Connect with us

KAUCIN KABA SHA NEMA

Yaya Mace Take Soyayya? (2)

Published

on

A makon da ya gabata, mun fara jero bayanai, game da irin takun da mata suke yi, yayin nuna soyayyarsu ga mutum. Wadanda mafi yawansu sun sha bamban da na maza. Wanda kuma hakan kan haddasa rashin fahimta, lokuta da dama. Darasinmu na wannan mako, wanibangare ne da ya shafin wadancan batutuwa.

Idan Mace Ta Kamu Da So
Sabanin namiji, wanda ko ba ya magana sosai da zarar ya afka tarkon soyayya, to fa nan da nan bakinsa zai bude. A tsammaninsa, shi ne ya fi cancanta ya yi magana, ya ja ra’ayinta ta hanyar dukkan maganganun da ya yi tsammanin za su iya faranta mata. Amma yayin da mace ta fara soyayya, to ko da mai yawan magana ce, sai ka taras bakinta ya rufe. Sannan sabbin alamomin kunya za su iya bayyana a tare da ita. Wannan abu ne mai saukin ganewa a tare da mata. Idan har z aka yi nazarinsu, ko da kuwa a cikin gidanku ne.

Idan Mace Ta Rasa Kulawar Miji
A hannu guda kuma, Yayin da mace ta tashi ta riski ana nuna wa mahaifiyarta kulawa da soyayya sosai a gida, sai kawai ita ma ta tashi da tunanin tabbas ta cancanci so da kulawa na musamman.
Amma duk da wannan, idan zama ya gaza yin dadi tunaninta yana iya sauyawa. Yayin da mace take tunanin ta cancanci a nuna mata dukkan nau’in so da kulawa, tana bude dukkan kofar da mijinta zai samu cikakkiyar damar bayyana mata soyayyarsa. Amma idan ta dauki wasu shekaru ba ta ga wannan mafarki nata ya cika ba, to fa za ta rufe kofofin. Daga nan kuma za ta iya dena yarda da shi. Domin tunaninta zai iya zama kamar haka” Na ba ka dukkan dama, na mallaka maka kaina, amma ka yi watsi da ni. Wannan alama ce ta cewa kai ba za ka taba nuna kulawarka ga mutum ba. Don haka ni ma na gaji, ba wani abu na kyautatawa ta musamman da zan iya ci gaba da nuna maka.”

Karbar Taimako
A duniyar mata, ba ka bukatar sai mutum ya nemi taimakonka, lokacin da ka fuskanci yana cikin damuwa. Kai tsaye za ka iya zuwa ka tanbaye shi damuwarsa, da zummar magance masa ita. Ko kuma in ka san damuwar, kai tsaye ka nufi magance ta. Wannan shi ya sa da zarar mace ta ga mijinta cikin damuwa, za ta zo ta nuna ita ce ta fi kowa cancantar daukar matakin warware masa ita. Abin da mata ba su sani ba shi ne, a duniyar maza ba a garajen ba wa mutum shawara ko taimakonsa, sai dai idan shi ne ya nema da kansa. Yana da kyau mata su fahimci cewa, maza suna karbar agaji ne bayan sun gwada dukkan kokarinsu, ba su sami mafita ba. To a wannan lokaci sai ya iya yin maraba da shawararki. Amma ba shi mafita ko kawo masa dauki a farkon shigarsa damuwa, yana iya dakushe karsahin jarumtarsa. Ko dai ya zama malalaci, ko kuwa rarrauna. Idan kuma kika dage da yawaita ba shi shawara ko kawo mafita a duk halin da ya shiga, to a ransa zai dauka kawai ba ki yarda da shi a matsayin cikakken gwarzo, kamar yadda kowace mace take ganin mijinta ba.

Idan Nuna Kulawa Ya Yi Yawa.
Daga cikin mafi girman so da mace za ta nuna wa mijinta, shi ne ta shiga komai na rayuwarsa, ta zama duk wani motsi da zai yi tana da ruwa a ciki. a wurinta, hakan shi ne abin da yake tabbatar da cewa an zama jini da hanta. Hakan abu ne mai kyau, amma yadda take tafiyar da abin yana gundurar da mijin ba tare da ta sani ba. Domin akwai gabar da ake kaiwa, sai kulawar ta fi kama da ta Uwa da da, maimakon Mata da miji. A irin wannan lokacin yayin da take ta tsammanin tana bayar da kulawar da ta kamata, shi kuma yana ji a ransa cewa ta raina hangen nesa da nutsuwa ko dabararsa. Yi nazarin wannan misalin.
Dr. Gray yana bayar da labarin farkon aurensa da matarsa, ya ce. Idan ya zo zai yi tafiya, sai ta yi ta yi masa tambayoyi game da abubuwan da suka kamata ya tanada a tafiyar, ko abubuwan da zai yi. Misali: karfe nawa za ka tafi? Yaushe za ka tashi daga barci ka fara shiri kenan? Karfe nawa kuma jirginku zai tashi? Saboda kada ka yi latti, su tashi. Ka dai tanadi isassun kudi da za a ka yi amfani da su ko? A tunaninta wannan ita ce kulawa. Amma abin da ba ta sani ba, haushi kawai take ba shi. Ya ce. “Na yi shekaru goma sha hudu ina tafiye-tafiye tsakanin kasashe, ina koyar da darussa, amma ban taba yin latti jirgi ya tashi ba ni ba.” Haka nan kuma idan ya tashi da safe za ta kara jero tambayoyin safe da-ban. Kamar: “fasfo kinka dai yana jikinka ko? Ka dauki wallet (cika-ka-yar) dinka? Kudin wurinka dai za sui she ka ko? Da sauran tambayoyi dangogin wadannan. A tunaninta tana nuna masa so ne, amma shi abin da kawai yake dauka shi ne, ba ta yarda da shi cewa yana da azancin da zai iya shirya wa kansa dukkan abubuwan da suka kamace shi yayin da tafiya irin wannan din ta zo masa ba. Don haka sai ya ji bacin rai kawai maimakon jin an taimake shi.
Har dai a hankali da ya ga abin ya ki ci, ya ki cinyewa, ya sanar da ita. Cewa, ya san abin da take yi tana yi ne don nuna kulawa gare shi. Ya gamsu tana son sa, amma fa gaskiya bay a son wannan kulawar irin ta mahaifiya. Wato kulawa wadda ta fi kama da wadda uwa take yi wa yaronta wanda bai gama mallakar hankalin kansa ba. Domin shi ne zai iya shirin tafiya kuma ya manta wadancan muhimman abubuwan da take tuna masa.
“Idan kulawa kike son nuna mini, to ki nuna min so ki kuma nuna kin yarda da ni kawai. Idan ma na makara, jirgi ya tashi, ya bar ni. Kar ki ce min dama ai na fada maka. Idan na manta buroshina da dangoginsu a gida. Ko na kira kar ma ki yi min maganar su, ni zan san yadda zan yi,a inda nake.”
Watarana kuwa yay i tafiya kasar Sweden, sai kawai ya manta fasfo dinsa. Amma da yay i mata waya ya fada mata, sai kawai ta ce, “Kai John, wace irin kasassaba ka yi haka? To kuma yanzu ya ya za ka yi kenan?” Sai ya sa ta ta tura masa da sakon katin ta hanyar na’urar sadarwar fas (fad) zuwa can ofishin jakadancinsu. Daga nan aka warware matsalar. Dga wannan lokaci sai ta dena yi masa wadancan dogayen kashedin. Tunda abin da ya fada, ya tabbata. Cewa, in ma ya manta wani abu, kar ta damu, shi zai san yadda zai yi ya samar wa kansa mafita.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!