Connect with us

ADABI

Munafurci A Tsakanin Marubuta Ya Yi Yawa –Saifullahi

Published

on

Matashin marubuci Saifullahi Lawan Imam, ya fadi haka ne a cikin doguwar hirar da suka yi da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, ADAMU YUSUF INDABO, hirar da mu ka soma kawo muku ita makon da ya gabata. Ga cigaban hirar:

Cigaba daga makon jiya

Ke nan online writers na da matsala?
Matsaloli ma, saboda online writer fa da kake gani suna da mugun girman kai fiye da mu marubutan gidi, saboda jagwalgwala rubutu kawai su ke yi ba tare da sun ma fahimci mece ce Hausar ba, don ba a taba yin lokacin da ake cin mutuncin rubutun Hausa da keta haddin ka’idojin rubutu irin na online writers ba. Idan suka yi wata kwabar Hausar. Wallahi ba zata karantu ba.
Su dai kawai su rubuta su watsa su burge ba ma tare da sun san don me ake rubutun ba, sai kuma zamowa da online writers suka yi a matsalin matsala kuma kadangaren bakin tulu ga marubuta, domin zan iya cewa suna daga cikin kanwa uwar gami na kashe kasuwar littafi da durkushewarta, saboda yanda suke rubuta a media ba ji ba gani, ya sa yanzu makaranta suka raja’a ga karatu a media, musamman gidajen wattpad, wordpress, okada, da sauran su. Sannan girman kai ba zai sa su tambayi abu ba, ba zasu koyi yanda ake amfani da ka’idojin rubutu ba, sannan ba za su yi biyayya a koya musu yanda a ke raba kalmomi da hadewa ba, da saka kalmomi inda suka dace ba, sai ma daukar kansu da za su rinkayi daidai da kowanne marubuci ko marubuciya.
Na ji wata tsagerar online writer da ta taba hura hancin cewa wallahi ko Maimuna Beli da Aunty Fauza da Asma’u Lamido ba za su nuna mata komai ba. Wacce ta yi wannan maganar fa ko watanni biyu cikakku bata yi da fara rubutu a online ba, shi ya sa nake jinjinawa marubutan online irinsu Amrah Auwal Mashi, Rufaida Omar, Ummyter Bingel, Rabi’at SK Mashi, Zulaihat Rano, Ummyn Yusrah, har gobe wasunsu suna turo mana labarinsu mu gyara musu da saita musu ka’idojin rubutu, sannan har gobe suna neman shawararmu da tambaya a kan wani labarinsu, sannan labaransu na da matukar inganci da salo mai kyau, saboda suna da biyayya da kwantar da kai ba irin su inna wuro ba masu ganin kansu warki daidai da kugun kowa. Don haka matsala da hatsari da tawayar da marubutan online ke kawowa harshen Hausa gaskiya suna da yawa wanda idan ba a dau mataki ba, online writer za su ci gaba da durkusar da harshen Hausa da zamewa marubuta kadangaren bakin tulu.

Ya batun rubutun fim, ko na zube kawai kake yi?
Ai kuwa ina rubutun film sosai ma, a takaice ni ma guguwar rubutun film ta ja ni kuma babu shiri na nade kafar wando na bi ta a guje, saboda idan ka ji haya haya to samu ne hhhh.

To me yake sawa marubutan zube komawa rubutun fim?
Dalili daya ya sa kasuwar adabin kano ta yi wa marubuta saki uku har suka kama kaura zuwa ga sabon aure wato film shine, misali idan ka auri mace aikinta ta rinka,kyautata maka tana maka biyayya tare da yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta faranta maka rai, amma duk wadannan ababen kai ba ka gani, kullum sai hantara da cin kashi da wulakanci, hadi da tozarta matar da kake yi, to saboda Allah ka gaya mun idan tura takai matar bango kasan dole ta nemi sauyin rayuwa ta hanyar neman rabuwa da kai koda kuwa kai ne autan maza. Wannan ne dalilin da ya sa marubuta ke kauracewa zuwa film don samun sabon angon da zai iya da bukatu da walwalarsu, kuma ga shi kwalliya na biyan kudin sabulu.

Ke nan dai an fi samu da gwabi a rubutun fim fiye da rububun littafi?
To kamar haka ne, saboda gaskiya babu marubucin film din dake korafin ba ya jan kaya a harkar film, sai dai dan abun da ba a rasa ba na hawan kawara daga wasu produsoshi.

Kamar ya hawan kawara?
Wasu produsoshin sun fi ‘yan kasuwar littafi hatsari da mugunta, domin za ka ba su labarin film su rike maka kudi kwata kwata, ko su dan baka kamar dubu goma,sauran sai illah masha Allah, saboda suna tunanin taimaka maka suke yi,ba kai ke taimaka musu ba, ina tabbatar maka babu inda ake daukar maeubuci a banzance a wulakance irin kannywood, saboda tsabar wulakanci za a iya biyan mace yar rawa dubu hamsin kai ba a ba ka dubu goma ba, abubuwa da yawa, amma duk da wadannan ababen akwai produsoshi masu mutunci da ba sa rike kudin marubuci komai yawanshi, amma kalilan ne.

To duba da kasancewarka marubucin da ya tsallaka duniyar fina-finai, ya kake ganin matsayin marubuta a idanun yan fim?
Ai kamar yanda na fada maka ne, marubuta basu da wani kima ko matsayi a idanun yan film, su ma wadanda, suka kafu suka samu gindin zama irinsu birniwa, nafseen, maje, NAS, shafiu giwa, inka duba zaka ga jajircewa da kwarewa da hakuri da sukayi yasa suka zama abunda suka zama ayau,amma anfi fifita mata yan rawa akan marubuta a film,akwai wata jaruma da ta kusa marina saboda kawai na yi mata gyara akan wani abu da ta fada wanda ba shi ke rubuce a script din ba,ire iren wannan abubuwa na faruwa musamman ga sababbin marubutan film.

Ke nan dai marubuta sun zama tamkar ‘yan Allah ba ku mu samu a gun yan fim?
Yauwa kamar haka ne, saboda tamkar karen da ake kora kullum ne amma rashin zuciya ke saka shi dawowa, sai dai daga karshe karen na samun gindin zama da kulawa idan aka gaji da koranshi, a fara kulawa da shi da ba shi abinci.

To rubutacciyar waka fa?
Ai nan ma na fi kauri, saboda rubutun waka wannan tamkar a jinina ya ke, domin waka ba ta taba ba ni wahala ba, a duk sanda na so na rubuta ta ko na rero ta, to zan yi ba tare da wata mishkila ba. Zan iya ce maka na fi kwarewa a rubutun waka fiye da ko wanne rubutun adabi.

Cikin rubutun fim da waka kana amfani da salonka na adabin bariki ko a zube kawai kake amfani da shi?
A rubutun zube kawai nake amfanin da salon adabin bariki, sai film da na ke dan sofanawa da kadan kadan kamar yanda ake jefa dan wake a tukunya hhhh.

Ko kana da sako ga masoyanka da suke bibiyar rubuce-rubucenka?
Sakona ga masoyana shi ne ina alfahari da su a duk inda suke, kuma ina musu fatan alheri, Allah ya bar zumunci, a duk inda suke ina son su kamar yanda suke sona, na gode da soyayyarsu a gare ni.

Wanne kira za ka yi ga yan uwanka marubuta da kuma makaranta baki daya?
Ina kira ga yan uwana marubuta da su yi wa Allah su cire bakin ciki da hassada da ganin kyashi a tsakanninsu, domin wadannan ababen ne ke kawo mana rabuwar kawuna da fada da juna, har ga shi muna nan a rarrabe kamar kwayoyin gero. Mu daure mu hada kai tafiya daya da murya daya, za mu ci gaba kuma mu ga amfanin rubutu, sannan darajarmu da kimarmu za su dawo idan muna hade. Ga makaranta kuma masu bibbiyarmu, su cigaba da juriyar kara mana kwarin gwiwa, idan sun ga inda muka yi kuskure don Allah su gaya mana ba zagi da bakaken maganganu ba. Allah ya taimake mu.

To a karshe me Malam Saifullahi zai ce game da wannan jarida mai tarin albarka ta Leadership A Yau Lahadi?
Wannan mashahuriyar jaridar ta leadership hausa tabbass ta fita zakka kuma ta tserewa tsara wajen zamowarta jaridar Hausa ta farko mai fitowa a kullum, tabbas abun alfahari ne a samu irin wannan jaridar a harshen Hausa, ina Rokon Allah ya ci gaba da ba wannan jaridar nasara da ci gaba ameen nagode da wannan damar da kuka ba ni.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: