Connect with us

BUDADDIYAR WASIKA

Baba Buhari, Mu Na Murna Da Tazarce

Published

on

Banbancin Buhari da Atiku tamkar banbancin sama da kasa ne, amma abu guda da su ka yi tarayya shine fafutukar neman shugabancin Nigeria. Atiku ya fara nasa hankoron ne tun a shekarar 1993, wanda bayan shekaru goma, wato a shekarar 2003 shi kuma Buhari ya fara nasa. Cikin dalilan da su ka sa Buhari ya fi Atiku samun nasarar dare kujerar shugabancin kasar shine kasancewarsa mutum mai gaskiya wanda jama’a, masoya da makiya, a 2015 su ka hakkake ba wanda zai iya ceto kasar a wannan lokaci idan ba shi ba. Alhamdu lillahi ya ceto kasar daga mawuyacin halin tsaro da tattalin arziki da kasar ta sami kanta a ciki.
Yawancin ’yan kudancin Nigeria na matukar mamakin yadda Buhari ke da magoya baya yan gani-kashe-ni a arewacin kasar da wasu sassa na Nigeria. Amma duk wanda ya san irin tasirin da gaskiya ta ke da shi a wajen al’umma, ko da su ba masu gaskiya ba ne, ba zai yi mamakin irin soyayya da biyayya da ake wa Buhari ba. Marigayi Sardaunan Sokoto ya ce “Makami mafi karfi shine gaskiya”. Gaskiyar Buhari da tsantseninsa da kuma kyamar cin hancin da rashawa ya jawo masa dimbin makiya kamar yadda a ke son sa.
Tun da Buhari ya fara takara a 2003, sai a shekarar 2015 kadai ya sami goyon bayan manyan kasar nan, musamman yan arewa. Dalilin samun wannan goyon baya bai wuce matsanancin halin tsaro da kasar ta sami kanta a ciki ba. Manyan sojoji masu ritaya, musamman kusoshin nan guda uku, wato Obasanjo, Babangida da Danjuma duk sun goya masa baya. Yan siyasa, kudu da arewa, yan kasuwa, malamai da tallakawa duk sun bi, idan banda mutanen CAN da sauran barayi na PDP da magoya bayansu.
Buhari ya sami lalitar gwamnati karkaf, yadda ko albashi ba a iya biya sai an ciwo bashin banki. Ya na hawa mulki man fetur ya yi faduwar da bai taba yi ba a tsawon shekaru. Naira ta rika hawan gwaron zabi ba kakkautawa, yadda farashi ya rika hauhawa. Nigeria ba ta taba samun kanta cikin mawuyacin halin irin wannan lokaci ba. Kai tsaye ya fara da tunkarar matsalar tsaro ta hanyar tabbatar da fara amfani da lambar asussun ajiya a banki ta BBN, abinda ya bawa jami’an tsaro damar gane wadanda ke da duk wani asusun ajiya da kuma irin hada-hadar da ke gudana a ciki. Miliyoyin mutane sun watsar da asusun ajiyar su, tare da barin biliyoyin Nairori a ciki.
Akwai banki guda da aka sami biliyan 57 ba masu shi saboda masu shi na tsoron su ce nasu ne. Wannan ne makami na farko da ya fara karya kungiyar Boko Haram, yadda su ka shiga kamfar kudade. Arewacin Nigeria ta zama filin daga yadda kowanne lungu da sako shingaye ne na sojoji yadda zirga-zirga ta zama matsala ga kowa. Nan take Buhari ya sa aka cire wadannan shingaye.
Kananan hukumomi kimanin ashirin da ke hannun yan Boko Haram wadanda su ka ayyana a karkashin daularsu, duk an kwato su, yadda mutane su ka koma garuruwansu. Sannan ya umarci rundunar tsaro ta tattara ta koma yankin arewa-maso-gabas. Ya kuma ziyarci makwabtan kasashe da fitinar ta addaba, yadda su ka hada sojojin hadin gwiwa domin yakar Boko Haram.
Aiki na farko da ya kaddamar shi ne na shirin bai wa manoma rance daga Babban Bankin kasa domin noman shinkafa a jihar Kebbi. Cikin shekaru biyu da fara wannan shiri, tare da hana shigo da shinkafa daga kasashen waje, sai gashi an daina siyen kashi 90% na shinkafa daga kasashen waje. Buhari ya kakkabe fayil-fayil na manyan ayyuka da aka yi watsi da su kamar shirin samar da wutar lantarki na Mambila wanda aka faro tun shekarar 1972. Ya kori kwangilar cuwa-cuwa ta wannan aiki wadda gwamnatin Jonathan ta bayar a kan kudi dala bilian $37.
Ya nemo sabbin yan kwangila daga China, wadanda su ka gina dam mafi girma a duniya, ya ba su aikin kan kudi dala biliyan $5.8 wato kaso daya cikin bakwai da su Jonathan su ka so su wawushe. Kafin Jonathan, shi ma Obasanjo ya ba da wannan aiki inda har aka fitar da dala miliyan $300 na fara aiki, aikin da ba a fara ba.
Wata majiyar na cewa dalilin sabani tsakinin Obasanjo da Buhari shine na kin baiwa mutanen da Obasanjo ya sake kawowa a basu wannan katafaren aiki. Idan a ka kamala wannan aiki wanda zai samar da megawatt 3050 nan da shekaru shida masu zuwa, zai samar da dubban ayyukan yi, aikace-aikacen raya kasa irinsu hanyoyi, makarantu, otal-otal, farfado da kamfuna ban da uwa-uba samar da hasken wutar lantarki da zai sa dauke wuta ya zama tarihi.
Wani katafaren aikin da ya zakulo shine na Ajaokuta wanda a halin yanzu har ta fara aiki. Wannan aiki da ya kai shekaru arba’in ana yin sa, masana’anta ce wadda za ta canza tattalin arzikin kasar fiye da yadda a ke tsammani. Layin dogo da ya taso daga Warri zuwa garin Ajaokuta ya wuce Itakpe, tu ni jirgi ya fara bin hanyar.
Sannan a kusa da wajen dai, aikin tashar jiragen ruwa ta Baro ita ma an kamala ta kuma shugaban kasa ya kaddamar da ita. Wadannan ayyuka, wato Mambila, Ajaokuta da Baro nan da yan shekaru kadan za su juya akalar tattalin arzikin Nigeria fiye da duk yadda a ke tunani.
A bangaren jirgin kasa, ban da biyan tsoffin yan fansho kudaden su, an gama titin Warri-Ajaokuta-Itakpe, da na Abuja zuwa Kaduna da na Lagos zuwa Ibadan. Sannan a hanyoyi mun ga yadda aka kusa kammala titin Lagos zuwa Ibadan da na Abuja-Kaduna-Kano. Yadda a ke wannan aikin ka san cewa ba’a taba aikin titi mai inganci a tarihin kasar nan irinsu ba. Domin bayan kankare tsohuwar kwaltar, ana zuba wata rubi biyu, yadda ko wacce guda a ciki ta ribanya wadda a ka cire.
Wadannan tituna idan an kammala su, kuma aka ci gaba da kula da su za su iya kaiwa shekara dari ana hawansu. Aikin titi mafi tsada guda daya shine wanda aka soma daga Akwanga zai bi ta Jos zuwa Bauchi har Gombe. Aikin zai lakume sama da dala biliyan $1
Hako mai a arewacin Nigeria ya tabbata, yayin da Buhari ya kaddamar da bude rijiyar mai ta farko a arewa a garin Alkaleri ta jihar Bauchi. Yankin Chadi da na Gongola da na Benue duk na da tabbacin cewa su na kwance a kan man fetur amma kasancewar siyasar mai ta duniya da ta Nigeria ta yi wa laluben mai a wadannan yankuna tarnaki.
A lokacin Obasanjo akwai Sanata na Bauchi da a ka kayar a zabe saboda nacewarsa ta ganin wancan aiki na hako mai a Alkaleri ya ci gaba duk da cewa an sami shaidar akwai shi. Gwamnatin Obasanjo ta hada kai da kamfanin da ke aiki a wajen cewa man bai isa wanda za’a hako a sami riba ba, amma sai gashi yanzu an kaddamar da rijiyar. Hatta rigingimun Boko Haram akwai wadanda ke ganin cewa akwai manakisa ta wasu kasashen waje wajen kitsa ta domin hana hakar mai ya yi tasiri a yankin.
Waje daya da gwamnatin Buhari ta gaza yin yadda a ke tsammani shine bangaren yaki da cin hanci. Shi ma ba za’a dora wa Buhari shi kadai laifi ba domin kusan kowa a kasar na da kashi a gindi, abinda ke hana aikin samun cikakkiyar nasara, musamman idan aka yi la’akari da wadanda su ka kamata su yi hukunci sun fi kowa cin hanci. Mun ga yadda Bukola Saraki (shugaban masu cin hanci na kasa) ya gurfana gaban kotu kan laifukan cin hanci amma sai gashi rana daya kotun Allah ya isa karkashi Onnoghen ta yi watsi da kararsa. Mun ga kuma yadda gwamna Ganduje aka nuna shi kuru-kuru ya na karbar daloli amma a ka yi amfani da kotu wajen hana a binciki lamarin a majalisar jiharsa.
Yayin da guguwar jirgin yakin neman zaben Buhari ke kadawa a fadin kasar nan, mun ga yadda dubun-dubatar talakawa ke tararsa a ko’ina. Duk da halin matsi da talakawa ke ciki bai hana su nuna soyayyarsu gare shi ba saboda sun yi imani da cewa mai gaskiya ne kuma ya na tare da talaka. Sabanin haka a wajen abokin takararsa ya sa babu yadda za’ayi Atiku ya ci wannan zabe.
Don haka ina taya yan Nigeria murnar mayar da Buhari kan kujerarsa cikin wannan sati mai kamawa. Ina kuma yiwa barayin kasar nan jajen tilasta musu yin murabus daga harkokin siyasar kasar nan daga wannan shekara. Umma ta gaida Aisha.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: