Connect with us

ADABI

Daga Littafin ‘Mene Ne Sanadi?’ Na Rabi’atu SK Mashi (5)

Published

on

Cigaba daga makon jiya.

Kamar yanda na fada maka, sunana Habiba, an haifeni a jahar Kaduna,
A nan iyayena suke da duk wani dangina. Mu uku ne a wurin mahaifanmu, Yayanmu Ahmad wanda ya bani kusan shekara takwas, sai ni Habiba, da kanwata Khadija, dana baiwa shekara hudu.
Iyayenmu ba wasu masu kudi bane, sai dai suna da wadata da rufin asirin Allah, duk abunda muke so suna ƙokarin su ga sun mana.
Matsala daya nake fuskanta a gidanmu, shine fifikon da ake nunamun tsakanina da kanwata Khadija, komai za’a mana, anfi mata mai kyau, ko kuma ayi mata ni ace inyi haƙuri in dauka girma, idan abu mukai sai ace nata yafi, ko laifi mukayi a tare, ni ce za’ai ma fadan. Khadija tana da fara’a da son mutane, gata da maida hankali akan karatun ta na boko dana addini, tana da son aiki ko kadan bata da kuiya. Ni kuma tun tashi na, hakanan banson zama cikin mutane, ko baki mu ka yi ji nake duk sun takura mun, ina da son jiki, ko yawo ban cika fita ba, nafi gane ma inyi kwanciya ta ina karatun littafi ko chat a waya, koda aiki aka sakamu, Khadija nake sakawa ta yi mun.
Islamiya kuwa tunda na gama secondry na daina zuwa, na dai samu na yi sauka da harda fiye da rabi, da littafan da baza’a rasa ba, daganan na daina zuwa ganin nima na fara girma, kuma duk da haka a na dukana a islamiya.
Fifikon da ake nunamun a gidanmu tsakanina da Khadija na daya daga cikin abubuwan dake azalzalar zuciyatah, Khadija ta fini kyau, ta fini biyayya, ta fini tsoran zuciya, ta fi ni son karatu, da sauran abubuwa dai, don duk yanda zan dage inyi aiki a gidanmu ba’a yabawa, sai dai in Khadija ce ta yi, Yayanmu Ahmad, yayi aure, yana da Matarsa daya Aunty Zainab, da yaransu biyu. Sun hadu da matarsa ne a Unibersity dake kasar Dubai, tare su kai karatu har suka kare, Iyayen Aunty Zainab masu kudi ne sosai, idan nace sosai ina nufin mahaukatan kudinnan da bansan yanda zan misalta ma ka yawansu ba, shima Yayanmu ya samu zuwanta ne sanadiyyar Schorlarship din daya samu.
Kafin auren Aunty Zainab da Yayanmu, tasha gwagwarmaya sosai, rufe idanu ta yi ta nuna duk duniya babu wanda take so sai shi, su kuma sun dage a kan ba za ta aura talaka ba, Ummin mu ma da farko kin amincewa ta yi da maganar auren, saboda gudun wulakanci, Anma Aunty Zainab ta dage da nuna mishi soyayya, tana kuma kula da Ummi, a wata sai tazo gidanmu sau biyu, kuma duk zuwan da zatayi, sai tayo mana tsaraba mai tarin yawa, ta zauna musha yinin mu, har girki da shara take taya Ummi.
Da kyar suka samu amincewar iyayensu, har suka yarda da auren, anma da sharadin Yayanmu zai koma can Abuja da zama, harma mahaifinta ya ba shi rikon daya daga cikin kamfanoninsa, Ummi ma ba shiri ta sauka, ganin kirkin Aunty Zainab da kuma soyayyar da take nuna ma Yayanmu. Ina da kawata guda ɗaya mai suna Fateema, mun shaku sosai, kusan kowanne lokaci tana gidanmu, duk inda zamuje a tare ne, koda dinki za mu yi, kala ɗaya mukeyi, Ummin mu ta zama tamkar Maminsu, haka ni ma har mun fi shiri da Maminsu akan Ummi na, bani da kawar shawara kaman Fateema, don ko kanwata Khadija bamu shaku da ita kaman yanda muka Shaku da Fateema ba.
Duk kawancenmu, sai dai halinmu ne baizo daya ba, Fateema akwai ta da son samari, da kuma son abun hannunsu, ta iya soyayya da jan hankalin saurayi, don duk saurayin da ya mata a ranta, tasan yanda zata bi ta samu soyayyarshi.
Saurayi daya nake kulawa mai suna Yusuf, ba shine first lobe dina ba, anma dai shine saurayin dana fara yima zazzafar soyayya, ina masifar son Yusuf, duk wani na tare dani ya sani, yana da wahala na zauna da mutum ban mishi firarsa ba, kaman yanda shima duk wani wanda ya san shi, yasan yanda yake sona,
Shekararmu daya da fara soyayya, iyaye suka shiga cikin maganar, ina nufin aka kawo kudin aike.
Dukkan wadannan mutanen dana maka bayaninsu, dama wanda zan maka bayaninsu anan gaba, sune SANADIN shigata wannan halin da nake ciki a yanzu, sune SANADIN tarwatsewar duk wani farin ciki na rayuwata, sune SANADIN da gaba ɗaya rayuwarnan tafi a raina.
“Ki na tufin hardaa iyayen naki?”
Ya tambayeta cikin zakuwa,”A hankali zakaji komai”
Ina kwance a daki, kallo nake a wayata da earpiece a kunne na, na kure karar sosai, ban ji shigowarta ba, sai dai na ganta tsaye a kaina,
“Me kikeyi tun dazu nake kwala miki kira anma kin gagara amsawa?”
“Yi hakuri Ummi, banji ba wallahi, earpiece ne a kunnena” na ba ta amsa bayan na mike zaune.
“Yau dai baiwar taki tana makaranta, ki tashi maza kije ki daura girki har rana tayi”
“To Ummi”
“Ki tashi yanzu fa”
Na kara binta da to, harta fice, n
Na jawo wayata, naci gaba da kallo na, saboda yanda film din ya dauka hankali na, sauran kiris in karasa, ga fi*** ina ji ya matse ni, anma koshi na kasa tashi inje inyi,
Ina kashe kallon naji Ummi ta kara kwallamin kira, “wai Habiba bazaki fito kimun girkinnan ba?” “Ganinan Ummi yanzu zan fito”
Na aje wayar da gudu na shige toilet din dake dakinmu, saboda yanda fi****n ya matseni sosai, na gama na fito, sannan ta tafi inda zan taya Ummi girki.
A kitchen na tarar da ita, harta kunna risho din, ta dauko tukunya zataje debo ruwa, na tare ta zan ansa, ta dakatar dani da hannu.
Na kara matsawa, “ki kawo in debo Ummi, wallahi toilet na shiga ne”
“kinga ki matsa ki bani wuri, girkin ne zai gagareni? Tun yaushe nake miki magana ki fito anma kinki”
“Ki yi Haƙuri don Allah Ummi”
“Ai kullum cikin yinsa nake, ki matsa ki bani wuri, koma kici gaba da kwanciyarki har sarkin kwanciya ya tarar dake, girkin ne zai gagareni, don ma Khadija batanan ai da bama sai na sakata ba zan fito in tarar da ita ta gama”
“Ni dai kiyi hakuri Ummi”
“Ki matsa ki bani wuri nace ko? Ai bawai yau kika fara ba, in da sabo na saba da halinki Habiba”
Ta raba ta gefena ta wuce tana ta fada, ba tayi shiru ba har na koma dakinmu, a can dinma data tuna sai tayi ita kadai a tsakar gida.
Can wuraren la’asar, ina a kwance, na fara jin yunwa, a gabana Khadija ta shigo da nata, ta zauna ta ci, tayi shirin islamiya ta tafi.
Na tashi naje kitchen ina ta bude kuloli babu abinci, na tafi dakin Ummi lokacin Abba ya dawo, na tsaya daga bakin kofa sai haɗe rai nake, na kalleta ta kauda kai.
“Ummi ina abincina?”
Ta dago cikin takaici tana kallona, “lallai yarinyarnan baki da kunya, in saka ki girkin ki kiyi, sannan ki saka ran in ajje miki? Ban girka dake ba, idan kin matsu ki je ki girka”
“Ummi yanzu har ayi girki baza’a bani ba?”
“Ba za a baki din ba, ai kinsan inda kayan abincin suke, sai ki je ki girka”
A gaban Abbanmu takemun wannan fadan, sai lokacin ya dago yamun magana,
“Baki kyautawa Uwata, ki daure ki rage kuiyarnan taki kinji, ki na dai ganin yanda kanwarki ta ke yi”
Kanwata dai, Khadija dai, babu yanda zasumin fada ba tare da sako sunanta ba. Na juyawata kawai na tafi, don nasan tunda tace ba za ta ba ni ba, to fa bazanci abincin ba.
Dakinmu na koma, na dauko cikin kayan ciye-ciyen da Yusuf ke kawo mun, wani babban biscuit mai dadi, shi naci kawai nasha ruwa, na kwanta naci gaba da Chat.
Sallamar Fateema na jiyo can tsakar gida, sai da ta biya ta gaishe da su Ummi, sannan ta shigo dakinmu,
“Matarnan kina jin dadinki fa, sai wani kiba kike karawa” ta ce mun lokacin da take neman wurin zama, a bakin gadon da na ke kwance,
Tashi nayi daga kwanciyar, nima na zauna, “wanne kiba zanyi Sahibi bai garin? Ban son sharri fa”
“Allah da gaske nake miki”
“Lallai kam, ina zaki je haka?”
“Kin masan fita zanyi kenan? Tashi zaki mu tafi, Mami ta aikeni kasuwa”
“Shi ne ki ka zo takura mun? Don dai aiken Mami ne da babu inda zanje”
“Na ji dai, sai ki tashi mu tafi”
Ta karbe wayar da nake chat da ita,
“Ki tashi ki shirya, halan My ɗin namu na Online ne?”
“Ehh mana, sai ki faɗa mishi kinzo fitar dani cikin ranar nan”
Na shiga toilet na dauraye kafafuwana kawai, daman nayi wanka, kuiya ta hanani shafa mai, ba wata kwalliya nayi ba, mai da powder kawai na shafa, na zira Hijab dina muka fito,
Dakin Ummi na shiga, ita kadai na tarar Abba ya fita,
“Ummi zanje raka Fateema kasuwa, Maminsu ta aikemu”
Ta kauda kai kawai alamun har lokacin fushi take dani,
“Kin ji Ummi” na kara mata magana cikin sanyin murya,
Ba tare data kalleni ba ta ce, “a dawo lafiya”
Jikina a sanyaye nabi Fatima muka tafi.
Mu na fita sai ga wayar Yusuf, tana Hannun Fatima ta miƙmkomun, “kin ga daga saukar ki harya kira”
“Saukarmun kikai kenan? Da kin barni muna tafiya ma ina fira da masoyi na”
Na karashe maganar ina daga wayar,
“Ya dai ko harkun tafi?”
“Mun fita daga gida yanzunnan”
“Gaskia Fatima bata kyautamun ba, zata fitarmun dake cikin ranar nan”
“Wallahi fa, kuma kaga a gajiye nake”
“Ayyah! Sannu kinji er lelena, ki fada ma Fatima ta kulamin dake”
“Ga ta dai ka fada mata da kanka”
Na mika mata wayar, dariya kawai take mishi bana jin abinda ya ke fada mata,
“Kar ka damu nima inaji da Habibatin nan tawa, sosai nake kula da ita”
“Ai duk wanda zai kalleta ma, nice nan zan shigar maka yakin, duk da kasan itama bazata bayar da fuska ba”
“Yauwa dai, gata bara na bata, don nasan kawaici kawai a ke mun, dukka matsu da kaci gaba da sauraren muryarta”
Ta miko mun wayar bayan sun gama,
“Ina sonki da yawa Habibatee, idan har waya dake kawai na sa ka ni yini cikin farin ciki ya koremun duk wata damuwa, ina ga lokacin da zaki zama mallakina? Don Allah ki kasance dani Habibatee, karki barni cikin kewarki koda na dakika daya”
Wani murmushin jin dadi na ke, saboda yanda kalamansa ke ratsa zuciyatah, farin ciki ya mamaye kowacce gaba dake jikina
“Ni taka ce My zan kasance da kai a kowanne yanayi, ina jin dadin soyayyar da kakemun”
“Ai baki ga komai ba, don duk ranar da kika shiga gidana, zaki zama ‘yar gata, mace mafi soyuwa a wurin mijinta.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!