar. Ga hirar wadda KHALID IDRIS DOYA ya yi da shi:

Gabatarwa
Sunana Honorabul Hamidu Sa’idu Ghani (Ciroman Liman Katagum), tsohon zababben shugaban karamar hukumar Bauchi.

A matsayinka na tsohon shugaban karamar hukumar Bauchi, ya kake kallon kananan hukumomi a daidai wannan lokacin?
A gaskiya kananan hukumomi a yanzu a karkashin jam’iyyar APC wasu wuraren sun koma baya, wasu kuma sun ci gaba, saboda wasu jihohin sun bai wa kananan hukumominsu ‘yancin cin kashin kansu ta hanyar ba su damar yin zaben kananan hukumomi da sauran abubuwan da suka dace, wanda shugaban kasa ya yi kiran a yi hakan domin yana neman tsaftace abubuwa da gyara abubuwa a cikin jama’a dalilin bijiro da batun bai wa kananan hukumomin damarsu ke nan, amma wasu da suke bin bayan shugaban kasa na gaskiya suke taimaka masa sun yi abun da ya fada. Don haka wasu kananan hukumomi a daidai wannan lokacin gaskiya suna cikin damuwa, kai hatta kai irin ofishin D.O-D.O din nan da aka yi da sun fi su walwala.

Ya kake kallon kudurin bai wa kananan hukumomin nan damar cin kashin kansu da kurar kin amincewa da ta biyo baya?
Ai shi ya sa a kullum na ke cewa zaban cancanta a zabi wadanda suka damu da damuwar jama’a shi ne mafita ga ci gaban kasa da talakan kasa, wannan zaben sak din nan ba karamin nakasu ya kawo wa kasa da kuma ita kanta APC da muke ta ikirarin sha bamban da jam’iyyar da muka kwace mulki a hanunta, abin da nake son na ce a nan kasancewar bakin jam’iyya guda a ma fi rinjayen majalisun jihohi da gwamnonin jihohi shi ne ya hana samar da wannan dokar ta cin kashin kan kananan hukumomi. Idan ka duba wasu jihohin ai sun yi zaben kananan hukumomi, amma wasu jihohin sun kekashe kasa sun ce ba za su yi zaben shugabanin kananan hukumomi ba, domin kada su rasa damar tursasa wa kananan hukumomin. Yau a ce kananan hukumomin nan sun samu damar cin kashin kansu jama’a da dama domin kashi sittin na jama’a a fadin jihohi na ‘yan siyasa da sauran jama’a sun raja’a ne daga kananan hukumomi, hatta canjin kudi a hanun jama’a idan babu a kananan hukumomi to babu canjin arziki a kasa. A saboda haka tashin baiwa kananan hukumomi damar cin kashin kansu din nan nakasu ne sosai wa siyasar ma gaba daya.

A matsayinka na shugaban kananan hukumomi ai su kananan hukumomi suna samun haraji (kudaden shiga) shin ba ya rike su ne?
Kananan hukumomi suna samun haraji amma ya kamata jama’a su gane cewa, akwai haraji wanda dokar kasa ya basu damar cewa wannan nasu ne na kananan hukumomi karbansu da sarrafasu dukka su za su yi kayansu, amma za su dan bayar da wani kaso wa jiha. Sannan akwai kudaden harajin da in Jiha ta tara a jiharta a ciki kashi 10 za ta bayar kananan hukumomi kamar yadda gwamnatin tarayya take baiwa wannan kason da ake zuwa domin raba wa jihohi da kananan hukumomi. Ita ma jiha idan ta tara haraji to kananan hukumomi suna da kaso kashi 10 a ciki. Amma wasu jihohin za ka tarar wannan kashi 10 na harajin da suka tara da doka ya ce su baiwa kananan hukumomi ba su basu, kuma harajin da kananan hukumomi suke tarawa an kwace an baiwa Kwararru suna tattarawa da zai kai ga jiha ta samu tsuma hanunta a ciki, wanda kuma harajin da kananan hukumomi suke samu ba hakkin jihohi ba ne, amma wasu jihohi haka suke yi suna tsuma kansu ciki don haka ne wasu jihohi zai yi matukar wuya su amince da sanya hanu kan dokar da za ta baiwa kananan hukumomin damar cin kashin kai, domin muddin kananan hukumomi ba su da cikakken iko babu abin da za su iya yi wajen shawo kan matsaloli.

Sama da shekaru 10 a jihar Bauchi ba yi zaben shugabanin kananan hukumomi ba, wasu gwamnonin na cewa babu kudin yin hakan ne ina gaskiya?
Maganar babu kudin yin hakan karya ce kawai da wasu batun tsaro dukka wadannan ana fakewa ne kawai da su, a dukkanin gwamnatocin da aka yi tun 1999 babu gwamnatocin da suka samu maguden kudade wadanda ba su ma daga cikin kasafi da aka samar musu daga wasu wurare ake samu a basu kamar wannan gwamnatin ta APC ta Buhari din nan, sun samu kudade sosai amma wasu su biya kudaden giratuti da fansho ma sun ki biya, yanzu jihohi da yawa za ka samu ba su biya ba, idan zan maka misali da jihar Bauchi yanzu kudaden da za a biya wai biliyan daya za a ke biya alhali ana maganar biliyan 27 da bakwai ko an samu meye biliyan daya zai yi?, a irin wannan raran kudaden da ake samu jihar Bauchi ta samu biliyan sha bakwai wasu suna cewa 19 yau da an biya kudaden fansho da giratuti zai taimaka wa jama’a alhali kudaden ana cirewa daga cikin kason da ake karewa, Saboda haka kamata ya yi jama’a su san meye abun yi su kuma zabi cancanta domin bin layi daya ya jefa wannan matsalar.

A jihar Bauchi shugabanin riko ne suke shugabantar kananan hukumomi haka ma a wasu jihohin, shin masu rikon kwalliya ba ta biyan kudin sabulu ne?
Ina kwalli za ta biya kudin sabulu a irin wannan? Ai duk lalacewar zababben shugaba ya fi na riko, domin idan shugaba ne wanda aka zaba akwai wasu hakkokin da doka ta shimfida da zai yi kokarin nemowa, amma idan na riko ne ba zai tabbatar da hakan ba domin daurasa aka yi. Kuma jama’an da kake mulka ba zabanka suka yi ba za ka iya cewa ni ba zaba na kuka yi ba, inda da wanda ya sanya ni aikin nan don haka zan masa biyayya. Saboda haka shugabanin riko bai cikin tsarin mulki, don haka ina neman masu ruwa da tsaki su shiga cikin lamarin nan domin a tabbatar da wannan dokar na cin kashin kan shugabanin riko.

Kana cewa Sak ta janyo rashin samun tagomashin amincewa da wannan dokar, yau da a ce an samu banbancin jam’iyyu da za a samu masu tirjiya da masu amincewa da kila a samu amincewa kan dokar ke nan?
Tabbas ma kuwa, da a ce ka mar jam’iyyu biyu ne suke tafka muhawara a tsakaninsu da za a samu natija, domin duk shugaban da yake da kishin wajensa muddin aka kawo wani abu na ci gaba to tabbas wannan shugaban zai yi wannan abun domin ci gaban jama’arsa da suka zabe shi, amma yau a ce ku ne da rinjaye amma abun da zai kawo ci gaba kun ki ba shi dama, shugaban kasan nan yana son ya ga kananan hukumomi sun samu cin kashin kai, shugaban majalisar tarayya shi ne ya fara kawo wannan kudurin a majalisa sun amince an kuma zaga da shi wasu a jihohi sun ki amincewa to meye amfanin rinjayen da ake da shi? An zo an mika kasafin kudi ga majalisun nan guda biyu, yau da rinjaye yana amfani kasafin kudi zai yi wata bakwai ba a amince da shi ba? don haka cancanta itace kawai ta dace da kasarmu duk wanda ya dace da waje shine ya dace a zaba. Hamayyar siyasa daban batu na ci gaba daban.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!