Connect with us

SIYASA

2019: Gwamna Wike Ya Bukaci Kungiyoyin Fararen Hula Su Sanya Ido A Kan INEC

Published

on

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike ya yi kira ga kungiyoyin fararen hula da kungiyoyi masu zaman kansu da su tabbatar da sanya wa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ido domin tabbatar da ta gudanar da zaben bisa gaskiya da adalci kuma sahihin zaben da babu magudi a cikinsa kamar yadda dokar zabe ta adana.
Kana ya kuma bukacesu da su tabbatar da sanya wa jami’an tsaro ido a lokacin gudanar da zaben na dubu biyu da sha tara a Nijeriya, Wike, wanda ke bayanin a karshen mako, a lokacin da yake ganawa da kungiyoyin fararen hula da kungiyoyi masu zaman kansu a garin Port Harcourt, ya shaida cewar suna da gagarumar rawar takawa wajen tabbatar da sahihancin zabe.
Ya ce: “ku sanya wa INEC da jami’an tsaro ido domin ku tabbatar aiyukan da suke gudanarwa yana kan layin da aka tsara musu a dokance kamar yadda dokar zabe ya tanadar,” Inji Shi Nyesom.
Gwamnan ya shaida cewar kawo yanzu ya razana da yunkurin INEC wanda a cewarsa kungiyoyin su tashi tsaye domin bibiyarsu.
Wike, ya nemi Majalisar kasa da ta sake duniya da nazarin dokar kungiyoyin fararen hula domin kara musu karfin iko wanda a cewarsa yin hakan zai kawo hanyoyin da za a samu rage magudin zabe.
Ya nemi kungiyoyin fararen hula da su yi aiki tare da sauran ‘yan Nijeriya domin tabbatar da Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa a zaben 2019, ya misalta sake zaman Buhari shugaban kasa a matsayin annoba ga kasa.
Ya ce: “muna godiya wa Allah da ya sanya dan takarar shugaban kasa na PDP ya shirya amsar mulki da kuma daidaita lamura. Wannan kasar ta mu ba za ta kai labari ba muddin Buhari ya kara yin wasu shekaru hudu kuma a matsayin Shugaba kasar,” A cewar gwamnan na Ribas
Nyesom Yana mai shaida cewar ababuwa sun lalace a karkashin Buhari don haka ‘yan Nijeriya suna nema wa kansu mafita. Wike ya kuma kara da cewa, a wannan lokacin dukkanin ‘yan Nijeriya suna da cikakken ikon fito bainar jama’a su bayyana cewar lamura ba su tafiya daidai wanda ya nemi a zabi sauyi domin cire shugabanin da suka gaza.
Wike ya kuma shaida cewar jihar Ribas babu wani dalilin da zai sanya su zabi Buhari a 2019 domin a cewarsa babu wani aiki kwara daya da za a nuna da Buhari ya aiwatar a jihar.
A jawabinsa shugaban kungiyar fararen hula na jihar Ribas Sotonye George ya yi kiran da a gudanar da sabe bisa gaskiya da adalci kuma sahihancin
George ya kalubanci hukumar zabe INEC da ta kaurace wa daukan bangaranci a yayin gudanar da zabe ko tsare-tsaren zabe wanda hakan zai bai wa jama’a damar zabin wadanda suke so, ya kuma jawo hankalin jami’an tsaro da cewar su tabbatar da sun gudanar da aiyukansu bisa kwarewa da sanin ya kamata hadi da bin dokokin aiki domin tabbatar da sahihancin zabe.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: