Connect with us

MAKALAR YAU

Atiku Barazanar APC

Published

on

Shekara 26 Atiku Abubakar ya yi yana neman a zabe shi don ya shugabanci Najeriya. Bai taba samun gangariyar damar takara ba sai a bana. An taba haduwa an kara a tsakanin Obasanjo da Muhammadu Buhari da Atiku a shekarar 2007, sai dai a wannan lokacin bata da armashi, karawar ta zo da sarkakiya ta siyasar irin yanayin.
Atiku gogaggen dan siyasa ne. Duk masu siyasa a yau a kasar nan ko a APC ko a PDP in dai karansu ya kai tsaiko sun taba mu’amala da shi. Yana kasuwanci na kazaman kudi, basarake ne na Fulani. Ya rike mataimakin shugaban kasa mafi karfi a Najeriya cikin shekara hudunsa na farko.Daga 1998 zuwa yau duk siyasar kasar nan da shi ake damawa.
Ba a taba samun dan siyasa mai bada kudi ba, amma da bakin jini a yankinsa kamarsa. Yana cikin mutanen da guguwar dawo da tsarin shari’ar Musulunci da ta taso daga Zamfara ta wujijjiga siyarsarsu. Wannan guguwar ce shi kuma Muhammadu Buhari ta haska shi.
Jam’iyyar PDP ta zabi Atiku a matsayin wanda zai yi mata takara da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Kuma an ayyana Peter Obi a matsayin mai rufa masa baya. PDP ta yi kyan kai, in kuma zamu fadawa kanmu gaskiya ta fuskar fitar da gwani na jam’iyyu yadda Atiku ya samu takara ya fi tsabta da yadda aka fitar da Muhammadu Buhari a APC. Shi ne sirrin jin tsit na cikin gidan PDP duk da cewa ba a taba samun irin wannan gasar ba a wata jam’iyya tun 1978.
Samun takarar Atiku shi ne abu mafi damuwa ga APC kuma mafi hadari a cikin neman tazarcen Muhammadu Buhari, ina da dalilai bakwai dana dogara da su kuma nake ganin lallai PMB da ‘yan tafiyarsa ya zama tilas a garesu da su kiyayi Atiku.
Dalili na daya shi ne: Tunda aka tsayar da Atiku, sam-sam babu masu kushe shi sai ‘yan APC da masoya Buhari. A lokacin da ya yi waccan takarar duk inda ya je kyamarsa ake yi da tsangwamarsa, mutanen gari da ‘yan jam’iyya, amma yanzu kuma rububinsa ake yi.
Dalili na biyu shi ne: a maimaikon karfin PDP ya ragu sakamakon yanayin da tsarin gwamnatin da tayi na shekara 16 ya shigar da jama’a, sai ta farfado, duk wanda aka bata wa a APC sai ya yi tsalle ya dira a PDP. Irin wannan yanayin ne ya faru a shekarar 2014 da 2015 aka karbe mulki a hannun PDP.
Dalili na uku: Atiku ya san ciki da baya na dabarun hada karfi da karfe na siyasa. A lokacin da aka bada sakamakon ya ci takara, aka kira shi ya yi jawabin karbar nauyin da aka dora masa, ba wata-wata ya ambaci sunan Obasanjo yana yi masa godiya cewa shi ne a wannan karnin ya haska shi. Kwana biyu tsakani kuma ya je ya sulhunta da shi Obasanjon a gaban malamin Kirista da Musulmi. Duk manyan kasa a cikin masu Khaki da ‘yan boko da ‘yan kasuwa da malaman addini da ‘yan siyasa da suke ja da Buhari zasu hada kafafuwansu a bayan Atiku, kaga yana da hadari.
Dalili na hudu: Atiku yana da kalmomi da hujjoji masu karfi a matsayinsa na dan takarar jam’iyyar hamayya da zai fada wa jama’a kuma su yarda, saboda a bayyane suke. Misali, tsadar abinci da tashin dala da karin kudin fetur da faruwar wasu rikice-rikice a gurare da yawa da suke haifar da kisan dan adam da garkuwa da su da asarar dukiya.
Dalili na biyar shi ne: Zuciyar masu zabe ta gamsu cewa Atiku zai iya gwabzawa da Buhari kwabo da kwabo. Suna ganin karan Atiku ya kai tsaiko, babu a inda za a layance masa ko a kudi ko a shiri ko a siyasa ko karfin halin ja da gwamnati a ciki da wajen Najeriya.
Dalili na shida shi ne: Kusan ko ina a yankunan da APC take da karfi tana cikin rigima da ba a iya warwareta ba. Ba a warware matsalar shugabancin jam’iyya ba, wasu suka fice daga gwamnoni da ‘yan majalisar dattijai da tarayya. An zo kuma an yi zaben fidda gwani a APC a gurare da yawa rikici ya kaure a tsakanin juna. Sannan kuma ga sabani ya bullo a tsakanin gwamnoni da shugaban jam’iyya. Shi kuma Atiku a sirri har ya fara kulla alaka da wadanda aka batawa kuma ‘yan rigingimun PDP na cikin gida ya shiga gaba yana warware su.
Dalili na bakwai shi ne: Bambancin da ke tsakanin PDP da APC a zabukan 2015 gaba daya kuri’a ce miliyan biyu da rabi. An yi zaben gwada kwanji a jihar da kyar APC ta karbi Ekiti da kyar Osun ta koma hannun APC da wasu gurare a Kogi da Bauchi da Katsina duk zabukan sun nuna kowane bangare tana iya fadawa hannunsa. Cike wannan gibin ba zai wahalar da PDP ba sosai in APC ta yi sakaci.
Gaskiya yana da kyau Buhari ya kalli takarar Atiku da idon basira,musamman da yake Atiku ya yi zagayen kamfen a jihohi da yawa, takararsa barazana ce kwarai Buhari, kuma sai Buhari ya tashi tsaye ya yi aiki sosai daga yau zuwa ranar zabe a duk fannoni, an yi gyare-gyare, sannan ya kai da bantensa. Amma Allah ne mafi sani.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: