Connect with us

RA'AYINMU

Najeriya 2019: Wasika Zuwa Ga Malam Talaka

Published

on

Kamar yadda mu ka saba fada, a yau ma za mu nanata wa Malam Talaka ne cewa, bai kamata ya bari wani ya samar ma sa da makomarsa ba. Hakika kai ne ka fi kowa cancanta dacewar ka samar wa kanka da makoma, domin kuskure dan kankani zai iya a wannan zabe da a ke daf da gudanarwa a 2019 ya janyo ma ka mummunan karshe, sannan ya haddasa wa ’ya’yanka da jikokinka mummunar makoma.
Ka sani cewa, wannan zabe da ke tafe za a yi shi ne domin a samar da sababbin jagorori a Najeriya, wadanda za su sa ko su hana a duk manufa da aiwatarwa a kasar. Don haka shugabannin da za a zabe su na da matukar muhimmanci a gare ka.
Ka tuna cewa, akwai muhimman abubuwa wadanda su ke a tsaye cak a halin yanzu da a ke jiran yiwuwarsu ko akasin hakan bayan an rantsar da sabuwar gwamnati. Misalai a nan su ne, sabuwar dokar zabe wacce tilas nan gaba maganarta za ta dawo kuma shugabannin da a ka zaba su ne za su wanzar ko kin wanzar da ita.
Akwai rikicin majalisar dokoki da bangaren zartarwa, wanda a ka shafe shekaru hudu a na yin dambarwarsa. Shin Malam Talaka za ka saisaita ruruwar wannan wutar ne ta hanyar samar da wakilai nagari da shugabannin nagari ko kuwa za ka bari abubuwa su cigaba da tafiya a yadda su ke a halin yanzu?
Akwai kuma maganar karin albashi. Ita ma duk yadda a ke ta kai ruwa rana, a kai gwauro a kai mari a kanta, ba za a iya warwarewa kuma a aiwatar da ita kafin zaben nan ba. Don haka makomar batun albashi mafi karanci shi ma ya dogara ne ga yadda kai Malam Talaka ka zafi sababbin shugabanni a wannan zabe da ke tafe, domin su ne za su tabbatar da yiwuwa ko akasin hakan.
Ga batun yajin aikin malaman jami’a, wadanda su ka shafe watanni su na yin sa; lamarin da ya janyo dimbin matasan Najeriya masu tasowa zaman kashe wando a gida tsawon watanni, inda makomarsu ta ke cikin halin ha’ula’i.
Akwai kuma batun tsaro. Shi ma muhimmin gaske ne. Kungiyar Boko Haram ta na cigaba da yunkurin kawo bara a na dakile ta, sannan kuma wasu miyagu su na can su na yin garkuwa da mutane su na amsar kudin diyyar fansa. Hakazalika rikicin manoma da makiya da na kabilanci ya na cigaba da wakana a sassan daban-daban na kasar, musamman a yankin Arewa, wanda shi ne mafi yawan jama’a a Najeriya.
Ba wai mu na nufin mu nuna gazawar gwamnati mai ci ba ne kuma mu na so mu ce, idan a ka zabi wata gwamnatin daban za ta iya maganta matsalar ba ne fiye da yadda mai ci ayanzu ta ke yi, a’a, abinda mu ke nufi shi ne, shi Malam Talaka ya tsaya ya yiwa kansa karatun ta-nutsu ya tankade ya rairaye ya duba ya ga mene ne bambancin kwaya da tsakuwa.
Kada ya manta da cewa, a 2015 ya damu da yadda matsaloli su ka dabaibaye kasar ne, shi ya sa ya kawar da waccan gwamnatin ya kawo wannan bisa fatan cewa, matsalolin da a ke da fama da su za su kau. To, sai ya tsaya ya yi tunanin ta-nutsu ya gani cewa, shin a yanzu burinsa ya cika ko kuwa a’a bai cika ba? Shin idan ya kawar da wannan gwamnatin, wacce zai zabo, za ta iya cika ma sa buri kuwa?
Dole ne Malam Talaka ya tsaya ya yiwa kansa wadannan tambayoyi ya gani a ina masalaharsa da ta kasar ta ke. Kada ya kalli muradin shugabannin na hawa mulki ko zarcewa; ya fara duban kansa da kasarsa tukunna. A ina a ka samu matsala kuma wa ke da ikon maganta matsalar? Ita ce tambayar da ta fi dacewa Malam Talaka ya yiwa kansa.
Malam Talaka, ka bar batun jam’iyya ko bautar mutum. Ka koma ka yiwa kanka tunanin dalilin da ya sa ka ke son kowanne dan takara da dalilin da ya sa ka ke kin kowane dan takara. Idan har ba ka hujja ta zahiri a so ko kin wani dan takara, to ka watsar da wannan ra’ayi ka koma tafarkin da zai fisshe ka, domin su ma ’yan takarar dukkanninsu su na yin abinda su ka ga zai kai ga gaci ne. Kai ina naka gacin, Malam Talaka?
Mu na fata za a yi zabe cikin hankali da hangen nesa, kuma a kammala cikin zaman lafiya da nutsuwa. Allah ya ba mu shugabanni nagari, wadanda za su za su kai mu da kasarmu ga gaci! Amin summa amin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!