Connect with us

MANYAN LABARAI

Yanzu Babu Zaman Lafiya A Arewa Sai Kudu – Shugaban Kungiyar Matasan Arewa

Published

on

•Kungiyar Tuntuba Ta Matasan Arewa Ta Ce Ba Za A Sake Yaudarar Su Ba

Zakakuri kuma jarumin matashin nan a Arewacin Najeriya, YERIMA USMAN SHETTIMA, wanda shi ne shugaban kungiyar Tuntuba Ta Matasan Arewa, wato Arewa Youth Consultatibe Forum (AYCF), ya bayyana matsayinsu kan zaben 2019 da dalilansu na juya wa shugaban Nejariya Muhammadu Buhari baya, duk da cewa, a su na cikin wadanda su ka yi ruwa su ka yi tsaki a zaben 2015 su ka kifar da gwamnatin PDP a karkashin jagorancin Goodlcuk Ebele Jonathan. Ga dai yadda tattaunawar Yerima Shettima da Editan LEDERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO ta kasance:

A 2015 kun yi aiki tukuru, don ganin kun kawar da gwamnati tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Bayan kun kafa gwamnati a karkashin mulkin Shugaba Buhari, shin burinku ya cika kuma ya ku ke kallon ta a halin yanzu da ta shekara kusan hudu?
Shi duk mai rai ya na tare da buri da zato da tunanin alheri, musamman abinda ya shafi al’umma da kasa gabakidaya. Gwagwarmaya da mu ka yi a 2015, don mu tabbatar da cewa an kifar da waccan gwamnati ta Jonathan, mun yi zaton babakeren da gwamnatin ta ke yi ta wurin fannin cin hanci da rashawa, rashin adalci da wadansu abubuwan, ga yadda mu ka taso mu na yara da labarin da mu ke samu a kan Janar Muhammadu Buhari, ga yadda kuma mutane su ka nuna ma na, iyaye da ‘yan uwa da abokan tafiyarsa, cewa mutum ne mai adalci da tausayi, mai kuma haramta duk inda ya ga za a yi cuta, sai ya ga inda karfinsa ya kare. Jin hakan ya sa mu ka yi zaton cewa, idan mu ka kife wancan (Jonathan) mu ka kawo shi (Buhari) mu na kyautata zaton cewa abubuwa za su gyaru. Kar ka manta, duk abinda ya ke faruwa kusan mu (matasa) ne mu ke cikin tsaka mai wuya. Mutane irinsu Buhari da sauransu sun riga sun yi nisa, amma mu mu na zaton cewa akwai abinda za mu iya tsinta daga rayuwarsu mu yi koyi da shi, don mu ga yadda za mu iya rike kasa gabakidaya a samu cigaba. To, sai a ka samu akasin haka bayan an yi zabe, bayan mun sadaukar da kanmu, bayan barazana da a ka yi wa rayuwarmu da abubuwa na gwagwarmaya mu ka tabbatar mun kifar da gwamnatin da ta ke kai, wanda ba a taba yin wannan tarihin a kasar Najeriya ba, sai wannan lokaci.

To, kamar meye gwamnatin ta ke yi wanda a yanzu ku ke ganin ba a kan daidai ta ke ba?
Cin hanci da rashawa, zakinci, rashin adalci da shugabanci nagari. Kusan abinda mu ka yi gudun sa a wancan zamani, to wannan karon sai ya ninka abinda mu ka baro baya… Yau duk satar da ka yi da halin babakere, idan kai mamba ne na (jam’iyyar) APC, gwamnati ta na yi da kai, Buhari ya na son ka, ba za a bincike ka ba. Idan ka na so sai na ba ka misali da Kano, Abba Kyari da sauransu. Duk ga su nan face-face an same su. Babachir ma da na ga a na wani barazana a na wani abu, saboda matsin-lamba ya yi yawa su na so su yi amfani da damar su nuna wa duniya a na wani abu, amma mu mun san cewa babu inda za a je. Shirme ne kawai! Don haka wadannan abubuwa ne su ka sa mu ka haramta gwamnatin baya mu ka yake ta, mu ka kawo gwamnatin Janar Muhammadu Buhari, kuma duk wanda ya ke zaton za a yi wani abu da ya na baya, sai wannan ya zo ta tabarbare.

Amma su na maganar a harkar tsaro an samu cigaba.
Kai mutumin Arewa ne da ka ke min wannan magana, Nasiru. Kai ka san halin da Arewa ta samu kanta a yau a harkar tsaro, kai ka san halin da Najeriya ta samu kanta yau. Ko da gwamnatin Jonathan ta tafi akwai wasu kauyuka ne kadan a guraren Maiduguri wadanda a lokacin da za a yi zabe saboda harkokin tsaro, sai da wanda ya ke kula da harkar tsaro, Sambo Dasuki, (a lokacin) ya nemi a kara sati biyu zuwa uku, don a samu a kaddamar da zabe kuma a ka yi hakan har Buhari ya samu kuri’a masu kyau daga yankin na Arewa maso Gabas.
Yau ka duba Allah ka ga halin da Arewa ta samu kanta. Yau ba maganar Maiduguri mu ke yi ba, yau mu na maganar Adamawa, mu na maganar Yobe, mu na maganar Zamfara, mu na maganar Birnin Gwari a Kaduna, mu na maganar Taraba, Binuwe, Jos. Ko’ina babu inda a ke zaman lafiya a kasar nan. Inda a ke zaman lafiya a kasar nan sai dai Kudu. Arewa gabakidaya ba ta da lafiya. Yau ba maganar Boko Haram, ba maganar bom ba, ka na zaune a gidanka za a zo a dauke ka da iyalinka, yau fashi da wasu abubuwa sun yi kamari.
Tabbas bincike ya nuna babu yadda za a yi a shawo kan matsalar tsaro idan mutane su na cikin halin kunci. Yau taken wannan gwamnati shi ne yunwa da kunci da wahala da ta saka talaka a ciki. Wadanda su manyan ne su na da hali, su kullum samu su ke yi su na cigaba. Talaka kuma shi ne ya zama karen farauta a cikin wannan tsari. Saboda haka babu yadda za a yi a ce kuma wannan matsala ta tsaro ta samu nasara da irin wadannan abubuwa.
Da ma taken yakin neman zaben Buhari shi ne yaki da cin hanci da rashawa, tsaro da kuma habaka tattalin arziki na kasa gabakidaya, musamman Arewa. To, sai na tambaye ka, a yau a banza a yadda kididdiga ta nuna ayyuka da a ka rasa ya kai miliyan 180. Ka duba kuma a ma’aikatun nan da a ke magana a ka kirkiro na wanda a ka rusa ta yau mutane nawa a ka dauka..? Kai yau ban san abu guda daya da za ka nuna min wanda ya ke aiki. Hatta maganar tsari na ilimi a Najeriya yau ya tabarbare a Arewa.

Amma za su ce a kwana-kwanan nan Shugaba Buhari ya je ya bude rijiyar mai ta farko a Arewa a Bauchi.
Shi wannan sai kamar da shi ya zama wani abu da za ka iya kamfen da shi a kansa? Mai da a na iya samun sa a ko’ina! Don ya kaddamar sai me? Shi me ya kawo?

Amma ba ka ga gwamnatocin baya sun gaza hako shi ba?
Wannan ba gaskiya ba ne. Ko kafin ya zo da ma an haka rijiyar. Gwamnatin nan babu wani abu guda daya da za ka ce ita ce ta kirkiro shi ya tabbata. Duk abinda ka gani an riga an yi shi su ka karasa. Da ma ita gwamnati ai ba kayan mutum na kashin kansa ba ne.

Ka na nufin hatta harkar jirgin kasa da gwamnati Buhari ta kaddamar ba ita ce ta kirkira?
Har jirgin kasan ai ba shirin Buhari ba ne. Jonathan ne. Da ma can an riga an kare aikin kafin a samu wannan matsalar har a ka dakatar a ka samu canjin gwamnati su kuma su ka zo. Budewa su ka yi kawai, saboda an riga an kare. To, saboda haka babu daya da su ka yi.

To, tunda ku na ganin an samu matsala da wannan gwamnati ta Buhari, wane mataki ku ka dauka na ganin kun mara wa wani baya?
Ai saboda halin da mu ka samu kanmu yanzu na halin kunci da wahala da kowa ya galabaita, jiki magayi, kowa ya farga, ba mu da zabi, saboda kowa ya kalli tsari na wannan gwamnati ka san cewa ba su da tunani na yin wani abu da za su taimaka wa kowa. Saboda haka mu yanzu ba mu da wani tunani sai mu ga cewa na kifar da wannan gwamnati an kawo ma na wata sabuwar gwamnatin.

A karkashin wa?
A karkashin PDP, wato Atiku… Yauwa…

To, ba ka jin cewa a na kallon shi Wazirin Adamawa a matsayin mutum in da ya ke daurewa rashawa gindi har a ke zargin ya arzurta kansa da lokacin da ya samu dama a gwamnati?
Ya na da kyau ’yan Najeriya su yi ma sa adalci. Idan a ka a na zargin mutum da wani abu, sai a kawo hujja. Har yanzu da na ke yi ma ka magana, wai-wai-wai ne! Kai ka san cewa wannan gwamnati yadda ta ke ganin ya na yi ma ta barazana, ta na ganin cewa ya na da damar da zai iya kife su, idan su na da wani abu, komai kankantar sa, za su iya kife shi da shi su kama shi su yi ma sa wulakanci. Ko daya babu! Sun ce ba zai je Amerika ba; babu abinda ba a fada ba, wai da klaifi da wane ne, mu mun goyi gayan ma kar ya je din, saboda zuwan Muhammadu Buhari Turai din babu abinda ya kawo ma na ko kwaya daya in banda asara. Mu mun goyi bayan shugaban kasar da ma zai ki tafiya Amerika ya zauna a nan ya yi ma na aiki a gida, a ka matsa-a ka matsa, haka ya debi jiki da iyalansa da abokan aikinsa da kuma wasu manya na PDP su ka je Amerikan. Shi ma a ka ce ai kafin ya dawo akwai rigima a kasa, akwai wai wani zargi da a ke yi ma sa.
Ko da ya je ka samu labarin an kira shi ya zo ya amsa wasu a kan wani abu da a ke zargin sa a kai? To, saboda haka yakamata mu dawo daga irin wannan abin da irin wannan tunnain na kauyanci da babakere da sharri da a ke nema a yi. idan mutum ya na da wata hujja ya kawo ya kafa ta. Ga zabe nan tafe ya kusa kuma ga shi mu na cikin tsakiya har yanzu ba mu ga abu daya da a ka yi ba. Saboda haka wannan zato ne; zato kuma aikin banza ne.

To, a na zargin cewa shi Atiku Abubakar ya na da kudi da yawa wanda zai iya sayen ku matasa ku mara ma sa baya.
Ka ce a na zato. Idan dai zato ne, ya zama maganar banza… Duk wanda ya bi tarihina ya san ba irin wanda za a saya ba ne. Ina da rufin asirina iya gwargwado. Na fi karfin a saye ni. Duk wanda ya san ni shekara 19 zuwa 20 ya san gwagwarmaya kawai na sa a gaba na ke yi. Ina da sana’ar da na ke yi, amma kuma duk wanda ya san ni ya san ni da gwagwarmaya. Duk kyanka, idan na same ka da laifi na ka yi wani abu wanda ba daidai ba, ko daga ina ka fito, Allah ya ba ni wannan karfin zuciyar da zan fuskance ka na gaya ma ka cewa wannan ba daidai ba ne, saboda ni na farko na san asalin da na fito, na san mene ne talauci, na kuma samu na samu dama na zauna da manya, na kuma fahimci mene ne babakere daga kasa har sama. Ni gogaggen mutum ne. Saboda haka na fi karfin a saye ni. Akidata ce, ra’ayina ne.
Gudunmawar da mu ka ba wa Buhari mu ka kifar da Jonathan a zaben 2015, shi Buhari ya na da kudin da ya saye ni? Kuma don me yanzu don mun canja ra’ayi mun ce ba a yi ma na adalci ba, za a ce sayen mu a ka yi? Kowa ya san cewa ba a yi adalci ba. Kusan duk matsaloli na rashin adalci a gwamnatin nan ya kare kan Arewa. Ita gwamnatin nan kullum ba ta da tunanin da ya wuce ta ga bayan wadanda su ke tasowa matasa na Arewa ko kuwa wadansu wadanda a ke tunanin za su iya bada alkibla na shugabanci a gaba a karya su. Ga Kudun nan babu abinda ta yiwa Kudun…

Amma fa Shugaba Buhari ya sa hannu a kan dokar bai wa matasa dama su tsaya zabe.
Ai ba mu bukatar ya sa ma na hannu; doka ta ba mu dama. Wannna wani ganin ido ne da hayaniya na yaudara. Ka san gwamnatin ta iya yaudara. Damarmu ce a matsayinmu na ’yan Najeriya mu nemi abinda mu ke so daga lokacin da mu ka kai shekara 18. Haka ya ke a doka. Saboda haka wannan ‘Not Too Young To Run’ wani ‘show’ ne a ka yi kamar bajekoli ko kalankuwa. Saboda haka ba wani alheri ba ne…
Idan da gaske ne mu fara gani daga kansa ma na ya ce, ‘tunda na sa hannu a wannan doka kuma Ina neman shekara 80 akalla’ don mu a tunaninmu ya ma fi shekara 80 din, to a hakan sai ya ce ‘to na janye, Ina son matashi ya zo ya cigaba’, to ai ka ga ya nuna dattaku a wurin. To, ka ga sai mu duba tsofaffin da su ke takarar su ma mu ce su hakura. To, amma ka zo ka ce ka sa hannu, amma ka na ta fafutukar neman zabe, ka na motsi ko ta ina, ga dukkan alama ka matsa sai ka yi, to ina maganar kuma an sa hannu a cikin wannan sabgar? Ka ga ba maganar an sa hannu a doka. Magana ce ta yaudara, kuma ba mu yarda da ita ba. Idonmu ya bude, ba za mu yarda wani ya kara yaudarar mu ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!